Wanne ya fi alfanu: Gyaran hanyoyin mota ko gina hanyoyin jirgin kasa?

A makon nan ne Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirinta na gina hanyoyin jirkin kasa a wasu sassa na kasar nan. Abin tambaya a nan shi ne, shin a gyara muhimman hanyoyin mota da suka lalace shi ya fi ko kuwa samar da sababbin hanyoyin jirgin kasa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin […]

Wanne ya fi alfanu: Gyaran hanyoyin mota ko gina hanyoyin jirgin kasa?

A makon nan ne Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirinta na gina hanyoyin jirkin kasa a wasu sassa na kasar nan. Abin tambaya a nan shi ne, shin a gyara muhimman hanyoyin mota da suka lalace shi ya fi ko kuwa samar da sababbin hanyoyin jirgin kasa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

 

Hanyar jirgin kasa ta fi muhimmanci – Muhammadu Sani

Aliyu Babankarfi, a Zariya

Muhammadu Sani, shugaban leburorin tashar jirgin kasa da ke Zariya: “A ra’ayina, gyarawa da gina hanyoyin jirgin kasa ya fi muhimmanci fiye da na mota a bisa dalilaina kamar haka: Jirgin kasa ya fi muhimmanci ta kowace irin siffa. Shi ne yake kawo sauki ga mutanen Najeriya, wanda saboda kayayyakin safara da ake shigowa da su kasar nan, da ake shigar da su hannun talakawa. Ba za a samu saukinsu ba sai ta karkashin jiragen kasa. Ta haka ne kyautatuwar kayayyakin suke saukin samuwa a hannun talaka, sannan kuma na karshen, shi ne yake dauke da kashi arba’in da biyar na mutanen Najeriya.”

 

 

Gyaran hanyar mota ya fi – Alhassan Mustapha

Kabir Yayo Ali, a Ibadan

Alhaji Alhassan Mustapha: “Ina ganin ci gaba da aikin gyaran hanyoyin da suka lalace ya fi muhimmanci fiye da kirkiro wani sabon aiki da za a kashe mukudan kudi ba tare da sanin lokacin da za a kammala shi ba. Idan aka gyara hanyoyin da suka lalace, za a samu ragowar aukuwar hadurran motoci da ke lakume rayukan mutane da barnatar da kadarori na miliyoyin kudade kuma za a samu saukin gudanar da harkokin sufuri a kan hanyoyin Najeriya.”

 

 

Jirgin kasa ya fi amfani – Muhammadu Sani

Aliyu Babankarfi, a Zariya

Muhammadu Sani Akko, shugaban direbobin kanta na Zariya: “A ra’ayina, matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka na gyara hanyoyin jirgin kasa zai fi amfanar da al’umma fiye da gyara hanyar mota, duk ko da sana’ata ce tukin mota. Idan ka duba amfanin da jirgin kasa ke kawowa, ya fi na mota fiye da yadda ba a zato ga talaka, kai har ma ga wanda ba talaka ba. Haka kuma karfafa sufurin jirgin zai rage mutuwar hanyoyin mota a Najeriya kuma al’umma za su amfana fiye da yadda suke amfana da sufurin mota.”

 

Hanyar mota ta fi muhimmanci – Rashida Dauda

Rabilu Abubakar, a Gombe

Rashida Dauda Tijjani: “A ra’ayina, a fara gyra titin mota domin shi ne ya fi amfanar duk wani dan Najeriya saboda kowa ya tashi sayen abin hawa, mota ko babur yake saye; domin shi ne daidai karfinsa ba jirgin kasa ba. Ni din nan ma yanzu da nake magana, ban ta taba shiga jirgin kasa ba amma na shiga mota yafi a kirga. Ka ga ashe dan Najeriya ya fi amfana da titin mota a kan na jirgin kasa. Idan dai a harkar sufuri ne, babu yadda za a kwatanta mota da jirgi, domin kafin mutum ya shiga jirgi sau daya ya shiga mota sau dari. Idan haka ne kuwa, ashe titin mota ya fi kyau a fi mayar da hankali a kai.”

 

 

 

Hanyar jirgi ta fi muhimmanci – Abubakar Zubairu

Kabir Yayo Ali, a Ibadan

Abubakar Zubairu: “Alal hakika a matsayina na dan Najeriya da na saba yin tafiye-tafiye a cikin mota da jirgin kasa zuwa sassa daban-daban na kasar nan, a gaskiya ina da ra’ayi dari-bisa-dari na goyon bayan wannan muhimmin aiki na shimfida layin dogo daga Kano zuwa Daura ya wuce zuwa Maiduguri. Miliyoyin mutane ’yan Najeriya za su amfana sosai da wannan sabon aiki da Gwamnatin Tarayya take shirin yi. Ina ganin amfanin wannan aiki ya fi gyaran hanyoyin mota muhimmanci ga jama’a.”

 

Jirgin kasa ya fi muhimmanci – Ardo Kulani

Rabilu Abubakar, a Gombe

Ardo Kulani: “A matsayina na dan Najeriya da ya san muhimmancin jirgin kasa tun a shekarun 1980, na san Jirgin kasa ya fi mota amfani, musammamn ma wajen daukar kaya mai yawa da kuma samun sauki. Yanzu idan za a yi zirga-zirgar kaya daga wani gari zuwa wani ko daga wata kasa zuwa wata, dauka a jirgin kasa ya fi riba da kuma sauki. Ashe kuwa ya fi cancanta gwamnati ta gyara titin jirgin kasa a kan na mota. Ko wajen samun kudin shiga ga gwamnati, za a fi samu da yawa a kan ta bangaren masu motoci saboda jirgi ya fi samar da kudin shiga, idan yana aiki yadda ya kamata. Titunan motar ma za a rage bin su.”