Wasika ga Jonathan: Al-Mustapha ya bukaci su yi mukabala da Obasanjo
Tsohon Babban Jami’in Tsaron marigayi Shugaban kasa Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha ya bukaci yi n mukabala da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo kan zarginsa na cewa ana horar da makasa kamar yadda ya fada a wasikarsa ga Shugaba Jonathan.Manjo Al-Mustapha ya ce duk da cewa akwai harkokin tsaro na sirri da suke fakewa […]
Tsohon Babban Jami’in Tsaron marigayi Shugaban kasa Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha ya bukaci yi n mukabala da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo kan zarginsa na cewa ana horar da makasa kamar yadda ya fada a wasikarsa ga Shugaba Jonathan.
Manjo Al-Mustapha ya ce duk da cewa akwai harkokin tsaro na sirri da suke fakewa a karkashin manufofi da dama, amma ya nace cewa babu wata makarkashiya da wani ke yi ga Arewa ko Obasanjo da aka sanya shi a ciki.
Manjo Al-Mustapha ya bayyana haka ne ga sashin Hausa na Muryar Amurka a shekaranjiya Laraba, inda ya roki Obasanjo ya amince su yi mukabala a daya daga cikin manyan tashoshin talabijin na duniya kamar CNN ko Al-Jazira, ya ce ta haka ne ’yan Najeriya za su gano wane ne ya san sirrin Najeriya a tsakaninsu.
Duk da cewa Obasanjo bai ambaci sunan Al-Mustapha a wasikar ba, amma masu sharhi kan harkokin siyasar kasar suna ganin akwai inda Obasanjo yake gugar zana ga Manjo din.
Al-Mustapha ye ce baya nan lokacin da Obasanjo ya rubuta wasikarsa da tuni ya mayar da martani. Dangane da jita-jitar cewa shugaba Jonathan zai yi amfani da Manjo Hamza ya horar da wasu ’yan banga da za su kashe ’yan hamayya, ya rantse cewa babu wani abu kamar haka. Ya ce bai sani ba ko Obasanjo da mukarrabansa suna shirya wani abu makamancin haka.
Ya ce wadanda ba su da imani suna ganin yafewar da ya ce ya yi ba da gaske ba ne, dalili ke nan suke yin wasu abubuwa. Ya ce a yi addu’a Obasanjo ya yarda su yi mahawara ido-da-ido a bainar duniya kowa ya ji domin gaskiya ta fito.