Wani Sanata ya fice daga APC
Shugaban APC ya ce sauyin sheka ba sabon abu ba ne musamman a irin wannan lokaci na kakar zabe.
Sanata mai wakiltar shiyyar Nasarawa ta Arewa a Majalisar Dattawa, Godiya Akwashiki, ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki a kasar.
Akwashiki ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar ne a yayin kaddamar da aikin titin Nasarawa Eggon zuwa Galle, a Karamar Hukumar Nassarawa Eggon ta jihar a ranar Litinin.
Ya bayyana cushe da kuma kagen da aka yi a sunayen daligets yayin zaben fidda gwanayen takara shi ne dalilinsa na barin jam’iyyar.
“Dukkanku kun san abin da ya faru a lokacin zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a Akwanga.
Na janye daga takarar ne saboda kagen da aka yi cikin jerin sunayen daligets da jam’iyyar ta yi.
Na fuskanci matsin lamba daga gareku ta ficewa daga jam’iyyar kuma a yanzu na amsa kiran ku na ficewa daga jam’iyyar APC don ganin tabbatar burina na sake tsayawa takara.
Nan da awa 72 zan sanar da jam’iyyar da zan koma, kuma duk tare da ku za mu sauya sheka zuwa jam’iyyar.
Sauyin shekar tasa na zuwa ne kwanaki bayan da tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama kuma jigo a jam’iyyar APC, Femi Fani-Kayode, ya yi gargadin cewa karin wasu Sanatoci 22 na APC za su sauya sheka zuwa jam’iyyar awada ta PDP.
Ya bayyana cewa guguwar sauyin shekar za ta kada ne saboda an hana Sanatocin tikitin tsayawa takara a jam’iyyar a Zaben 2023.
“Sanatocin APC 22 suna barazanar sauya sheka zuwa PDP saboda an hana su tikitin komawa Majalisar Dattawa.
“Wannan babban abun damuwa ne kuma dole ne a yi wani abu don ganin hakan bai tabbata ba, domin kuwa rasa wadannan sanatoci babban gibi ne a wurinmu,” in ji Fani Kayode.
A bayan nan ne Aminiya ta ruwaito yadda Sanatoci bakwai suka fice daga APC zuwa wasu jam’iyyun adawa.
Sanatocin da suka fice daga APC sun hada da Ibrahim Shekarau, Yahaya Abdullahi, Adamu Aliero, Dauda Jika, Ahmad Babba Kaita, Lawal Yahaya Gumau da Francis Alimikhena.
Da yake zantawa da manema labarai bayan ganawar sirri da Sanatocin APC, Shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce abin takaici ne yadda ‘yan majalisar suka fice daga jam’iyyar.
Sai dai Sanata Adamu ya ce kadawar guguwar sauyin sheka ba sabon abu ba ne musamman a irin wannan lokaci na kakar zabe.