Wasika ga Wada Nas: Arewa ta tabarbare
Daga Ghali Sule Shugaba Rogo Ranka dade, na taba shaida maka a wasikar baya, cewa a wannan karon zan ba ka cikakken bayani akan wasu lamura, amma abin kamar da wuya saboda tashin hankalin da ya same mu a karshen makon can da farkon wannan makon na kashe-kashe da kiyasi ke nuna sama da mutum […]
Daga Ghali Sule Shugaba Rogo
Ranka dade, na taba shaida maka a wasikar baya, cewa a wannan karon zan ba ka cikakken bayani akan wasu lamura, amma abin kamar da wuya saboda tashin hankalin da ya same mu a karshen makon can da farkon wannan makon na kashe-kashe da kiyasi ke nuna sama da mutum 300 sun hallaka. Hmm! Hakika muna cikin dimuwa a yanzu sai dai ka yi hakuri.
Ina son tsegunta maka irin halin da zababbun ’yan majalisar mu ke ciki tsakanin su da al’umma. Babu wata alaka tunda talakawan suka sha rana da dukan ruwa wajen zabe. Abin takaicin da kona rai, ranka ya dade, shi ne tun da aka yi zaben nan, ko na ce nadin nan, shekaru 12 ko fiye, babu wani kuduri ko yunkuri don tsamo mutanen Arewa daga danniyar da ake musu a wajen rabon tattalin arzikin kasa.
Ka san cewa Jihar Bayelsa ba ta kai gundumar dan majalisar Dattawa na Kano ta kudu ba, amma ka san yanzu suna amsar kudi lakadan a wata daya da ya fi na jIhohin Jigawa da Gombe da Yobe a wata shida. Wai mene ne amfanin zaman taren nan ne? Ga dan banzan gori da ake mana kodayaushe, amma babu mai cewa komai don shi da ‘ya’yan su suna can suna cabawa a Abuja. Hmm!
Ba ma wannan ne abin haushin ba sai ka ji dan talaka na kare muradun wanda bai damu da shi ba, don kawai wani na yin wannan ra’ayin ko don abin kari da za a ba shi. Gaskiyar, ana bauta har yanzu, Ah! Bauta mana, ina ka taba ganin a cusa wa dan Adam akida kuma ya rike ta gamgam kamar addini. Abin tausayi, dan Arewa ya kasa gane bautar da shi ake yi, wai shi yana da ‘yanci, ‘yanci ko hauka, ka dauki son wani mutum ba, don neman riba ko tsoron Allah ba, sai wai kai ka yarda ya zama akan dinya kai kana kasa yunwa ta kashe ka. Allah wadaran naka ya lalace!
Bari ka ji labarin kwalejojin Fasaha na Gwamnatin Tarayya da ke yajin aiki wajen wata bakwai, ba fa don wani abu ba ne, amma sai don ‘ya’yan talakawa ne kawai a makarantun (su nasu na jami’o’in kasashen waje). Haka, ko kasan tattalin arzikin Najeriya ya habbaka kwarai da gaske, ka san ka bar mu ana sai da Dalar Amurka a kan Naira N84 =$1, yau ana sai da ita a kan Naira N172=$1. Ai ko Naira ta samu tagomashi.
Ranka dade, wutar lantarki kuwa ai mun manta ana dauke wuta. Sai uwa uba man fetur, yanzu dai ya kai N120 zuwa N160 a wasu sassa na kasar nan duk da yake ana sayarwa ne a farashin gwamnati a kan N97. Na san ka bar mu ana sai da man a kan N22. Ka ji halin da muke ciki, na san za ka kintato halin da talakawan Arewa ke ciki a yanzu.
Tabarbarewar al’ummar mu ta Arewa ya kai Lahaula! Rashin sanin ciwon kai da mutuwar zuciya da bambadanci ; rashin zumunci da mutunta juna, duk mai mutunci, sai wanda zai ba da kudi ko da ko na sata ne. Mutumin Arewa yau ba ya iya fadar gaskiya ko kan wa ta kama, kamar yadda kuka rika yi. Wannan halin ya taimaka wa gurbatattun ‘yan siyasa don cin karensu babu babbaka. Kamar yadda wani hamshaki ya taba subutar baki ya ce, ‘babu wani kasuwanci a duniya da ya fi ka zama dan siyasa a Najeriya, kuma jam’iyyar da ke kan mulki’, me wannan ke nuna wa? Kuma duk masu wannan wasoson ba su fi su dubu10, amma sun danne mutun sama da miliyan 160. Kuma haka abin zai ta tafiya in ba mu tashi mu ce MUN kI WAYON BA . Idan ka kalli tsananin talauci da jahilcin da mutanen Arewa ke ciki, dan Arewa ne fa aka hana shi kada kuri’a a kudu, don sun san ba zai zabi wanda suke so ba, kai wasu har dukan su aka rika yi da kona kadarar su. Kuma kowa ya san haka babu abin da wani ya yi ko ya ce, amma mu a nan Arewa babu jihar da bai samu kashi 25 cikin 100 din da ake bukata ba! ‘Ya’yan wadanda ba su da abincin mako a ajiye ke wannan fa. Wadannan al’amura na faruwa duk da muna da ta’adar tausassa.
Na so in yi mantuwa kan yadda lamba daya na kasar nan ke fadin cewar ya bada kudi don a sayi masu zabe, amma wani shugaba ko na ce gwamna ya kwashe kudin bai raba ba! Don Allah me wannan ke tabbatar wa? Ashe dai kudin dai aka yi amfani da su don sayar da mutanen Arewa. Ranka dade, da bakin sa ya fadi hakan a Kano lokacin amsar tsohon Gwamnan Kano da ya koma PDP, a wajen taron na ga rainin hankali da ake yi wa talaka. Kash! ko a jikin talakan don su aka debo daga kowane lungu akan Naira dubu daya a wuni don su taya su rawa da juyi.
Idan jaridar Aminiya ta isar maka da wannan wasika ka nema min izini don aikawa da Dokta Aliyu Tilde da Tsohon Sarkin Gwandu, Sa Mustapha Jokolo, takardar fatan alheri tare da Lamidon Adamawa budaddiyar wasika.
A karshe ina cike da alhinin ‘yan matan da ‘yan ta’adda suka kwashe don yin garkuwa da su a jihar Borno, kuma har lokacin da nake rubuta maka wannna takarda babu wani bayani da muka samu na ceto su.
Zan dakata a nan sai wani lokaci kuma insha Allahu. Ina rokon Allah da Ya kyautata makwancinka, Ya jikan duk wadanda suka riga mu gidan gaskiya. Na gode!
Ghali Sule Shugaba Rogo [email protected] (facebook, tweeter, LinkedIn) 08023702045.