Wani ya mutu a gasar shan kwayar da Kwastam ta kone

A ranar Larabar da ta gabata ne Hukumar Kwastam ta kone miyagun kwayoyin da ta kame wanda ta kiyasta kudin su akan sama da Naira biliyan 14, miyagun kwayoyin da suka hadar da tiramadol da dangoginta dauke cikin motocin kwantaina 58 wanda aka yi aikin kone su cikin kwanaki biyu a dandanli kone kayayyaki irin […]

Wani ya mutu a gasar shan kwayar da Kwastam ta kone

A ranar Larabar da ta gabata ne Hukumar Kwastam ta kone miyagun kwayoyin da ta kame wanda ta kiyasta kudin su akan sama da Naira biliyan 14, miyagun kwayoyin da suka hadar da tiramadol da dangoginta dauke cikin motocin kwantaina 58 wanda aka yi aikin kone su cikin kwanaki biyu a dandanli kone kayayyaki irin wannan da ke kan hanyar Ikorodu daga garin Shagamu.

Binciken da jaridar Aminiya tayi ya nuna cewa, an sami wasu matasa ‘yan garin Sabo Shagamu wadanda suka bi dare suka yi lalibe a burbushin miyagun kwayoyin da Kwastam ta kone inda suka kai ga samun wadanda basu kai ga konewa ba suka yi ta jidar su tamkar sun sami ganima har ta kai ga sun tafi da su unguwar Shagamu suka aza gasar kwankwadar shan kwayar tiramadol da suka kalato.

Wata majiyar mu ta shaida mana cewa wasu matasa 3 da suka yi gasar shan kwayar tiramadol da kwastam ta kame sun yi ta yin amman ta yayin da daya daga cikin su da bai yi aman ba ya mutu nan take.

Majiyar ta ce, a daren Juma’ar da ta gaba ta ne matasan suka sanya gasar shan kwayar ta Kwastam inda suka  sanya kwayar tiramadol guda 15 ko wannen su a cikin lemon kwalba inda suka yi ta kwankwada domin nuna bajinta lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar daya daga cikin su wanda aka yi wa sallar  jana’iza  a masallacin Kungiyar Izala da ke garin Sabo Shagamu.

Wata majiyar ta shaidawa Aminiya cewa, wasu dilallan miyagun Kwayoyin sun yi ta sayen kwayar tiramadol da wasu matasa suka yi kalenta a inda Hukumar Kwastam bayan ta qone miyagun kwayoyin a Shagamu.