Wani ya harbe baban budurwarsa saboda kin amincewarsa da aurensu
Wani matashin Ba-Indiye, dan shekara 22 ya harbi baban budurwarsa, saboda ya ki amincewa da bukatarsa ta neman aurenta, kamar yadda jami’an ’yan sanda suka bayyana a birnin New DelhiMatashin ya kai wa Yoges Jain, dan shekara 55 hari, ya kuma tunkari mahaifiyar yarinyar Poonam, ’yar shekara 50, inda ya tunkareta da sanda. Iyalan na […]
Wani matashin Ba-Indiye, dan shekara 22 ya harbi baban budurwarsa, saboda ya ki amincewa da bukatarsa ta neman aurenta, kamar yadda jami’an ’yan sanda suka bayyana a birnin New Delhi
Matashin ya kai wa Yoges Jain, dan shekara 55 hari, ya kuma tunkari mahaifiyar yarinyar Poonam, ’yar shekara 50, inda ya tunkareta da sanda. Iyalan na zaune a gidansu da ke Jyoti Nagar a gabashin Delhi a lokacin da aka kai musu harin, kamar yadda ’yan sanda suka bayyana.
Wannan matashi dai ya gudu, har yanzu ’yan sanda ba su kama shi ba. Ya harbi Yogesh Jain a ciki, inda ya ji masa rauni.
’Yan sanda sun ce matashi ya yi fada da yarinyar bayan an ki amincewa da bukatarsa ta neman aurenta. Ita dai wannan budurwa ta samu ta tsere, don haka sai saurayin ya huce haushinsa a kan iyayenta.
Saurayin da ya kai wa iyayen wannan yarinya hari, mazaunin wani gari ne da ake kira Shahdara, ya shafe watanni yana neman shawo kanta, har suka saba da juna a lokacin tana karatu. Tuni dai yarinyar ta shiga jami’ar Delhi.