Wani ya daba wa dan uwansa wuka a Kano
Wani dan shekara 30 mai suna Tasi’u Iliyasu, da ke zaune a rukunin gidaje na Sauna, a Karamar Hukumar Nasarawa da ke Jihar Kano ya gamu da ajalinsa bayan da aka zargi dan uwansa Abba Sule da daba masa wuka. Kawo yanzu ba a san dalilin da ya sanya ya kashe shi ba. An ce […]
Wani dan shekara 30 mai suna Tasi’u Iliyasu, da ke zaune a rukunin gidaje na Sauna, a Karamar Hukumar Nasarawa da ke Jihar Kano ya gamu da ajalinsa bayan da aka zargi dan uwansa Abba Sule da daba masa wuka. Kawo yanzu ba a san dalilin da ya sanya ya kashe shi ba. An ce mamacin ya rasu ne sakamakon raunin da ya samu.
Da yake tabbatar da lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa cewa ya yi lamarin ya faru ne, bayan wanda ake zargin ya hada baki da wani mutum mai suna Magaji (wanda ba a bayyana sunansa na biyu ba) suka aikata wannan ta’asa daga nan kuma suka tsere. Rundunar ’Yan sanda ta ce lamarin ya auku ne ranar Lahadin da ta wuce da misalin karfe 8:30 na dare.
Kiyawa ya ce “Ana zargin Abba Sule da wani Magaji wanda ba a san sunansa na biyu ba wadanda ’yan unguwa daya ne dauke da makami Abba ya daba wa dan uwansa mai kimanin shekarA 30 wuka inda ya yi sanadiyyar mutuwarsa a nan take, kuma dukkansu sun tsere.”
Ya ci gaba da cewa ’yan sanda a karkashin jagorancin DPO na Dakata sun ziyarci inda wannan lamari ya auku, suka duba mamacin tare da daukar hoton gawarsa kafin daga bisani su wuce da shi Asibitin Kwararru na Sa Sanusi inda Likitoci suka tabbatar da ya cika.
Kakakin ya ci gaba da cewa ’yan sanda sun baza komarsu don kamo wadanda ake zargi da aikata wannan ta’asa. Ya kara da cewa tuni an mika wannan lamari ga sashen binciken manyan laifuffuka (CID) don ci gaba da bincike.