Wanne ya fi muihimmanci a tsakanin hankali da ilimi?

Wakilanmu a wasu daga sassan kasar nan sun tattauna da mamakrantanmu a kan taken Muhawararmu ta wannan mako kuma abin da abin da kowane daga cikinsu yake cewa kamar haka: Hankali ya fi komai -Alhaji Sani Azare Adam Umar, Abuja Hankali ya fi komai. Saboda sai da hankali ne za a nemi ilimin kansa sannan har […]

Wanne ya fi muihimmanci a tsakanin hankali da ilimi?
Wanne ya fi muihimmanci a tsakanin hankali da ilimi?

Wakilanmu a wasu daga sassan kasar nan sun tattauna da mamakrantanmu a kan taken Muhawararmu ta wannan mako kuma abin da abin da kowane daga cikinsu yake cewa kamar haka:

Hankali ya fi komai -Alhaji Sani Azare

Adam Umar, Abuja

Hankali ya fi komai. Saboda sai da hankali ne za a nemi ilimin kansa sannan har ya yi amfani. Kuma komai tarin ilimi in dai babu hankali, barna zai samar a maimakon amfanarwa ko gyara. Haka nan rashin hankali zai sa mutum ya zaci abinda yake yi daidai ne ko da barna ne yake tafkawa.

Hankali ya fi ilimi -Alhaji Umar Faruk Muhammad

Adam Umar, Abuja

Hankali ya fi ilimi. Saboda ko da mutum ya samu ilimin a cikin halin rashin ishashshen hankali, to ba zai yi amfani da shi yadda ya kamata ba idan bai da hankali. Haka kuma ko a wajen neman jagoranci na shugabanci ko na jan ragamar jama’a a cikin mota, ba mai tarin ilimi a ke baiwa muhimmanci ba, mai hankalin nan dai wanda shi ke da natsuwa da tinanin abu kaza shi ya fi kamata, a ke nema.

In babu hankali ilimi ba shi da amfani -Abu Isah Sakkwato

Nasiru Bello a Sakkwato
In ba hankali ilmi ba ya da amfani, kowa da nasa ra’ayi da tunani da fadar abin da yake ganin yakamata. A nawa ra’ayin hankali ya fi ilmi amfani a rayuwa don duk ilminka in ba ka da hankali ba ya da amfani. Ko wannan aikin da kake yi na jarida in ba ka da hankali ba za a dauke ka har ka rika aiwatar da shi gwargwadon iyawarka ba. Ka sani duk wanda ba shi da hankali duk ilminsa ba za a aura masa mata ba. Akasarin malaman kiwon lafiya da unguwar zoma duk suna amfani da hankali ne wurin aikin, duk marar hankali ba zai iya wannan aikin ba ko da shi ne littafi uban karatu.

Hankali ne jigon rayuwa -Tasi’u dangata

Nasiru Bello a Sakkwato

A nawa ra’ayin hankali ne jigon rayuwa da ke dauke da duk wani fanni na rayuwa. Dalilina kan wannan zancen da na furta shi ne dubi masu sana’ar hannu yadda suke gudanar da ita ba tare da ilmi ba. Haka kuma ban taba ganin mutumin da ya auri macen da ba ta da hankali ba komai ilminta. Dubi soyayyar da ke tsakanin uwa da da ana iya karbe shi daga hannunta matukar ba ta da hankali. Hankli ne ke jagorantar mutum ya nemi ilmi har ya iya bambance tsakanin fari da baki. Ilmi ba hankali nakasa ne.

Hankali ya fi ilimi muhimmanci –Muhammad Sani Abdullahi

 

A.A. Masagala a Benin

Nine Malam Muhammad Sani Abdullahi Eyaen: “A ganina wadannan abubuwa biyu ko wanne yana nan da matsayinsa da kuma amfaninsa. Sai dai a fahimta ta hankali shi ne na farko domin idan ka duba sai da hankali ake neman ilimi, kuma da hankali ne ilimin yake amfani jama’a. 
Saboda ko a tsarin shari’a ta Addini ko ta Zamani ana bukatar mai hankali domin muddin an rasa hankali to babu maganar amfanin ilimi ai sai da hankali ake samun ilimi duk da ce wa ba wai ina nufin Ilimi ba shi da amfani ba ne.

Hankali na gaba da ilimi –Ustaz Usman Alkanawi

A.A. Masagala a Benin
Ustaz Usman S. Alkanawi: Da farko tukunna, menene hankali kuma menene ilimi? Hankali wani sinadarine da Allah (s.w.t) ya kan sanyashi a zukatan wasu zababbu daga cikin bayinsa wanda yake saduwa zuwa ga kwakwalwarsa don ta gudanar da aikinta daidai Ilimi kuma shi ne yin amfani da hankali da kuma tunani wurin riskar abinda mutum bai sani ba. Don haka tun daga nan za ka fahimci ce wa hankali ya fi Ilimi muhimmanci nesa ba kusa ba.

’Yan bindiga sun kashe mutum 7 da sace dabbobi a Katsina  

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato

Kotu ta soke hukuncin yi wa Jam’iyyar NDC rijista