Wasa Alkalami
Marubutan Hausa sai ku farka, Aikinku na da girma ba kadan ba. Rubutunku don ya zarce warka, Zango ne mai tsawo ba kadan ba Kar ku buge ga batun wasika, Shafukan rayuwa duka bai bari ba. Aikinku ya zam dole ya surka, Jiya da yau ba ku zam bari ba. Da […]
Marubutan Hausa sai ku farka,
Aikinku na da girma ba kadan ba.
Rubutunku don ya zarce warka,
Zango ne mai tsawo ba kadan ba
Kar ku buge ga batun wasika,
Shafukan rayuwa duka bai bari ba.
Aikinku ya zam dole ya surka,
Jiya da yau ba ku zam bari ba.
Da zamani idan zai daukaka,
Daurin ma ba za ku ki kula ba.
Mu dauko himma mu zanka,
Aiki tukuru ba da kosawa ba.
Gudun falalen tsallake tanka,
daukar daga ba za a zam bari ba!