Wasan Nakiya Da Garma ba sihiri ba ne – Alhaji Mainakiya Da Garma

Wani magidanci da ke yin wasan gargajiya da Hausawa ke kira Nakiya Da Garma a Jihar Legas, mai suna Alhaji Muhammadu Mainakiya Da Garma ya ce wasan gaskiya ne ba tsafi ba ne.Shi dai wasan Nakiya Da Garma wasa ne na gargajiya da masu yinsa suke jefa garma sama suna cafewa don burge jama’a.Muhammadu, wanda […]

Wasan Nakiya Da Garma ba sihiri ba ne – Alhaji Mainakiya Da Garma
Wasan Nakiya Da Garma ba sihiri ba ne – Alhaji Mainakiya Da Garma

Wani magidanci da ke yin wasan gargajiya da Hausawa ke kira Nakiya Da Garma a Jihar Legas, mai suna Alhaji Muhammadu Mainakiya Da Garma ya ce wasan gaskiya ne ba tsafi ba ne.
Shi dai wasan Nakiya Da Garma wasa ne na gargajiya da masu yinsa suke jefa garma sama suna cafewa don burge jama’a.
Muhammadu, wanda ake yi masa lakabi da Alhaji ya ce: “Gaskiya ina son na tabbatar wa jama’a cewa mu masu wasan Nakiya Da Garma na yanzu ba ma yin amfani da sihiri, tsabar kwarewa muke amfani da ita. Don tun kafin ka fara sai an koya maka, idan ba ka koya ba duk sihirinka babu yadda za a yi ka iya jefa garma sama kuma ka cafe ba tare da ta kauce ta yi maka rauni ba.”
Ya ci gaba cewa: “Koda ka kware wani lokaci, idan aka samu bacin rana garmar takan iya kaucewa ta yi maka rauni. Saboda haka sai ka iya, ka san yadda ake rike ta kuma ka koyi yadda ake jefawa da kuma yadda ake cafewa.”
Ya ce ya koyi wasan Nakiya Da Garma a wurin mahaifinsa tun yana karami, ya samu fiye da shekaru 20 yana yin wasan.
Kamar yadda ya kara bayani, ya ce shi dan asalin kauyen Kayarda ne da ke cikin garin Saminaka a Jihar Kaduna kuma ya yi kimanin shekaru 40 a duniya tare da iyali da ’ya’ya tara.
Ya bayyana cewa ya zo Jihar Legas ne don yin was an a matsayin sana’a don samun abincin da zai ci. Sai dai ya ce ya taba gamuwa da matsala a lokacin da yake was an, inda garmar ta yi masa rauni.
“Akwai lokacin da nake wasa, na jefa ta sama sai rana ta kashe mini ido ya zama ba na ganinta, ni kuma maimakon na kauce saboda kada na ba ’yan kallo kunya sai na tsaya. Sai kuwa ta fado mini a fuska, ta yi mini rauni har ta cire mini hakori. Gaskiya ba zan taba mantawa da wannan rana ba a rayuwata ba.” Inji shi.
Ya kara da cewa yana dauran tsummokara da sanya hula da rike karfen nakiya wacce take hade da garma a jikinta yayin da zai yi wasa. Ya bayyana cewa yana son daya daga cikin ’ya’yansa ya gaje shi, yadda shi ma ya gada daga wurin mahaifinsa.