Wasika Ga Shugaba Buhari: Lokacin Sulhu Da ’Yan Boko Haram Ya Yi

Ya mai girma Shugaban kasa, Allah ne cikin iko da hikimarSa Ya amshi addu’oinmu, ’yan kasa, Ya shugabantar da kai a kanmu, domin tsammanin da muke da shi na za ka zamo mai jinkai da rahama a gare mu. Alhamdu lillahi, fata da burin da muke da su a kanka sun fara bayyana, domin sanin […]

Wasika Ga Shugaba Buhari: Lokacin Sulhu Da ’Yan Boko Haram Ya Yi
Wasika Ga Shugaba Buhari: Lokacin Sulhu Da ’Yan Boko Haram Ya Yi

Ya mai girma Shugaban kasa, Allah ne cikin iko da hikimarSa Ya amshi addu’oinmu, ’yan kasa, Ya shugabantar da kai a kanmu, domin tsammanin da muke da shi na za ka zamo mai jinkai da rahama a gare mu.
Alhamdu lillahi, fata da burin da muke da su a kanka sun fara bayyana, domin sanin kowa ne a kasar nan hankula sun samu kwanciya. Zuciyoyi na dada samun natsuwa daga tashe-tashen hankula da masifar ’yan Boko Haram da ake shan fama da ita da dadewa, musamman a Arewacin kasar nan; wadda ba don Allah da Ya taimaka Ya kawo mana canjin gwamnati ba, da yanzu ba mu san inda lamarin ya kai mu ba, saboda ta’azzararsa da fantsamarsa.
Lallai ba karamin kokari gwamnatinka ta yi ba na ganin ta dakusar da aniyar wannan kungiya ta Boko Haram ba, domin a bayyane kuma a fili yake, lokacin da ka shata wa dakarun Najeriya kudiri kuma Ka ba su wani takaitaccen lokacin da kake son ganin sun yi galaba a kan mayakan  kungiyar Boko Haram. Hakan kuwa aka yi, domin ba mu shiga sabuwar shekarar nan ba sai da sojojin Najeriya suka kutsa har makakabar kungiyar Boko Haram suka yi masu illa, suka karya lagonsu. Kuma suka yi nasarar ceto mutane da dama, wadanda mayakan kungiyar suka sace don wasu manufofinsu.
Alal hakika mun ji dadin wannan kwazo da sojojin Najeriya suka yi a karkashin shugabancinka, domin ko ba komi ka taimaka masu, kima da darajarsu ta sake dawowa a idon duniya, kamar yadda aka sansu tun a farko.
Sai dai wani hanzari ba gudu ba shi ne, ya mai girma Shugaban kasa, muna son a yi mana izini mu kawo wasu shawarwari da muke ganin sun dace a dora su a kan wannan kokari da buri da gwamnatinka ke da su na ganin ta ga bayan wannan kungiya ta Boko Haram. Shawarwarin kuwa su ne kamar haka:
Ya mai girma Shugaban kasa, mu sai muke ganin yanzu an iso lokacin da ya dace a duba yiwuwar yin sulhu da kungiyar Jama’atul ahlil sunna Lild da’awati wal jihad watau Boko Haram. Domin in da a can baya ba a san su waye su ba, ba a san inda suke ba, to yanzu an sani, a dalilin kutsawar da aka yi cikinsu tare da kama wasu membobin kungiyar da dama; ciki kuwa har da wasu shuwagabanninsu, tare da samun bayanai da labarunsu na sirri da aka yi daga jama’ar da aka ceto, wadanda suka kama suka tsare a wurinsu.
Mu muna ganin dacewar a yi sulhu da su ne, domin a samu damar takaita zubar da jinin al’umma da ake ta fama da shi. Domin idan muka lura, lallai an yi galaba a kan ’yan Boko Haram a fagen fama amma kuma ya za a yi da burbushinsu da suka rigaya suka fantsama a cikin kasa, suka saje da al’umma kuma suke ta ci gaba da yaduwa tare da yin nasarar ta’asarsu a duk lokacin da suka yi yunkurin yin hakan, in ba ta hanyar sulhu ba? Domin ko a ’yan kwanakin nan, ranar wata Asabar da ta gabata, talatin ga watan daya na wannan shekarar, ’yan Boko Haram sun yi nasarar kai wani hari mafi muni a farkon wanan shekarar, harin da ya tayar wa da kowa hankali a kasar nan saboda yawan hasarar rayukan da ya biyo bayansa. Har wayau  kuma za a samu damar rage fargaba da zaman dar da al’ummomin yankin ke fuskanta. Domin ko al’ummomin da aka umurce su da su koma garuruwansu, sun koma ne kawai amma ba su da wani kwarin gwiwa da tabbacin sun samu zaman lafiya matabbaci.
Amma idan  gwamnati da kanta ta je ta kwankwasa kofar ’yan Boko Haram don gayyato su zuwa ga teburin sulhu kuma cikin lalama da salama, a maimakon tayin sulhu da ta yi masu a can baya. To, lallai mu muna tunanin hakan zai fi, domin za su bayyana, za a tattauna da su kuma a samu matsaya tare da yafiyar da za ta sa su ajiye makamai, a samu zaman lafiya dawwamamma. Kuma su ma za a samu damar ceto su da dawo da su kan tafarki madaidaici tare da inganta rayuwarsu da canza masu tunani daga kiyayya ga ’yan kasa zuwa ga kauna da so da kishin kasarsu, kamar kowane dan kasa.
Kodayake wasu mutane suna ganin kamar gazawa ce ga hukuma ta nemi sulhu daga ’yan tawaye ko ’yan tada kayar bayan kasarta. Mu kuwa sai muke ganin duka wa wada ba zai hana ka mikewa da tsayinka ba, domin Bahaushe ma ya ce, zaman lafiya ya fi zama dan sarki. Ai yin zaman tattaunawar sulhun alheri ne mai yawan gaske, domin tattaunawa da sulhu ne kadai suka san hanyar kashe wutar rigima cikin sauki tare da fahimtar juna. Tattaunawar sulhu ce ke halarto da bangarori biyu da ba su zaman lafiya wuri daya, a zauna kowa ya fadi abin da ba ya yi masa dadi daga dan uwansa a cikin zamantakewa. Ta nan ne ake fahimtar matsalolin juna, ta nan ne ake gano bakin zaren warware matsalar kuma ta nan ne ake samun matakan kare sake faruwar hakan. Akan samu daidaito da maslaha a wurin zaman tattaunawar sulhu. ma’ana, kowa zai fadi matsalarsa, kowa zai gane matsayinsa, mai gaskiya da marar gaskiya. Kuma ta nan ne ake sake musabahar soyayya da ta tabarbare a tsakanin juna. Ta nan ne ake samun damar ba juna hakuri a kan ta’addancin da aka yi wa juna tare da yafe wa juna.
Sau da dama mukan yi husuma da junanmu a cikin rashin sanin ainihin abin da hada mu, ko bisa zargin juna, ko kuskure, ko ma tsokanar junanmu da gangan amma ba abin da ke gano bakin zaren cikin sauki irin zaman tattaunawar sulhu da juna. Sai ka ga ma wani sa’in an yi da na sani ko jin kunyar yin husumar da aka rigaya aka yi da juna.
A don haka ne muke ganin ya dace matukar dacewa, ya mai girma Shugaban kasa, a dai duba yiwuwar tattaunawar sulhu da ’yan Boko Haram kuma muke ganin wannan karon ya zamana hukuma ce da kanta za ta lalabo hanyoyi da matakan da za su kai ga yiwuwar hakan.
Harwayau, yana daga cikin ta mu shawarar ga gwamnati da hukumomin da abin ya shafa, da su juya baya su binciko labarai da rahotannin kwamitocin da aka kafa tun a farkon asalin faruwar husumar, irin su kwamitin Shaikh Ahmad Lemu. Za a iya kuma lalabo mutanen da suka so taka rawar shiga tsakanin lamarin, tun a farko. Irin su mai girma tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo da malamai, sarakuna, da ’yan jarida na gida da na waje da suka so taka rawar kashe wutar rikicin tun farko; sai a hada da bincike da rahotanni na sirrin da aka samu a yanzu, sai a zauna a kalli yadda za a samu yiwuwar tattaunawar sulhu da ’yan Boko Haram.
Lallai mu muna ganin in sha Allahu, idan mai girma Shugaban kasa ya duba wasikarmu da shawarwarin da take dauke da su, za a gane cewa ba komai muke nufi ba, illa fatan kasarmu ta samu dauwamammen zaman lafiya na dindindin.
Ya Allah Ka taimaki Shugaban kasa tare da manufofinsa na alheri. Ya Allah Ka yarda a samu sulhu mai fa’ida tsakanin ’yan kasa, hukuma da ’yan Boko Haram. Ya Allah Ka dawo mana da dauwamammen zaman lafiya ga kasarmu Najeriya, amin.