Wasika zuwa ga Marigayi Wada Nas

Aminci Allah da Rahamar sa a gare ku mutanen kirki da kuka rigamu gidan gaskiya, muna roka muku aminci da samun haske cikin makwantanku. Allah ya sa haka amin.  Yau na zo ne na gaya maka yadda karshen Gwamnan Adamawa Murtala Nyanko a gidan gwamnati. Makiyya ci gaba da raya al’umma sun sami galaba akan […]

Wasika zuwa ga Marigayi Wada Nas
Wasika zuwa ga Marigayi Wada Nas

Aminci Allah da Rahamar sa a gare ku mutanen kirki da kuka rigamu gidan gaskiya, muna roka muku aminci da samun haske cikin makwantanku. Allah ya sa haka amin.  Yau na zo ne na gaya maka yadda karshen Gwamnan Adamawa Murtala Nyanko a gidan gwamnati. Makiyya ci gaba da raya al’umma sun sami galaba akan shi.
Yau daga dukkan alamu kaskanci ya karewa jama’ar Adamawa masu kishin kan su da yiwa mahaifar su fatan alhairi, nasan zaka so jin me ke faruwa, abin nan dai da na tsegunta maka cewar mutanen Arewa ba su iya fadin albarkacin bakinsu, ko gaskiyar abin da suka fahimta sai dai abin da na kan dinya ya gaya musu. Amma watannin baya  sai Murtala Nyako Gwamnan Jihar Adamawa ya yunkura, kasan tsohon soja ya bayyana wani makirci da ake yi wa mutanen Arewa baki daya ga Gwamnoni Arewa. Inda aka yi masa ca! Wai bai kamata ya nuna cewar ana cin zarafin ’ya’yan boran ba. Tun daga wancan lokaci suka tasa tsohon a gaba sai sunga bayan sa, da taimakon ’yan asalin yanki da kuma manyan ’yan asalin Adamawan da suke tare da mai jan ragamar kasar. Yau na ga makiya suna murna, suna holewa a wasu sassa na Abuja kuma duk inda ka ga gungun mutane maganar suke yi.
Abin dubawa a nan shi ne yau mun yi lalacewar da ba ma iya kare kanmu da kanmu, don amfanin kanmu, a ce mutumin wani tsallake zai zo ya yi amfani da ’yan asalin Adamawa don biyan bukatar kashin kansa, ba don al’ummar Adamawa ba ko kishin makomar su, duk da halin tsaka mai wuya da aka saka al’ummar Adamawa na rashin kwanciyar hankali, karya musu tattalin arzikin da matsi da kaskanci daga hannun jami’an tsaro, duk wannan bai sa mutumin Adamawa ya gamsu cewar shi ne ba a so watau (talakan yankin) haka ’yan majalissar da  al’ummar Adamawa suka taru, suka zaba su ne yau aka yi amfani da su, don kunyata shugaban su, kuma har wasu ke murna halin da suke ciki.  
Hmm! Ranka ya dade na yi bakin cikin yadda Fulani da sauran kabilun Adamawa suka bari rikicin dan su da shugabancin kasar nan ya kai ga inda suka watsa wa dan su kasa a ido. Mutanen Adamawa tarihi zai dade yana nuna irin lalacewar da al’ummar jihar suka yi da sunan siyasa , Ranka ya dade ka sani an dade ana son yin hakan a Jihar  Ribas da Jihar Imo, a Kudu maso Kudu na kasar nan, amma a’lummar yanki suka tsaya tsayin daka, don kare mutuncin gwamnan su da jihar su. Amma yau mutumin Adamawa ya zama mara kishi da son nashi don samun abin da zai bari a nan duniya.
Faruwar haka ciki sauki da sauri ya nuna irin amintar da al’ummar Adamawa suka yi na bautar da kansu don biyan bukatar wani wanda shi kuma ba ya kaunar ganin irin su a doron kasa. Abin nan ya dada tabbatar da cewar tarihi yana maimaita kanshi karni zuwa karni, dubi halin da Arewa ke ciki, a yau, to wannan nake ji musu tsoro in hakan ta faru kuwa, to sai dai Allah ya saukake. Ranka ya dade kamar yadda ka sha fada cewar in mun salladar da mulki sai mun zama bayi, ga shi kuwa.
Shi nake ganin zai faru a Adamawa. Tabbas jama’ar Adamawa za su yi da na sani da nadama a lokacin da ba za tayi amfani ba. Abin takaici shi ne mutanen Adamawa suna da shahararrun mutane daga sojoji da ’yan siyasa da ’yan kasuwa, amma marasa kishi don sun dade suna amfani da rashin wayewar jama’ar su, don danne su.
A Jihar Adamawa dama tun ba yau ba, akwai masu neman haka ta faru.  Yau an karya ludayin shan fura, kun zama daya da marashi.
A karshe ina jajanta wa al’ummar Adamawa akan fadawa cikin wannan tashin hankali da kaskanci, haka ina yaba wa Baba Mai mangwaro Murtala Nyanko dangane da karfin halin da ya nuna wajen farkar da al’ummar Arewa, don su shirya wa makircin da ake kullawa. Amma yin hakan ga abin da ya jawo maka duk da irin rawar da ka taka wajen tabbatar da Goodluck akan karagar mulki a 2011.
Ranka dade zan tsaya nan, sai na dawo don gaya maka abin da ya biyo bayan tsige gwamna, da kuma shirin da makiya za su zartar don yaudarar lalatattun mu, don samun biyan bukatar su cikin hanzari.
Allah Ya fidda Najeriya cikin hannun marasa kishi da son zaman lafiya. Allah Ka ba mu shugabanni nagari masu tausayi da sanin ya kamata. Allah Ka samar mana da zaman lafiya da kwanciyar hankali da karin arziki.

Ghali Sule Shugaba Rogo ya rubuto makalarsa daga Rogo 08023702045 [email protected]
(facebook, LinkedIn, tweeter)

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno