… Wani ya kashe abokinsa a kan Naira 800

Kotun da ke unguwar Ebute-Metta a Legas ta ba da umarnin tsare wani matashi mai suna Lateef Jimoh, mai shekaru 32, kan zargin daba wa abokinsa mai suna Nurudeen Adio kwalba kan cacar baki da ta shiga tsakaninsu saboda Naira 800.Aminiya ta gano cewa lamarin ya auku ne a unguwar Amukoko, inda Jimoh da abokinsa […]

… Wani ya kashe abokinsa a kan Naira 800
… Wani ya kashe abokinsa a kan Naira 800

Kotun da ke unguwar Ebute-Metta a Legas ta ba da umarnin tsare wani matashi mai suna Lateef Jimoh, mai shekaru 32, kan zargin daba wa abokinsa mai suna Nurudeen Adio kwalba kan cacar baki da ta shiga tsakaninsu saboda Naira 800.
Aminiya ta gano cewa lamarin ya auku ne a unguwar Amukoko, inda Jimoh da abokinsa Adio suke karbar kudin tasha daga masu  hayar babura. A ranar 9 ga watan Maris, bayan da suka dawo daga wurin sana’arsu, suna cikin lissafin kudin da suka samo, sai musu ya kaure a tsakaninsu kan Naira 800, sai fada, inda nan take Jimoh ya fasa kwalba ya daba wa Nuru a kirji, ya fadi cikin jini kafin a kai shi asibiti ya mutu.
A lokacin da aka gurfanar da Jimoh a gaban kotu mai gabatar da kara sufeton dansanda Clement Okuomoise ya shaida wa kotu cewa ‘A ranar 9 ga watan Maris na shekarar 2014 da misalin karfe 6 da rabi na yamma, a unguwar Amukoko da ke jihar Legas Lateef Jimoh, ya kashe wani da ake kira Nurudeen Adio mai shekaru 32 a duniya ta hanyar daba masa fasashshiyar kwalba a kirji yin hakan ya saba wa sashen doka na 221 na kundin dokokin jihar Legas ta tarayyar Najeriya na shekarar 2011’.
Duk da  rokon afuwa da wanda ake zargi ya yi kotun ta ki saurarsa, saboda haka sai dansanda mai gabatar da kara ya nemi kotun ta tura Jimoh gidan maza har zuwa lokacin da sashen da ke bayar da shawara kan manyan laifuka na jihar ya yanke shawara kan lamarin.
Sai dai lauyan da yake kare Jimoh mai suna Spurgeon Ateane ya soki bukatar dansanda mai gabatar da kara na kai wanda yake karewa kurkuku inda ya kafa hujja da sashe na 264 karamin sashe na (9) na dokokin jihar Legas.
Mai shari’a O.O. Olatunji, bayan ya saurari shaidar da dan sanda mai binciken manyan laifuka, Saja John Babalola ya bayar kan lamarin, sai ya ba da umarnin a tsare wanda ake zargi a gidan yarin da ke unguwar Ikoyi har zuwa ranar 7 ga watan Mayu sannan za a ci gaba da sauraron shari’ar.