Wasan biri
Wasu Fulani ne su uku sun shigo birni sai suka ga ana wasa da biri, suka tsaya suna kallo sai aka ce biri ya yi tafiyar Maman Iyabo ta ga mai kudi. Biri ya yi far da ido yana tafiya yana yanga da kwarkwasa kai ka ce wata tsohuwar ’yar bariki. Aka yi ta sanya […]
Wasu Fulani ne su uku sun shigo birni sai suka ga ana wasa da biri, suka tsaya suna kallo sai aka ce biri ya yi tafiyar Maman Iyabo ta ga mai kudi. Biri ya yi far da ido yana tafiya yana yanga da kwarkwasa kai ka ce wata tsohuwar ’yar bariki. Aka yi ta sanya shi yana kwaikwayon abubuwa daban-daban yana yi, aka ce ya yi tsallen kwado, sai ya yi. danfulani ya ji haushin biri, ya ce: “Yau ga shege!” Sai aka ce biri yi zaman danfulani shanu sun kare. Sai biri ya dauko sanda ya sa a kafadarsa, ya lankwashe kafarsa, ya murtuke fuska, ya zare ido, ya langabe kai jikin sanda. danfulani na ganin haka ya bushe da dariya, ya ce: “Tirkashi, aradu kamar Baffa a ruga.”
Daga Adamu Aliyu Ngulde, 07083336622