Wasika zuwa ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Cikin girmamawa, tare da fatan wannan wasika tawa za ta same ka cikin aminci da walwalar zuciya, ya mai girma zababben Shugaba kasa, kasancewar wannan shi ne karon fari da zan isar da wani sako zuwa gare ka tun bayan bayyanaka a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 28 na watan Maris din shekarar da […]
Cikin girmamawa, tare da fatan wannan wasika tawa za ta same ka cikin aminci da walwalar zuciya, ya mai girma zababben Shugaba kasa, kasancewar wannan shi ne karon fari da zan isar da wani sako zuwa gare ka tun bayan bayyanaka a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 28 na watan Maris din shekarar da muke ciki da gagarumin rinjaye, na ga ya kamata in bude wasikata da taya ka murna bisa wannan nasara da Allah ya ba ka tare da fatan Allah ya ba ka ikon sauke nauyin da ya rataya a wuyanka cikin gudanar da mulki bisa gaskiyar da duniya ta yi maka shaida akanta tareda tabbatar da adalci tsakanin al’ummar wannan kasa.
Na yanke shawarar rubuto wannan wasika ne a daidai lokacin da kake shirin rantsuwar kama aiki gadan-gadan a matsayin Shugaban kasar Najeriya mai cikakken iko, domin tunatar da kai wasu muhimman al’amuran da za su taimaka matuka wajen cika burin da mafi yawan al’ummar Najeriya suka dora wa gwamnatinka mai shirin kama aiki nan da ‘yan sa’o’i masu zuwa, na tabbata gwamnatin jam’iyyar APC ba za ta manta da halaccin da talakawa suka nuna mata ba tun farkon fara wannan
tafiya, al’umma sun nuna halacci a lokacin yakin neman zabe wanda al’umma ce ta yi karo-karo wajen tara kudaden da APC ta yi yakin neman zabe ba don komai ba sai don kwarin gwiwa da take da shi a kan salon tafiyar da mulki zai canza karkashin jagorancinka. Kazalika tarihin siyasar kasar nan ba zai manta da irin soyayyar da al’umma suka nuna wajen ajiye sana’o’insu da sauran harkokinsu na yau da kullum domin halartar tarukan yakin neman zabe musamman naka ya maigirma Shugaban kasa, na san ba ka manta yadda al’umma suka rika kuka a gabanka ba, a jihohi daban-daban musamman Arewa maso Gabashin Najeriya, tabbas ba za ka manta da yadda al’umma suka jure wa zafin rana da ruwa da iska da sanyi da wasu suka hana idonsu barci domin tabbatuwar wannan nasara tun daga farkon tafiyar har zuwa wannan lokaci.Tare da fatan cewa bukatarsu ta samun canjin salon mulki na zaluci zuwa na gaskiya da rikon amana za ta biya idan Allah ya kawo ka wannan matsayi.Yanzu dai kwalliya ta biya kudin sabulu an samu nasarar kawar da Shugabannin da suka kwashe shekaru suna mulkin wannan kasa ba tare da kawo wani ci gaba ba a kasa. Ya maigirma zababben Shugaban kasa yanzu me ne ne abin yi? Ta ina za a fara? Canjin da ake nema na kawar da Shugabannin da kasawarsu ta fito fili , ta yaya za a samar da canjin na gudanarwar al’amura?
Maigirma zababben Shugaban kasa! Gogewa da jajircewarka sun fito fili bisa la’akari da tarihin ayyukanka a matakai daban-daban. Wannan ta sa ba na haufi ko gezau a kan za ka nemo bakin zaren matsalolin da suka yi wa kasarmu dabaibayi sannan ka warwaresu cikin taimakon Allah, zan so na kara maka kaimi a kan kudirinka na yaki da cin hanci da karbar rashawa, hakika wannan matsala da na ambata ita ce tushe kuma jigon susucewar al’amura a kasar nan, hakika yaki da cin hanci da rashawa zai sanya wasu matsalolin su magance kansu da kansu, wanda da ma cin hancin shi ne ya haifar da su! Ya maigirma Shugaban kasa, matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa ya taka rawa sosai wajen haifar mana da matsalar rashin tsaron da ke ci gaba da lakume rayukan ’yan kasa da kuma raba su da muhallinsu. An yi amfani da wannan matsala wajen jefa matasa da dama cikin kungiyoyin ta da zaune tsaye da sara-suka tareda bangar siyasa.
Samar da wutar lantarki a kasa zai taimaka kwarai wajen rage adadin matasan da ke raya majalisu tare da kashe wanduna ba aikin fari balle na baki. Tattalin arzikin Najeriya ya shiga halin ni-’ya-su, sakamakon dogaro da albarkatun man fetur da kasarmu ke yi tsawon lokaci, duk da yake Allah ya huwace wa kasarmu filayen noma da sauran ma’adinai, Tabbas idan gwamnatinka ta farfado da tattalin arziki talaka zai samu sa’ida daga kangin talaucin da ya yi wa al’umma daurin talala! Daga cikin manyan abubuwan da suka fi ci mana tuwo a kwarya cikin wannan kasa su ne, matsalar rashin tsaro, lalacewar harkar ilmi da lafiya da kuma tabbatar da mulki na adalci.Hakika bayar da muhimmanci a kan abubuwan da na gabatar zai sanya nutsuwa a zukatan ’yan kasa tare da samun ci gaba mai dorewa.
Muna sane da cewa an yi wa wannan kasa kisan mummuke , ta ko’ina an kassara al’amura. Don haka ina mai ba ka tabbacin talaka ba zai sanya garaje ko kawo nesa kusa ba, za mu zage damtse sosai wajen bin doka da oda wacce yanzu karyata ya zamo mana jiki. Za mu ba ka duk wani hadin kai da kake bukata wajen ciyar da kasarmu gaba. Mun sani cewa aikin ba naka ba ne kai kadai wajibi ne mu hadu waje guda domin kai kasarmu tudun mun tsira.
Kwamared Sagir Musbahu Daura Dole
Shugaban kungiyar Muryar Talaka na jihar Katsina 08095597525