Wargi wuri yake yi
Ficewar Cif Olusegun Obasanjo daga jam’iyyar PDP da rana tsaka gagal, a ranar Litinin da ta gabata, ya hargitsa wa shugabanninta lissafi, domin kuwa ya daga kara ne a gaban tarkon shugabanninta, wadanda yake cewa sun yi mummunar tsarin mike kafa bisa mulki sai Mahdi ya zo, ya ture. A matsayinsa na tsohon shugaban kasa, […]
Ficewar Cif Olusegun Obasanjo daga jam’iyyar PDP da rana tsaka gagal, a ranar Litinin da ta gabata, ya hargitsa wa shugabanninta lissafi, domin kuwa ya daga kara ne a gaban tarkon shugabanninta, wadanda yake cewa sun yi mummunar tsarin mike kafa bisa mulki sai Mahdi ya zo, ya ture. A matsayinsa na tsohon shugaban kasa, wanda ya yi zamani da sojoji da kuma farar hula, Cif Obasanjo na iya fahimtar abubuwan da sukan je, su kuma komo a harkokin siyasar kasar nan. Ya fahimci cewa a halin yanzu dai an dora Najeriya bisa wata mummunar turbar da za a gungura ta cikin wani wagegen rami mai zurfin gaske.
An dai ce wanda ya san kudin wada shi zai fayyace farashin jariri, to Obasanjo ya san yadda kulle-kullen da ya yi don zarcewa bisa mulki a karo na uku ya ci tura; yana kuma sane da yadda Janar Ibrahim Babangida ya sha murmurdawa don ya canja kamannu zuwa Shugaban farar hula, ta hanyar sossoke tsarin mayar da mulki farar hula, amma bai kai ga nasarar cikan burinsa ba. Janar Abacha ma ya gwada zarcewa, amma sai ga shi nan mutuwa ta yi masa yankan kauna. To, tun da an ce mugu ne ya san makwanci mugu, ya fahimci irin dabarun da suka bi dangane da zrcewa, ya kuma gano cewa irinsu ne Shugaba Goodluck Jonathan ya dukufa akai a wannan marrar, shi ya sa yake fadakar da talakawa.
Jam’iyyar PDP da shugabanninta sun hanzarta dukkan zargin zarcewa bisa mulki da Cif Obasanjo ya yi, amma har yanzu talakawa ba su gamsu ba, ganin cewa shugabannin jam’iyyar PDP da kuma jiga-jigan gwamnati na kokarin kawo wasu hujjoji da dalilan bogi da za su kawo cikas game da gudanar da zaben ranar 28 ga watan Maris.
Jama’a sun bubbude idanuwa, sun kuma karkasa kunnuwa don fahimta da nakaltar irin rawar da ake zargin Majalisun kasa za su taka daidai da kidan da jam’iyyar PDP za ta buga musu bayan komowarsu bakin aiki daga hutun da suka tafi.
To, ko dai mene ne ke faruwa tsakanin Cif Obasanjo da Shugaba Jonathan bai dada ‘yan Najeriya ba da kasa ba, abin da suka sani, suke kuma cewa shi ne Allah ne Ya kama su, suke yi wa juna bi-ta-da-kulli irin haka, kuma hakan zai sa gaskiya ta fito fili, firi-falo, don jama’a su samu kubuta daga mugun tarko da jam’iyyar PDP ta kafa wa kasar nan. Abin da sauran jama’ar gari ke cewa shi ne an yi bari, ba kuma za a kwashe gaba daya ba. Jam’iyyar PDP ce za ta fi kwaruwa da wannan al’amari, musamman ma ganin yadda ta kidime a cikin ‘yan kwanakin nan saboda barazanar da jam’iyyar APC da dan takararta na shugabancin kasa, Janar Muhammadu Buhari ke yi mata.
Shugabannin PDP sun tabbatar cewa karshen gwamnatin jam’iyyarsu ya zo, kuma muddin dai za a ce za a yi zube-ban-kwaryata ne tsakaninsu da talakawa to, ba wanda zai sha a cikinsu, duk za su kwana ciki. Wannan ne dalilin da ya sa aka tsiri kinibibin da ya kai ga dage zabe don jam’iyyar ta tsiri sababbin shirye-shirye da kinibibin da zai ba ta galaba a zabe, bayan an sha ruwa, an koma wasa. Batun rashin tsaron da aka takalo, har a sabili da shi aka dage zaben, ya zamanto tatsuniyar da talakawan Najeriya suka ki gasgatawa, kuma sakamakon haka sun kwantar da hankulansu, sun ki tayar da hakarkari don kada a samu dalilin yin amfani da jami’an tsaro wajen cin mutuncin jama’a da kuma dakile zaben ma dungurungun.
Jama’a sun nuna rashin amincewarsu da rawar da jami’an tsaro suka nuna cikin harkar dage zaben, sun kuma kara tabbatar da cewa ba ruwan sojoji cikin tsarin gudanar da zabe, saboda haka nan za su ci gaba da bin dokokin kasa don a samu yanayin da zai taimaka wa ‘yan sanda aiwatar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana ba tare da bayar da wata damar da za a tayar da fitinar da za ta kai ga tafka magudi ba.
Ai an aiwatar da zabubbukan kananan hukumomi a tsakiyar yankin da ake dambarwa da ‘yan Boko Haram, watau Jihar Yobe, inda gwamnatin jihar ta gudanar da zaben kananan hukumomi ba tare da wata tangarda ba, me zai hana ba za a bi matakan da aka bi aka kai ga haka ba a lokutan zabubbuka masu zuwa, ba tare da fuskantar hare-hare daga ‘yan ta’adda ba? Shin bikin Magaji yana hana na Magajiya ne? Idan sojoji suna dambarwa da ‘yan ta’adda sai kuma a hana ‘yan sanda agaza wa jama’a gudanar da muhimmin abin da ke gabansu?
Ziyarar da Janar Muhammadu Buhari ya kai Jihar Barno, da kuma yadda jama’a suka yi ta barkowa daga birane da kauyuka, suka yi cincirindo a gefen hanya, saffan-saffa, wasu makale a bisa itatuwa kamar jemagu, wasu kuma dankare a filin taron, daba-daba kamar kwarin dango, ya nuna ke nan jama’a na iya gudanar da muhimmin sha’anin gabansu ba tare da taimakon ‘yan sanda da kuma ‘yan kato-da-gora ba, ba tare da an rabo sojoji daga bakin daga ba, inda za su yi ta yin dauki-ba-dadi da ‘yan ta’adda. Irin abin da ya kamata ya kasance ke nan a ranakun da za a yi zabe: watau jama’a su firfito ba tare da matsi, ko tsangwama, ko tsoron komai ba, su kada kuri’a, domin sun san cewa akwai sojojin da ke can filayen daga suna karawa da wadanda za su iya kawo musu cikas. Babu wani mugun abin da ya faru sakamakon ziyarar Shugaban kasa da Janar Buhari suka kai Jihar Barno don yakin neman zabe, to me zai sa a ce ba za a iya yin zabe ba a irin wadannan wuraren? A tsaya, a tsara zabe kawai, kuma kada a fasa fitowa don kada kuri’u, domin ai shi wargi wuri yake yi.