Wanne za ka fi jin haushi a tsakanin wanda ya kalleka ya kece da dariya da wanda ya kalleka ya barke da kuka?
Kana zamanka, sai wani ya kalleka ya fashe da dariya har da kyalkyatawa. Shi kuma wani da zuwa ya kalleka sai ya rushe da kuka. Abin tambaya a nan shi ne, shin tsakanin wadannan mutane biyu wanne zai fi ba ka haushi? Ga ra’ayoyin da wakilanmu suka kalato mana game da wannan muhawara: Mai dariya […]
Kana zamanka, sai wani ya kalleka ya fashe da dariya har da kyalkyatawa. Shi kuma wani da zuwa ya kalleka sai ya rushe da kuka. Abin tambaya a nan shi ne, shin tsakanin wadannan mutane biyu wanne zai fi ba ka haushi? Ga ra’ayoyin da wakilanmu suka kalato mana game da wannan muhawara:
Mai dariya ya fi ban haushi – Labaran Bature
Ahmad Kabir, a Katsina
Labaran Bature Sararin Tsako: “Mai dariya ne ya fi ban haushi saboda dariya tana cikin rainin wayo da rashin tausayi. Kazalika, dariya haka kawai na cikin cin fuska da wulakantarwa. Saboda haka duk wanda ya dube ka haka kawai ya fashe da dariya babu mai ban haushi irinsa. Duk da ana cewa dariya na daga cikin abin da ke sa wa ka amince da mutun amma mutun ya dube ka ya fashe da dariya, kai!”
Mai dariya ya fi cutarwa – Abubakar Zubairu
Kabir Yayo Ali, a Ibadan
Abubakar Zubairu: “A gaskiya mutumin da ya kalle ni ya kyalkyace da dariya ya fi ba ni haushi, domin watakila ya hango wani abun sakarci da wauta a jikina ne da na aikata ko kuma shi ne ya cutar da ni ba tare da sani na ba, shi ya sa yake kallo na yana yi mini dariya. Amma wanda ya fashe da kuka kuwa, ina zaton wani abun da ya taba cutar da ni a baya shi ne yake yin wannan kuka da zarar ya kalle ni domin tausaya mani.”
Mai kuka ya fi ban haushi – Abu Sufyan
Ahmad Kabir, a Katsina
Abu Sufyanu Funtuwa: “Wanda ya fi bani haushi shi ne wanda da ganina ya fashe da kuka. Dalilina shi ne, an fi son mutun ya zamo cikin raha kowane lokaci ba bakin ciki ba amma kawai sai ka nufo da abin bakin ciki? Kuka ai kowa ya sani nau’i ne na bakin ciki, don haka ni wanda ya dube ni ya fashe da kuka shi ne makiyina ma, ba wai mai ban haushi ba. To an ce masa na rasa wani abu ne da kawai yana kallo na ya fashe da kuka?”
Na fi jin haushin mai kuka – dan Arewa
Kabir Yayo Ali, a Ibadan
Olfijahla Salisu dan Arewa: “Ni zan fi jin haushin wanda ya fashe da kuka a lokacin da ya kalle ni, domin watakila wata hasara ce ta shafe ni ko wani abun bakin ciki ne yake dari-darin fada mani, a maimakon haka ya kama kuka. Shi kuwa wanda ya kalle ni ya kama yin dariya watakila abokin wasana ne ko kuma yana so ya faranta mani rai ne ya sa yake yin wannan dariya.”
Mai kuka ya fi matsala – Muhammadu Sani
Aliyu Babankarfi, a Zariya
Muhammadu Sani Babban Gwani: “Duk wanda ya kalle ka ya fashe da kuka, to akwai matsala. Wanda zai fi ba ni haushi shi ne wanda ya kece da kuka, domin me saboda kuka da kake ganinsa ba hikima ba ne, domin da za ka zaunar da shi ka ji dalilin kecewarsa da kuka kila ma kai da ka riga shi yi wa kanka kukan; donin kuka ba hikima a cikinsa amma dariya ai wannan ba wani abu ba ne saboda halin ma da ake ciki na yanzu kawai kana ganin mutum sai ya kama kyelkyacewa da dariya, kila ko akwai tsohon basir da ke tare da shi ko akwai hauka ko makamancin haka amman kuka ai ba hiki ma.”
Dariya rainin hankali ce – A’ishatu Adamu
Aliyu Babankarfi, a Zariya
A’ishatu Adamu: “Ai ni in dai kuka ne, daga gani na mutum ya fashe da kuka, ai kansa ya yi wa; ni ina ruwana? Amma mutum ya kalle ka ya fashe da dariya, ai rainin hankali ne, domin ka tuna fa har akwai inda idan mutum ya kalle ka ya fashe da dariya, kakan dauki tsinke ne ka mika masa, ka ce ya cire maka abin da ya gani a jikinka da ya ba shi dariya. Amma kuka ai damuwa ce a kan wanda yake yin ta kuma kansa yake yi mawa. Amma idan mutum ya dube ka ya bushe da dariya, to ya raina maka hankali.”