Wani shugaban Shi’a ya kai ziyara Saudiyya

Wani shugaban Shi’a daga kasar Iraki Muktada al-Sadr ya kai ziyara kasar Saudiyya inda ya gana da yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman da wasu jami’an gwamnatin kasar. Tun a ranar lahadin da ta gabata ne ofishin al-Sadr ya fitar da wani sanarwa inda ya nuna cewa an gayyaci al-Sadr zuwa kasar ta Saudiya.  […]

Wani shugaban Shi’a ya kai ziyara Saudiyya

Wani shugaban Shi’a daga kasar Iraki Muktada al-Sadr ya kai ziyara kasar Saudiyya inda ya gana da yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman da wasu jami’an gwamnatin kasar.

Tun a ranar lahadin da ta gabata ne ofishin al-Sadr ya fitar da wani sanarwa inda ya nuna cewa an gayyaci al-Sadr zuwa kasar ta Saudiya. 

“Mun ji dadin kwarai na abin da muka gani a lokacin ziyarar na yadda ake samun ci gaba a bangaren alaka tsakanin Saudiya da Iraki. Muna fata wannan ya zama farkon wata nasara tsakanin kasashen Larabawa,” kamar yadda sanarwa daga ofishin al-Sadr ta nuna.

A watan jiya ne Saudiya da Iraki suka amince su shirya wata majalisa da za ta fadada tsare-tsare hadin kai a cikin shirin magance matsalolin rashin hadin kai day a dabaibaye yankin Larabawa.

kasar Saudiya ta bude ofishin jakadancinta na Baghdad a shekarar 2015, bayan ya shafe tsawon shekara 25 yana kulle

Hakanan kuma, a watan Fabrairun bana, Adel alJubeir ya zai ziyara birnin Baghdad, wanda ya zamo na farko da Ministan harkokin kasashen wajen Saudiya zai kai ziyara birnin tun a shekarar 1990.

Tsawa ta kashe mutane 21 a India

Mutane 21 ne suka mutu bayan tsawa ta fada a kan su a Gabashin Indiya.

Ana kwarara ruwan sama kamar da bakin kwarya a kasar ‘yan kwanakin, wanda ya yi sanadiyar ambaliyar da ta kashe mutane da dama kuma mutane miliyoyi suka rasa muhallansu, kamar yadda jami’an suka sanar.

A Jihar Osisha, mutane 18 ne suka mutu, sannan kuma mutane uku suke mutu a Jihar Jharkhand kamar yadda jami’ai a jihohin suka sanar. Sannan kuma a Jihar Jharkhand, ‘yan uwa biyu sun mutu bayan tsawar ta fada musu har cikin gidansu a Gundumar Kharswan, sannan kuma an kara samun wasu gawar mutane uku a cikin ruwa a Gundumar Jajpur.

Hukumar kula da yanayi ta kasar ta yi gargadi a kan cewa za a iya fuskanta wata tsawar nan gaba.

An shiga wani yanayi na damina gadan-gadan, inda ake da rahotannin da ke cewa hakan ya jawo matsaloli da dama a wasu jihohin daban-daban, wanda ya kai ga lalacewar tituna da layukan wutar lantarki.

Daminar ta yi sanadiyyar ambaliyar ruwan da aka shafe shekaru ba a ga irin sa ba.