Warwara da nade-naden sarautu bayan rasuwar Sarkin Zazzau
Tun bayan darewar Sarki Ahmed Bamalli kan karaga aka fara samun wasu sauye-sauye a masarautar.
Tun bayan darewar Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli karaga a matsayin Sarkin Zazzau na 19 aka fara samun wasu sauye-sauye a masarautar.
Bamalli ya hau karagar ce bayan Allah Ya karbi ran tsohon Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris bayan ya kwashe kimanin shekara 45 yana karagar mulki.
- An haifi jariri da azzakari uku
- ’Yan bindiga sun yi amai sun lashe kan Daliban Afaka
- Dan majalisa ya halarci zaman Majalisa tsirara
- Matawalle ya sauke basarake kan ba wa soja mai sayar da makamai sarauta
Sabbin nada-nade
Mai Martaba Sarkin Zazzau Ahmad Nuhu Bamalli ya yi nade-naden sabbin sarautu a fadar Zazzau, cikinsu har da daga darajar sarautar Malam Muhammad Munnir Jafaru, daga matsayin Yariman Zazzau zuwa Madakin Zazzau, sarautar da ita ce ta biyu a jerin sarautun Masarautar Zazzau.
Daga cikin nade-naden da ya fara, akwai sarautar Iyan Zazzau, inda kwana 34 da rasuwar Iya Bashir Aminu, ya nada Dokta Abbas Tajuddeen wanda dan Majalisar Wakilai ne mai wakiltar Zariya.
Sarki ya kuma tumbuke rawanin Ciroman Zazzau, Alhaji Sa’idu Mai Lafiya, daya daga cikin manyan ’yan majalisar Masarautar.
Mai martaba Sarkin Zazzau ya warware rawanin Ciroman Zazzau din ne bisa zargin sa da rashin biyayya da girmama Masarautar.
Wata Majiya daga cikin fadar ta bayyana cewa tsohon Ciroman mai shekarau 84 a duniya, babban dan majalisar sarki kuma dan uwa na kusa ga Sarki Ahmed Bamalli, wanda dukkansu suka fito daga gidan Sarautar Mallawa.
A yanzu haka tsohon Ciroma Alhaji Sa’idu kusan shi ne babba a jerin ’ya’yan sarki da suka fito daga gidan Mallawa a Masarautar Zazzau.
‘Abin da ya sa aka cire ni a matsayin Ciroman Zazzau’
Aminiya ta ziyarci gidan Alhaji Sa’idu Mai Lafiya da ke Kwarbai a cikin birnin Zariya, inda ta cin ma al’umma na ta tururuwa don jajanta masa tare da iyalansa a kan abin da ya faru.
A tattaunawa da Aminiya ta yi da shi bisa abin da ya faru, ya ce, “Zuwa yanzu zan kai shekaru tamanin da wasu abubuwa a duniya. Kamar yadda ka tambaya cewa daga wane gidan sarauta na fito a jerin gidan Sarautun Zazzau, to na fito ne daga gidan Mallawa.
“Da farko dai ina wa marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris addu’a, Allah Ya gafarta masa da rahamarsa, amin.
“Sannan kuma kamar yadda ka tambaya, shekarun da na yi ina rike da sarauta shi ne marigayi Sarkin Zazzau Shehu ya shekara 45 da watanni a wannan gidan ni kuma shekaruna 43 ina rike da sarautar da ya nada ni.
“Da farko marigayi ya nada ni Sarautar Yari, sannan kuma aka kara mani matsayi zuwa sarautan Dan Buran, a inda kafin rasuwarsa aka kara daga matsayina zuwa Sarautar Ciroman Zazzau.
“Kuma abin da muke gode wa Allah da kuma alfahari da shi, shi ne a wancan lokacin nasarorin da aka samu, zaman lafiya da aka samu a lokacin mulkin Sarkin Shehu Idris, domin da wanda suka gaji mulki da ma wadanda ba su gada ba duk ana zaune lafiya tare da girmama mutane, da samun walwalar al’umma.”
Da Aminiya ta so jin ko an tuntube shi kafin cire rawaninsa sai ya ce, “A’a, wallahi babu wanda ya tuntube ni, ni ma a bakin jama’a na ji cewa wai an tsige ni kuma har zuwa yanzu ban samu wata takarda daga gare su ba.
“Kamar yadda ka tambayi alakata da marigayi Iyan Zazzau Alhaji Bashir Aminu, to shi Iya Bashir dan gidan nan ne, domin mahaifiyarsa daga nan gidan ta fito, marigayi Iya Sa’idu ne ya haife ta, dan uwana ne na jini.
“Kuma al’umma da ka gani suna ta zuwa domin yi min jaje wannan na nuna maka cewa mun zauna lafiya da jama’a don haka ina godiya, Allah Ya saka wa kowa da alheri.”
Bayan haka, kuma sarkin ya maye gurbin Mailafiya Barden Zazzau, Alhaji Shehu Tijjani, inda aka masa musaya zuwa Ciroman Zazzau.
Sai shi kuma kanin Ciroman da ya cire din, Alhaji Shehu Mailafiya aka nada shi a matsayin Barden Zazzau.
Al’umomin a Zazzau na bayyana mabambamtan ra’ayoyinsu game da sake fasalin tsarin fada da kuma nade-naden sabbin sarautu tare da sauke wasu jiga-jigan masu sarauta da sarkin ke yi.
Duk wadannan canje-canje da nade-nade na zuwa ne cikin wata 5 kacal da darewar sarkin gadon sarauta.
A ranar 7 ga watan Oktoban bara ce Sakataren Gwamnatin Jihar Kaduna Malam Balarabe Abbas Lawal tare da Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masaratu Alhaji Jafaru Sani, da Wazirin Zazzau Alhaji Ibrahim Muhammad Aminu suka mika wa sabon Sarkin Zazzau na 19 a jerin sarakunan Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamali takardar tabbatar masa da sarautar kuma aka mika masa sandar sarauta da kundin masarautar Zazzau a ranar Litinin 9 ga watan Nuwambar bara.
Mai Martaba Sarkin Zazzau ya dauki damarar sake fasalin tsarin ginin fadar tare da cika wasu alkawura da marigayi Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya yi wa wasu wadanda aka ba takardar zabansu a matsayin masu rike da sarauta a fadar amma Allah cikin ikonSa bai kai lokacin da aka tabbatar da nadin ba sarkin ya rasu, sai bayan hawan sabon sarkin ne aka tabbatar musu da nadin sarautun.
Daga cikin sarautun da ya cika alkawarin tsohon sarkin akwai Sarkin Hatsin Zazzau, da Durbin Zazzau, da Jagaban Matan Zazzau, wadda aka tabbatar wa Hajiya Maryam Abdullahi, sai Kuliyan Zazzau wanda aka tabbatar wa tsohon Mai Shari’a Alhaji Isiyaku Bello.
Daga nan kuma mai Martaba Sarkin Zazzau ya ci gaba da nada sabbin Hakimai da za su taya shi gudanar da mulkin kasar Zazzau, wanda hakan ya haifar da muhawara a tsakanin al’umma.
Duk da kasancewar masarautar ta Zazzau ta yi rashin wasu daga cikin manyan Hakimanta a dan tsakanin nan da dama.
Abin da mutane suke cewa
Aminiya ta zagaya tare da tattaro ra’ayoyin jama’a daban-daban dangane da sauya-sauyen da ake gudanarwa a masarautar ta Zazzau.
Wani mazaunin birnin Zazzau, wanda ya nemi da a sakaya sunansa ya yi Allah wadai da wannan yunkuri, inda ya ce sarautar Zazzau an gina ta ne a kan adalci, shi ya sa ta samu daukaka da fice a fadin kasar Hausa da makwabtanta.
Ya kara da cewa samun dama da walwala a cikin fadar Mai Martaba Sarkin Zazzau ya sa sha’awa da bibiyar abubuwan da ake gudanarwa a cikin masarautar Zazzau a cikin zukatan al’umma.
Ya bayyana cewa, “killace Fadar Zazzau ya kara nesanta jama’a da cire sha’awa a zukatan mutane, wanda a baya ba mu saba da haka ba.”
“Akwai ma jama’a daga garuruwan kasar Hausa daban-daban da kan zo domin cin kasuwa a bakin fadar, inda a yanzu sakamakon ginewa da zagaye fadar ya sa dole wannan kasuwa da ta dade ta tashi saboda killace fadar da ake yi.’’
Yunkurin jin ta bakin fadan ya ci tura
Da Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin Masarautar Zazzau bayan kwashe tsawon lokaci, sai Sakataran Masarautar Alhaji Barau Musa Aliyu ya ce irin wannan wani abu ne wanda ya shafi aikin ofis, don haka sai dai a ruboto masu abin da ake bukatar karin bayani.
Sai dai wani da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce sarauta ta sarki ce kuma shi ke nada wanda ya so kuma ya karbi rawanin wanda ya so, “don haka za ka ji a wajen nada sarauta ana cewa Allah Ya ba ka, sarkin ya nada ka, kuma za a fitar da sanarwa nan ba da dadewa ba game da wannan batun da kake yi.”