Wasikar barazanar hallaka ’yar takarar Gwamnan Taraba ta bayyana
Wata wasika da ke kunshe da barazanar hallaka ’yar takararar Gwamnan Jihar Taraba a karkashin Jam’iyyar APC, Hajiya Aisha Alhassan da shugaban jam’iyyar a jihar Alhaji Hassan Ardo tana kawo zaman zullumi ga ’ya’yan jam’yyar a jihar. Wasikar wadda aka jefar da kwafenta a wurare daban-daban a garin Jalingo ta kuma yi barazana ga rayukan […]
Wata wasika da ke kunshe da barazanar hallaka ’yar takararar Gwamnan Jihar Taraba a karkashin Jam’iyyar APC, Hajiya Aisha Alhassan da shugaban jam’iyyar a jihar Alhaji Hassan Ardo tana kawo zaman zullumi ga ’ya’yan jam’yyar a jihar.
Wasikar wadda aka jefar da kwafenta a wurare daban-daban a garin Jalingo ta kuma yi barazana ga rayukan alkalan da suke gudanar da shari’a a kotun sauraren kararrakin zaben Gwamna a jihar da kuma lauyoyin da ke wakiltar ’yar takarar a gaban kotun.
Wasikar wadda ba ta dauke da sa hannun wani ta ce za a yi maganin ’ya’yan jam’iyyar ta APC kamar yadda aka yi wa magoya bayan APC a kananan hukumomin Wukari da Donga da Sardauna inda aka kashe su tare da wulakanta su a lokacin zaben Gwamna da na Shugaban kasa.
“Ko kun manta da abin da aka yi wa magoya bayanku a Wukari da Donga da Sardauna ne a lokutan zabe,” inji wasikar.
Ta kuma yi barazanar cewa wadanda ake so a yi maganinsu wato ’ya’yan Jam’iyyar APC a jihar ba su da wurin buya domin an san duk inda suke kuma za a cimma musu a yi duk abin da ake so a yi musu.
“Ba ku da wurin buya a ko’ina a kasar nan duk inda kuka shiga za mu same ku,” inji wasikar.
Da yake tsokaci kan wasikar, Alhaji Hassan Ardo ya ce wasikar ba ta ba su mamaki ba, domin sun sha fuskantar barazanar kisa su da magoya bayansu a lokuta da dama.
Ya ce sun sanar da jami’an tsaro dangane da wasikar, inda ya ce barazanar da ake yi wa ’yan jam’iyyar a jihar tana dada kamari.
Ya ce an kori hakimi da dagatai masu yawa don kawai gwamnatin jihar tana zargin ba su taimaka wa PDP a lokacin zabe ba. Ya ce a wasu kananan hukumomin jihar an hana wasu ma’aikata albashi wasu kuma aka yi masu canjin wurin aiki kan zargin sun zabi Jam’iyyar APC.
Ya ce abin da ke faruwa a Jihar Taraba ba dimokuradiyya ba ne, illa mulki ne na wariya da nuna bambancin addini wanda ba zai kawo alheri ga jihar ba.
kokarin wakilinmu na jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, ASP Joseph Kwaji kan lamarin ya ci tura.
A halin da ake ciki dai an mayar da zaman kotun zuwa Abuja saboda dalilan da ba za su rasa nasaba da barazanar da aka yi wa alkalan kotun da lauyoyin da suke tsaya wa masu kara ba.