Wani ya harbe jaririyarsa saboda ba ya son fara haihuwar mace

Ba ya son ya fara haihuwar ‘ya mace sai dai namiji.

Wani ya harbe jaririyarsa saboda ba ya son fara haihuwar mace

Jaririya

’Yan sanda a Pakistan sun bazama wajen neman wani mutum ruwa a jallo da ake zargi ya kashe ‘yarsa ‘yar kimanin kwanaki bakwai da haihuwa.

Ana zargin mutumin da harbe jaririyar ne saboda ba ya son ya fara haihuwar ‘ya mace sai dai namiji.

BBC ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne a birnin Mianwali da ke tsakiyar Pakistan.

Bincike ya nuna cewa jaririyar ta mutu ne nan-take bayan harbinta sau biyar da bindiga.

Kisan ya fusata jama’a tun bayan da aka sanya hoton gawar jaririyar a shafukan sada zumunta.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam a kasar sun ce kisan yarinyar da suka sanyawa suna Jannat na daga cikin kisan da aka yi wa kanana yara abin da kuma ba za su amince da shi ba har sai an bi mata hakkinta.

Zaɓen Edo: Yadda aka kama masu sayen ƙuri’a da ’yan daba

Sarakunan Nijar sun kai wa Gwamnatin Yobe ziyarar jaje

Ɗan majalisa ya yi jinjina kan naɗa Danyaya Sarkin Ningi

’Yan Sanda sun kama gungun ’yan fashi 7 a Katsina