Wani sashe na mahalarta taron tunawa da zuwan boko kasar Hausa
Sannan Muslim ya ruwaito daga Abu Huraira (RA) daga Annabi (SAW) cewa “Lallai wani mutum ya ziyarci wani dan uwansa a wata alkarya, sai Allah Ya aika masa da wani Mala’ika a kan hanyarsa. Lokacin da ya zo, sai Mala’ikan ya ce: “Ina ka nufa?” Sai ya ce, “na nufin wurin wani dan uwana ne […]
Sannan Muslim ya ruwaito daga Abu Huraira (RA) daga Annabi (SAW) cewa “Lallai wani mutum ya ziyarci wani dan uwansa a wata alkarya, sai Allah Ya aika masa da wani Mala’ika a kan hanyarsa. Lokacin da ya zo, sai Mala’ikan ya ce: “Ina ka nufa?” Sai ya ce, “na nufin wurin wani dan uwana ne a wancan alkarya.” Sai ya ce, “Ko akwai wata ’yar ni’ima da za ka samu?” Ya ce, “A’a, iyaka dai ina sonsa ne saboda Allah Madaukaki.” Sai ya ce, to ni dan aiken Allah ne zuwa gare ka, cewa Lallai Allah Yana sonka, kamar yadda kake sonsa saboda Shi.”
Haka ake saka wa masu gaskiya da ikhlasi, wadanda suke auna soyayarsu da kiyayyarsu ga mutane a mizanin ikhlasi ga Allah! Idan suka jibinci mutum, to don Allah ne, idan suka yi adawa, nan ma don Allah ne. Wannan ma’auni na so da kin abu don Allah, shi ne mafi amincin igiyar imani. Idan Musulmi ya tozarta shi, sai imaninsa ya sami nakasu. Manzon Allah (SAW) ya ce, “Mafi aminicin igiyar imani, ita ce, jibinta don Allah da yin gaba don Allah, da so don Allah da kiyayya don Allah Mai girman daraja.” dabarani ne ya ruwaito shi daga Ibn Abbas.
Na biyar: Daga cikin wadanda Allah zai yi musu inuwa da laimarSa, akwai mutumin da ya tuna ko ya ambaci Allah shi kadai a kebe, amma idanuwansa suka zubar da hawaye. Wannan mutun yana tunowa ne da haiba da girman Allah, yana gabato da tsoron Allah a zuciyarsa, yana tsoron Allah a boye da bayyane. Wannan mutum yana daga cikin wadanda Allah Ya ce kansu: “Abin sani kawai, muminai su ne wadanda suke idan aka ambaci Allah, sai zukatansu su firgita, kuma idan aka karanta ayoyinSa a kansu, su kara imani, kuma ga Ubangijinsu suke dogara.” (k:8:2).
Wannan shi ne wanda ya tuna da Allah a boye idanuwansa suka zubar da hawaye, kuma wannan hawaye mai tsarki da ya zuba, ya zuba ne don Allah kawai ba don waninSa ba. Domin wannan mutum ya kasance a kebe shi kadai, babu wani a tare da shi, sai wannan hawaye ya zamo bisa ikhlasi da tsarkakuwa, saboda babu batun riya, ko jiyarwa game da shi. To haka salihan bayi masu komawa ga Allah suke. Manzon (SAW) yana cewa kamar yadda ya zo a cikin Sahihul Jami daga Hadisin Anas (RA), “Idanuwa biyu wuta ba ta shafarsu har abada: idon da ya yi kuka ya zubar da hawaye saboda tsoron Allah, da idon da ya kwana yana tsaro a fagen yaki saboda daukaka addinin Allah.”
Ya bayin Allah! Yaushe zukatanmu za su gyaru? Yaushe ne zukatanmu za su yi taushi su ji tsoron Allah? Yaushe za mu koma zuwa ga Allah da ikhlasi, mu tsaya gaba gare Shi muna masu jin tsoronSa, masu kankan da kai, masu nadama bisa abubuwan da muka yi, muna masu neman afuwarSa da rahamarSa? Hawaye ne da mabubbugarsa tsoron Allah, hawaye ne wanda ya fito saboda tsoron Allah da gaskata Shi da tsarkake aiki dominSa da neman tsira daga azabar Allah da shamakancewarSa daga wutarSa.
Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ba za a jefa mutumin da ya yi kuka saboda tsoron Allah a wuta ba, har sai idan nonon da aka tsotso zai koma cikin mama. Kuma ba za a hada wa bawa kurar jihadi a tafarkin Allah Madaukaki da hayakin Jahannama ba.” Ahmad ya ruwaito shi daga Abu Huraira.
Don haka ku bi Allah da takawa ya ku bayin Allah! Ku kiyaye Shi a fili da boye, ku tuba ku koma zuwa gare Shi, lallai Shi Mai yawan karbar tuba ne, Mai jin kai. Ina fadin wannan magana tawa, ina neman gafarar Allah, lallai ne Shi Mai yawan gafara ne Mai jin kai.
Huduba ta Biyu
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu. Babu gaba face a kan mutane azzalumai. Tsira da amincin Allah su kara tabbata a kan ManzonSa amintacce.
Ya ’yan uwa a cikin imani! Amma na shida daga cikin mutanen da Allah zai yi musu inuwa aranar da babu inuwa, sai inuwarSa, shi ne mutumin da wata mace mai daraja ma’abuciyar girma da mukami da kyau ta kira shi su yi lalata, amma ya ce, “Ina jin tsoron Allah Ubangijin halittu!” Wannan azama ce mai karfi da aminci a cikin yi wa Allah alkawari, wadda ba ta girgiza a lokacin da ake gaban babbar fitina. Wannan mutum ya san lallai Allah Yana tare da shi, sai ya ji tsoron kada ya yi fito na fito da Shi ta wajen saba maSa. Ya san lallai Lahira ita ce mafi alheri daga duniya, sai ya zabi Hurul Aini a kan matan duniya.
Wannan mutum wasu dabi’u da Allah Ya ambata a cikin LittafinSa kan kissar AnnabinSa Yusuf, duk sun tattaru gare shi. Yusuf mai tsira da aminicin Allah, ya ce a lokacin da Matar Aziz ta kira shi zuwa ga alfasha: “Ina neman tsarin Allah! Lallai Shi ne Ubangijina. Ya kyautata mazaunina. Lallai ne shi, masu zalunci ba su cin nasara.” (k:12:23).
Wannan mata fa ita ce matar Aziz din Masar (Firaminista), ba ta cikin matan talakawa, sannan tana da tsananin kyau, tana da karfi da iko, amma karfin imani da Allah a cikin zukatan salihai ya fi karfinta. AzabarSa ta fi muni, don haka mafi gudun mutane daga sabonSa ya himmantu daga gudu daga gare ta, mafi hakurin mutane a kan fitina komai tsananinta, ya hakura. To haka, wannan mutum da mace mai daraja da matsayi da kyau ta kira shi yake. Al’amarin ta fuskoki biyu yana sanya kwadayi, ita dai ba talaka ba ce, ko wadda ta fito daga matan ya ku bayi! A’a tana daga cikin madaukaka a al’umma da kowane mutum ke son ya je kusa da su. Ita kuma ba mummuna ba ce, balle a ce mutane suna kawar da kai daga gare ta. A’a kyakkyawa ce, sannan kuma ita ce ta nemi a gagauta aikata alfashan da ita. Amma duk da haka wannan mutum ya shaida mata ta harshen muminai wanda ba ya kimanta zunubi da ma’aunin mutum ma’aunin sha’awa ta kusa, a’a yana auna shi ne da mizanin Allah Madaukaki. Ya san sha’awa tana gushewa ta bar bakin cikinta matukar duniya tana nan, sannan azabarSa ta babbake shi ranar kiyama. Don haka ya fadi maganarsa da ta zame katanga tsakaninsa da wannan mace, ta gaza cimma burinta ta kuma yanke kauna daga gare shi. Saurari abin da ya ce: “Ni ina tsoron Allah Ubangijin halittu!”
Na bakwai shi ne: Mutumin da ya yi sadaka amma a boye, hatta hannun hagunsa bai san abin da dama ya bayar ba.
Ya bayin Allah! Sadaka babban abu ne mai muhimmanci, Allah Yana sakawa a kanta da mafificin alheri. Domin ita tana ta’allake da bayin Allah Mai tsarki ne. Tana kwance tsananin wanda ke cikin tsanani, ta ciyar da mayunwaci ta tufatar da huntu. Duk Musulmin da hannunsa ya saba da bayar da sadaka, to yana cikin alheri kuma yana kan alheri. Domin yana godiya ne ga Allah bisa ni’imarSa ta wajen ciyarwa. Wannan ni’ima ce da Allah Ya yi masa, kuma ya yi i’itirafi da cewa hakan daga fafalar Allah ce. Don haka ya dauki wani abu daga cikinta ya ba fakiri da mabukaci da wanda ke cikin tsanani. Saboda haka yana kan alheri a kullum. Sabanin haka kuma, duk Musulmin da hannunsa ya saba da rowa da kwauro, to yana kan halaka babba.
Domin dukiya ta Allah ce, Shi Yake bayar da ita kuma Yana iya kwace ta. Duniya da abin da yake cikinta na Allah ne, kuma zai gaje ta wata rana, Shi ne Mafi alherin masu gado. Don haka don me za mu yi rowa a cikinta? Don me za mu manne mata har ba za mu iya ciyar da fakiri da mai bukata daga abin da ke cikinta ba?
Lallai Mala’ikun Mai rahama, suna addu’a ga ma’abucin sadaka a kullum, kuma suna addu’a a kan mai kin yin sadaka. Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Babu wata rana da bawa zai tashi da Asuba face, akwai Mala’iku biyu da suke sauka, dayansu yana cewa: “Ya Ubangiji! Wanda ya ciyar ka mayar masa.” dayan kuma yana cewa: “Ya Ubangiji! Wanda ya yi rowa ka watsa dukiyarsa.” An yi ittifaki a kansa daga Hadisin Abu Huraira.
Wadannan su ne ayyuka bakwai na wadanda Allah zai sanya su a inuwa a yinin da babu wata inuwa sai inuwarSa. Wadannan su ne mutanen da za su samu aminci a wancan rana, a lokacin da sauran mutane suke cikin tsoro!
Hakika a duniya sun yi aiki na imani, sun tsare dokokin Allah a cikinta, su mabubbugar ayyukansu ikhlasi ne da son abin da yake wurin Allah, da fifita rayuwa ta gaba daga ta kusa.
Don haka sai mu roki Allah Ma’abucin Tsarki Ya karfafa imani a zukatanmu, kuma Ya taimake mu a kan tunawa da Shi da gode maSa da kyautata bauta gare Shi.