Wani ya auri ’yarsa ’yar shekara 13 a Zimbabwe
Wani mutumin Bulawayo da ke kasar Zimbabwe, ya shiga hannun hukuma, bayan da ya auri ’yarsa ’yar shekara 13, al’amarin da ya ce umarni ne daga matarsa da ta mutu. Wannan yarinya dai tana karatun Firamare a aji na shida, kamar yadda shafin sadarwar na bulawayo24 ya ruwaito.Kafafen uyada labarai sun ruwaito cewa mutumin, wanda […]
Wani mutumin Bulawayo da ke kasar Zimbabwe, ya shiga hannun hukuma, bayan da ya auri ’yarsa ’yar shekara 13, al’amarin da ya ce umarni ne daga matarsa da ta mutu. Wannan yarinya dai tana karatun Firamare a aji na shida, kamar yadda shafin sadarwar na bulawayo24 ya ruwaito.
Kafafen uyada labarai sun ruwaito cewa mutumin, wanda ba a bayyana sunansa ba, ya dade yana zaune da ’yarsa, tun a shkarar 2009, bayan mutuwar matarsa. Majiyar ta bayyana cewa, a watan da ya wuce, mutumin ya ce ya yi mafarki da matarsa da ta mutu, inda ta umarce shi da ya auri ’yarsa. Sai mutumin ya sanar da ’yan uwansa game da wannan ‘umarni.’
A farkon wannan watan kawai, sai ya yanke hukuncin bin umarnin ‘auren’ ’yarsa, a wani biki da abokansa na kut da kut suka halarta. Wannan biki dai aboye aka gudanar da shi. Sunsawo kayan abinci da abubuwan sha, inda suka yi dan kwarya-kwaryan biki. Shi ke nan, sai wannan karamar yarinya ta auri babanta, a cewar majiyar.
Wannan aure dai ya watse ne a daidai lokacin da wannan miji/uba ya yi kokarin tarawa da matarsa, sai kawai ta gudu, ta kai kara wurin wani dan uwansu, wanda ya kai kara wurin ’yan sanda.