Wasa ko mugunta?
Wasa ko mugunta? Wani Babarbare ne ya hau babbar mota zai je cin kasuwar qauye. Yana da sabbin kuxi a gaban aljihunsa, ana tafiya kuxin suna fita xaya-bayan-xaya kuma bai sani ba. Ashe wani Bafulatani yana gani, idan iska ta xauki xaya sai ya ce: “Ya yi kyau!” Babarbare ya ce: “Kai Xanfulani, ka dame […]
Wasa ko mugunta?
Wani Babarbare ne ya hau babbar mota zai je cin kasuwar qauye. Yana da sabbin kuxi a gaban aljihunsa, ana tafiya kuxin suna fita xaya-bayan-xaya kuma bai sani ba. Ashe wani Bafulatani yana gani, idan iska ta xauki xaya sai ya ce: “Ya yi kyau!” Babarbare ya ce: “Kai Xanfulani, ka dame mu!” Bayan da mota ta tsaya, ya ce: “Xanfulani, sha ruwa ka binne rijiya.” Shi kuwa sai ya yi dariya, ya ce: “Xanborno, tun xazu na ga wasu takardu suna fita daga jikinka. Babarbare ya duba aljihunsa ya ga babu kuxi, sai ya ce: “Xanfulani ka cuce ni, tsakanina da kai Allah Ya isa!”
Daga Garba Sabiyola Gashuwa
Bamaguje da varayi
Wata matar Bamaguje ce ta tirka shanu guda biyu sai ta sayar da su, sai varayi suka shiga gidansu don yin fashi. Suka samu Bamaguje da duka, da ya ji duka sai ya ce: “Kuxin suna gun mai su a ciki.” Sai suka shiga, suka fara dukan matarsa, ta fara ihu tana cewa: “Maigida, maigida!” Shi kuma yana gefe yana cewa: “Ki ba su, kar su kashe ki!”
Daga Abubakar Sani
Masu abin…
Wani Bufilatani ne ya je Saudiyya sai ya ga lasifika a sama, ana karanta Alqur’ani sai ya ce: “Lallai mun zo gidan masu abin, a Saudiyya har bokiti ma ya iya karantun Sabbi!”
Daga Sadibaby da Hasina, 08064981108
Sarakan musu
Wata rana wani mutu yana cika baki a cikin jama’a, cewa babu wanda ya kai shi musu; sai ga wani mutum ya zo ya ce masa: “Kar ka cika baki, akwai wani a gari kaza da ya fi ka iya musu.” Da jin haka sai ya tambayi inda mutumin yake, sai ya shirya ya hau mota ya tafi garin mutumin. Ya isa garin da tsakiyar dare, sai ya tarar da qofar gidan mutumin a rufe. Da ya qwanqwasa qofar, sai mutumin ya tambeye shi cewa waye? Shi kuma ya ce: “Ni ne.” Mutumin ya ce: “Ba kai ne ba.” Haka suka yi ta gardama, baqo na cewa shi ne, shi kuma maigida yana cewa ba shi ba ne. Sai baqon ya ce: “Kai, wannan mutumin ya fi ni musu, bari in koma garinmu.
Daga mai lamba, 08097082395