Wannan magana abar dubawa ce
Tun da dadewa ‘yan jarida da jami’an tsaro, musamman ma ‘yan siyasa ke ta kaffa-kaffa da takatsantsan game da batun haramtacciyar kungiyar Boko Haram, suna kuma dari-dari wajen bayyana wasu al’amura game da su don gudun kada a tozarta ko a wulkanta su. Dalili kuwa shi ne babu wanda ke so a ce yana da […]
Tun da dadewa ‘yan jarida da jami’an tsaro, musamman ma ‘yan siyasa ke ta kaffa-kaffa da takatsantsan game da batun haramtacciyar kungiyar Boko Haram, suna kuma dari-dari wajen bayyana wasu al’amura game da su don gudun kada a tozarta ko a wulkanta su. Dalili kuwa shi ne babu wanda ke so a ce yana da wata masaniya ko hulda da ‘yan kungiyar, domin halin da ake ciki na saurin nuna yatsan zargi ko yin kazafin da babu gaira, babu dalili ga abokan adawar da aka sanya a gaba.
A wajen ‘yan kudancin kasar nan shugabannin Arewa ne ke da hannu wajen samar da wannan kungiyar, su ne kuma ke daure mata gindi, suna taimakawa da kudade da kayayyakin aikin gudanar da ita. Dangane da haka sun sha cewa manyan ‘yan Arewa sun ki fitowa fili, firi-falo don tsawata kungiyar, ko kuma su wanke kawunansu daga zargin da ake yi masu. Duk da cewa manyan shugabannin al’ummomin Arewa, ciki har da fitattun ‘yan siyasa da janarorin soji da fitattun malaman addinin Islama, da manyan sarakunan yankin sun bugi kirji, sun tozarta akidar kungiyar wacce ta saba koyarwar addinin Musulunci, suka kuma nesanta kawunansu daga gare su, amma ‘yan kudu ba su gamsu ba, su a ganinsu duk wani dan Arewa dan ta’adda ne da ake kyama kamar annoba a wasu sassan kudancin kasar nan.
Wasu ‘yan siyasar ma da suka zafafa wannan al’amarin sun ce da gangan ne ‘yan Arewa da shugabanninsu suka kirkiro kungiyar ta’addancin da suka yi wa lakabi da Boko Haram domin kawai su takawa Shugaba Jonathan birki, su hana shi mulkin kasar nan hankali kwance. Akwai kazafin da ya fi haka zafi ga jama’ar Arewar da su ne suka fi tagayyara sakamakon wannan ta’adin, su ne kuma suka fi yin asarar rayukansu da dukiyoyinsu? Ai a yankin Arewa ne kadai balbalin bala’in ta’addancin Boko Haram yake kamari, su mutanen kudu ba abin da ya dame su, kuma tun da jifa ya wuce kansu to ya fada can kan ‘yan Arewa.
A yanzu dai wannan ta’addancin ya buwayi kowa a kasar nan; idan wani bai yi asara ba to wani nasa ya yi, kuma gwamnati ce kan gaba wajen tagayyara sakamakon haka, domin kuwa tana narkar da dubban miliyoyin Nairori amma hakan bai sa ta’addancin ya tsagaita ba, kuma ‘yan Boko Haram din ba su saduda ba, hasali ma sai kara buwaya suke yi, suna ta kakkame garuruwan da aka girke daruruwan dakarun Najeriya a ciki. Abin dai ya zame tamkar ruwan dare, domin ba Najeriya ce kadai ba ke fama da wannan mummunan al’amari, haka ma wasu manyan kasashen duniya. Dangane da haka ana iya cewa ‘yan Arewar da ake zargi da assasa kungiyar Boko Haram a Najeriya ne suka gurgusa can, suka kunna wutar ta’addancin?
Turawan Amurka da Yammacin Turai sun kawo wa Najeriya dauki, musamman ma don gano mabuyar barayin ‘yan matan Kwalejin ‘yan mata ta Chibok sama da dari biyu, amma lamarin ya zame abin mamaki kamar bacewar nono a kirjin budurwa. Baicin haka nan kuma Gwamnatin Tarayya ta yi hayan wani Baturen kasar Austireliya, Mista Stephen Dabies, wanda aka ce kwararre ne a fannin tattaunawa da masu danke mutane don biyan wata manufarsu ta dabam, don ya tattauna da ‘yan kungiyar da nufin lallashinsu har su ajiye makamansu, su kuma mikawa gwamnatin Najeriya wuya. Mista Dabies dai bai yi nasara ba, ya kuma koma garinsu inda ya fitar da wata sanarwa da ke cewa ya ci karo da wani muhimmin bayani game da wadanda suka kasance ummul-haba’isin kafuwa da kuma ruruwar wutar fitinar kungiyar Boko Haram. Ya ce tsohon Gwamnan Jihar Barno, Sanata Ali Modu Sheriff na da hannu dumu-dumu a game da haka, sa’anan kuma tsohon Hafsan-hafsoshin rundunar mayakan Najeriya Laftana-Janar Azubuike Ihejirika ya taimaka ainun wajen cinna wutar masifar ‘yan kungiyar da aka fi sani da Yusufiyya.
Ko da yake wadannan mutanen biyu sun gaggauta karyata wannan zargin, amma talakawan Najeriya sun san cewa biri ya yi kama da mutum, kuma hakan ya tabbatar da cewa zargin da wasu ma suka sha yi game da haka na da kanshin gaskiya. Wasu da yawa sun hakikance cewa Sanata Ali Modu Sheriff na da hannu wajen kafa kungiyar ‘yan bangar siyasa da ake kira ECOMOG, wacce ya yi amfani da ita don dare kujerar gwamnan Jihar Barno a shekrar 2003. Daga bisani ne ya kulla abota da kungiyar Yusufiyya.
Bayan haka ne aka ce wai an samu baraka tsakaninsu, kuma bayan an kai ga yamutsin watan Satumbar 2009 wanda ya fito da kungiyar Yusufiyya fili, aka kuma fahimci irin manufofinta da kuma aikace-aikacenta na ta’addanci da ya yi sanadiyyar asarar daruruwan rayuka a Barno da Bauchi, sai aka ce wai an harbe shugabanta, Muhammad Yusuf bayan sojoji sun kama shi da ransa, suka mikawa ‘yan sanda. Wannan ne mafarin tashin-tashinan da ya zuwa yanzu ya gagari kowa a kasar nan. Mafita daga wannan ja’ibar ita ce ta yin bincike na musamman da gwamnatin tarayya za ta sanya a yi don tabbatar da zargin wancan Baturen Austireliya da kuma neman gano wanda ya bayar da umurnin kashe madugun kungiyar Yusufiyya, Mohammed Yusuf. Kada fa a yi wasa da zargin wancan baturen domin maganarsa abar dubawa ce.