Wasika zuwa ga ’yan siyasa (3)
Idan kana son ka san yadda ’yanci yake a dimokuradiyya ka kalli kawai abin da aka yi kwanan nan a Faransa. Jaridar Charlie Hebdo ta yi batunci ga Manzon Allah (SAW) amma ba ta yi laifi ba. Ta bata ran Musulmi miliyan dubu biyu amma cikin ’yancinta ne, wai tana da hakkin ta yi haka. […]
Idan kana son ka san yadda ’yanci yake a dimokuradiyya ka kalli kawai abin da aka yi kwanan nan a Faransa. Jaridar Charlie Hebdo ta yi batunci ga Manzon Allah (SAW) amma ba ta yi laifi ba. Ta bata ran Musulmi miliyan dubu biyu amma cikin ’yancinta ne, wai tana da hakkin ta yi haka. Shugabannin kasashe sama da ashirin sun yi jerin gwano don su taya ta juyayin abin da ya same ta. Sannan kuma duk da haka daga bisani ta sake yin abin da ta yi da farko, kyale ta da aka yi kuma shi ne dimokuradiyya.
Ya ku ’yan uwa Musulmi! Duk da kasancewar wannan tsari na dimokuradiyya yana kunshe da zalunci da cuta a cikin cikinsa, ba mu da makawa gare shi a halin yanzu. Don haka a yayin da zaben gari duka yake gabatowa nan da ’yan kwanaki kadan dole ne mu tunatar da al’ummar Musulmi cewa:
1. Dole ne mu fito mu yi zabe kwanmu da kwarkwatarmu, saboda neman wa al’umma abin da zai zame maslaha gare ta. Kuma duk wanda ya san bai karbi katin jefa kuri’arsa na dindindin ba ya tabbata ya je ya karba. Matasan da suka isa jefa kuri’a a bana kuma a tabbata sun je sun yanki rajista.
2. Ya zama wajibi mu kauce wa fitina da tada hankali, domin ba su haifar da alheri ko kusa ko nesa.
3. Mu sani, siyasa ba sana’a ba ce, duk wanda ya ce wanda ya ba ni shi zan zaba, to, ya jahilci hadarin abin da zai yi. Mutum ne ka amince ka ba shi kuri’a ya yi mulki don dan abin duniya da zai ba ka. A tsawon shekarun da zai yi yana mulki daidansa za ka iya samun lada, amma fa duk jinin da ya bari aka zubar, duk wata rayuwar da ya kyale ta tagayyara, duk wata fitina da tashin hankali da ya haifar…kai, duk wata sata da ya yi ko almundahana a cikin dukiyar jama’a, to, a wurin Allah tare kuka yi su, don kuri’arka ce ta yi masa jagora zuwa hawa wannan mukami!
-Ya ku ’yan siyasa! Zaman lafiyar wannan kasa da ci gabanta shi ya kamata ya zama jagorar abin da kuke yi. Duk wanda yake fafutikar siyasa don kansa kon don mara wa wani baya ba da manufar samun ci gaban al’umma ba, to, ya sani fa shi mayaudari ne, maciyin amana.
Amfani da ’ya’yan mutane, ana ba su kwayoyi suna fita hayyacinsu don a sa su yin rashin kunya da cin mutuncin jama’a, wannan shi ma wata babbar yaudara ce da Allah ba zai kyale ku a kanta ba duniya da Lahira.
– Magudin zabe zamba ne. Zamba kuma aikin ’yan wuta ce. Manzon Allah (SAW) ya ce: “Duk wanda ya yi zamba ba shi tare da ni.” Wanda ba ya tare da Manzon Allah kuwa to, a ina za a same shi?
Ya ku jama’a! Mu sani, wannan zabe na 2015 ya bambanta da sauran zabubbukan da aka yi a baya. Dalili kuwa, babu wani lokaci da al’ummar Musulmi a kasar nan take cikin zilla da wulakanci kamar wannan lokaci. Muna da akalla ’yan gudun hijira sama da miliyan daya. Muna da garuruwa barkatai wadanda aka kone su, ko aka ruguza gidajensu, aka ci mutuncin mazaunansu. Muna da mata da aka kwace su daga hannuwan uwayensu da mazajensu aka bautar da su, kuma babu wanda ya san halin da suke ciki a yau sai Allah.
• Zaben 2015 ya bambanta da inda aka fito saboda matasanmu na fama da rashin aikin yi fiye da inda aka fito kamar yadda alkalumman kididdiga suke nunawa.
• Yana da wahala mu ayyana wani sashi da za mu iya cewa, tsakani da Allah an samu ci gaba a wadannan shekarun na baya. Ilimin ’ya’yanmu ne ya habaka? Jarrabawar makarantun sakandaren da aka fitar a shekarar da ta wuce ba a taba faduwa irinta ba duk tsawon tarihin Najeriya. Ko harkar sufuri ce ta inganta? A yau babu wata jiha da za ka bari zuwa wata ka ce, ka hau sabuwar hanyar da Gwamnatin Tarayya ta shimfida saboda jin dadinmu. Haka sha’anin wutar lantarki, duk masana’antunmu sun durkushe saboda rashin wuta. Fita batun maganar tsaro ko kiwon lafiya ko sha’anin noma da makamantansu.
• A yau kwanaki kadan suka rage mana mu fito mu kada kuri’a a kan dayan biyu: Ko dai tazarce ko a yi sabon zubi. Duk wanda ka zaba za ka yi wa Allah bayanin me ya sa ka zabe shi. Kuma duk abin da zai aikata kai ne mai lamuninsa.
Ya ku al’ummar Musulmi! Muna ji ana ta fadi cewa, babu ruwan siyasa da addini! Mun sha jin ana fadin wannan, duk wanda ya ce haka, ya wautar da addinin Musulunci kuma ya wautar da magabatan Musulmi. Yanzu misali, Shehu Abdullahi da ya wallafa littafai kan siyasa kamar Dhiya’ As-Siyasat da kuma Usul As-Siyasa shigar sharo ba shanu ne ya yi?
Ana cewa, duk wanda ya hau da Constitution yake aiki, wannan magana a zahirinta haka take. Amma tsakani da Allah tun wucewar su Sardauna Ahmadu Bello, wane shugaba aka yi wanda yake aiki da wata doka? Wanda kundin tsarin mulkin ne yake biya? Mu yi wa kanmu adalci don ya amfane mu. Annabi (SAW) yana cewa, halal a fili take, haram ma haka. Kuma yana cewa, ka nemi fatawa daga zuciyarka koda mutane sun yi maka irin tasu fatawar.
Kira zuwa ga jami’an tsaro:
An dauke ku aiki ne saboda al’umma, kuma duk wanda aka dauke shi aiki, Allah zai tambaye shi. Ba aikinku ba ne ku shiga rikicin siyasa, ko ku goyi bayan wata jam’iyya ko wani dan takara. Kowanenku yana da tasa kuri’a da zai jefa, don haka ku yi aikinku tsakani da Allah ban da cin mutuncin jama’a.
Jami’an Hukumar Zabe:
Duk wanda aka dauke shi wannan aiki ya tuna hakkin jama’a yana rataye a wuyansa. Don haka, in ya yi aiki tsakaninsa da Allah ya taimaki kansa, idan kuma ya shigar da kansa a cikin magudi da cin amana, to, Allah fa ba Ya jinkiri ga azzalumi.
Ya Allah! Muna rokonKa, Ka nuna mana baya ga zaben nan cikin aminci. Ya Allah! Ka sanya wannan zabe mafi nagarta da lumana da salama bisa ga duk zaben da aka taba yi a kasar nan. Ya Allah! Ka kare mu daga fitina da tashin hankali. Ya Allah! Ka yi mana zabi na alheri, Ka zabar mana shugabanni nagartattu masu tausayinmu da jinkanmu, masu yi mana adalci, su yi mana mulki bisa kyautatawa. Ya Allah! Duk wanda aka hada kai da shi aka cuce mu, Ubangiji Ka yi mana maganinsa. Ya Allah! Kada ka yi masa jinkiri, kada Ka ba shi lamuni. Ubangiji! Duk wanda ya shanya mu cikin rana, ya wahalar da mu, sannan ya sace kuri’unmu, ya yi mana magudi, ya Allah! Ka hana shi abin da yake so a nan duniya, Ka sakar masa bala’in da ba ya da magani ya Rabbul alamin. Ubangiji! Duk wanda ya kawo mana tashin hankali a wannan kasa, aka nakasa mu ko aka zubar da jininmu ya Allah! Ka nakasa shi a nan duniya kafin Alkiyama, Ka raba shi da jin dadinta da dandanonta.
An ciro wannan Huduba ce daga shafin intanet na Dokta Mansur Sokoto