Wasika zuwa ga Janar Murtala Mohammed

Ban san wani irin lakabi ya dace in ambace ka da shi ba, musamman a wannan lokacin da lakabin Allah Ya ja zamaninka bai da wani amfani a gare ka, domin ka riga mu gidan gaskiya. Da farko ina mai mika sakon gaisuwata gare ka da fatar kana cikin Rahamar Ubangiji. Bayan haka, kasantuwar wasu […]

Wasika zuwa ga Janar Murtala Mohammed
Wasika zuwa ga Janar Murtala Mohammed

Ban san wani irin lakabi ya dace in ambace ka da shi ba, musamman a wannan lokacin da lakabin Allah Ya ja zamaninka bai da wani amfani a gare ka, domin ka riga mu gidan gaskiya.

Da farko ina mai mika sakon gaisuwata gare ka da fatar kana cikin Rahamar Ubangiji.

Bayan haka, kasantuwar wasu muhimman abubuwa da suke faruwa a wannan shekarar, na ga dacewar rubuta maka wannan wasika.

Sai dai kash! Ban san ta inda zan fara bayyana abin da wasikar tawa ta kunsa ba, saboda dukkan harsashin da ka dasa don ganin mu ’yan Arewa ba mu fuskanci kila-wa-kalan rayuwa ba, wadansu sun rusa su.

An wayi gari yau Arewa mu ne barace-barace a kan titi, mu ne shaye-shaye da yawan batagari, in ka ji jini ya zuba a kasa, to mu-ya-mu ne, saboda mun rasa jajirtaccen jagoran da zai mana jagoranci.

Yaki ya ci mu, kuma ya ci iyayyenmu  da mu da iyayen namu duk mun zama bayi. Ba mu da hanyar bi balle wurin zuwa, haka zalika mun rasa kuzarin tunkarar kowane irin kalubalen rayuwa.

Mutuwar zuciya duk ta cinye mu, ba ma cas balle as, sai zaman jiran ganima daga gwamnati, wanda kuma wannan babban kuskure ne. Yau Arewa an mai damu tamkar karnukan farauta, ba ma karatu sai yawon bangar siyasa, wadanda suka yi karatun ba aikin yi, kuma babu makoma, ga iyayenmu ba su da abin yi, wadanda suka yi aikin sai mutuwa suke ba fansho.

Yankinmu ya zama tamkar kufai, ba a noma sai shuka gawarwaki, kullum cikin zullumi muke ba mu da kwanciyar hankali, saboda rashin nagartaccen jagoran da zai tsaya mana domin gobenmu da ta ’ya’yanmu ta yi kyau.

Babu mai kishinmu balle yankinmu, sun maishe mu tamkar karmami, sai dai su yi amfani da mu wajen cin zarafi da tallar karya da ba mu tarbiyyar rashin kishin kai, sun dagula mana rayuwa matuka.  Za ka zubar da hawaye idan ka ga yadda muke rayuwa a yau.

Ba ma wannan ba, yau a wasu sassan Arewa, natsuwar da za a bauta wa Allah ma an rasa, saboda fargabar abin da ka iya zuwa ya komo. Lalacewar tamu ba a iya nan ta tsaya ba, domin abin ya kai ga har akan iya shigowa a kwashi ’ya’yanmu (sata), a kai su can wata uwa duniya a sake musu addini da tunani. Inna lillahi wa’inna ilahir raji’un.

Duk da Ubangiji Allah bai cika maka kudirorinka na ciyar da kasarmu ba, hakika kai masoyinmu ne, matsayinka tabbatacce ne a zukatanmu, domin har yanzu akwai abubuwan rikitarwa game da abin da ka bari.

Nakan yi mamaki idan na ji an ambaci wani da sunan ‘mai gaskiya’ bayan kai, ina wata gaskiya a wajen mutumin da talakawansa ba ta cikunansu suke ba ta rayukansu suke?

Yau an wayi gari Arewa ta zama tamkar mahauta, sai kisan kiyashi ake mana, kullum cikin zullumi muke ba mu da kwanciyar hankali.

Ga dimokuradiyyar an jingine ta a gefe an koma nadi, ko da jama’a sun zabi wanda suke tsammanin zai share musu hawaye ba a ba su, idan suka fita zanga-zanga a kashe su.

Na jima ina burin zuwa Kano, don kawai in shaki iskar mahaifarka inda ka tashi, sannan in ziyarci kushewarka, in kai wa iyalanka da ’yan uwanka ziyara, domin jina nake tamkar wata tsoka daga gare ka.

Sai dai kash! Tabarbarewar tsaron kasar ya sa na yanke kauna da hakan. Nakan yi kuka in yi hawaye duk lokacin da na ga hotonka a jikin Murtala (Naira 20), sannan in daga hannuna in yi maka addu’a. Zan yi matukar farin ciki idan ’yan uwanka da iyalanka suka samu wannan wasikar tawa.

A karshe ina yi maka fatar kwanciya cikin ludufi da rahamar Ubangiji, tare da addu’ar Allah Ya hada mu a gidan aminci(Aljanna).

 

Dan ’yar masoyinka, Mohammed Bala Garba, Maiduguri. 08098331260.

[email protected]