Wani tsiro ya jawo wa wata jaririya yoyon fitsari da bahaya
Wata yarinya mai kimanin wata 20 mai suna Habiba Abdullahi da aka haifa da wani tsiro a karkashin cibiyarta ta samu kanta cikin matasala bayan da tsiron ya jawo mata yoyon fitsari da bayan gida. Mahaifin jaririyar Malam Abdullahi Muhammed da ke Unguwar Bulunkutu a birnin Maiduguri Jihar Borno, ya shaida wa wakilinmu cewa “An […]
Wata yarinya mai kimanin wata 20 mai suna Habiba Abdullahi da aka haifa da wani tsiro a karkashin cibiyarta ta samu kanta cikin matasala bayan da tsiron ya jawo mata yoyon fitsari da bayan gida. Mahaifin jaririyar Malam Abdullahi Muhammed da ke Unguwar Bulunkutu a birnin Maiduguri Jihar Borno, ya shaida wa wakilinmu cewa “An haifi Habiba ne da wani tsiro a kasar cibiyarta wanda tsiron ya hade al’aurarta kuma ya haifar mata da yoyon fitsari da bayan gida. A lokacin da aka haife ta mun ga tsiron a kasar cibiyarta a hankali yana girma, shi ne muka je asibitin Fatuma Ali Sheriff, amma sai suka ce abin ya fi karfinsu, muka wuce babban asibiti, su ma suka ce mu tafi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri.” Ya ce har yanzu ana yi musu jeka-ka-dawo a asibitin babu magani babu takamammiyar magana, kuma har yanzu jami’an asibitin ba su fada masa nawa zai kashe kan aikin da suka ce za a yi mata ba. “Mun yi gwaje-gwaje da dama amma har yanzu ba mu san halin da muke ciki ba, wannan tsiro yana hana mu barci ba mu da kwanciyar hankali,” inji shi. Malam Abdullahi ya ce, lokacin da iyalinsa ta dauki cikinta ta yi ta zuwa awon cikin a asibiti kamar sauran haihuwanrsu biyu, kuma babu wata matsala da aka gano. Ya ce wasu likitoci sun tabbatar masa cewa za a kashe sama da Naira dubu 300 wajen yi mata aiki, inda ya bukaci uwar gidan Gwamnan Jihar Borno ko gwamnatin jihar da sauran kungiyoyin jin kai su taimaka wajen daukar nauyin jinyar.