Wasikar Obasanjo ga Jonathan

A ranar Larabar da ta gabata ne kafar yada labarai ta Premium Times ta buga wata wasika da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya aika wa shugaba Jonathan, mai taken; ‘Kafin a Makara,’ inda a cikin wasikar ya farke wa shugaba Jonathan laya, wanda hakan ya sanya mutane da dama a ciki da wajen kasar nan […]

Wasikar Obasanjo ga Jonathan

PHOTO/DOC./PROD. PHOTO/FEB. 10/ACTING L-R: Acting President, Dr. Goodluck Jonathan; Mohammad Abdulhassan and Saad Al Assousi, Kuwait Ambassador to Nigeria, when Kuwait Special Envoy paid a curtesy call to the acting President at the state house… on Wednesday.

Shugaba Goodluck Jonathan da Tsohon shugaban kasa ObasanjoA ranar Larabar da ta gabata ne kafar yada labarai ta Premium Times ta buga wata wasika da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya aika wa shugaba Jonathan, mai taken; ‘Kafin a Makara,’ inda a cikin wasikar ya farke wa shugaba Jonathan laya, wanda hakan ya sanya mutane da dama a ciki da wajen kasar nan suka yi ta tofa albarkacin bakinsu a kan wasikar, inda wadansu ke jinjina wa Obasanjo, wadansu kuma suke la’antarsa. Aminiya ta gutsuro wadansu daga cikin muhimman abubuwan da wasikar ta kunsa kamar haka:
Gabatarwa
Ya zama dole a gare ni in rubuta maka wannan budaddiyar wasikar saboda dalilai masu yawa. Na farko, halin da ake ciki da kuma tunanin abubuwan da za su biyo baya ya sanya ni yin haka domin in jawo hankalinka game da hadarin da ake fuskanta. Na biyu,babu daya daga cikin wasiku hudun da na aika maka da ka ba ni amsa ko ka tabbatar mun cewa sun kai gare ka.Na uku, mutanen da ke kusa da kai, ko kai kanka, suna tambayar wai shin me Obasanjo yake nema ne? Na hudu, halin da muke ciki ya yi kama da wanda muka fada a lokacin mulkin Abacha. Na biyar, dole ne a yi duk abin da ya kamata domin a kare mulkin demokaradiyya tare da kiyaye zubar da jini a kasar nan. Na shida,dole ne mu kare kasar nan daga darewa biyu ta hanyar Arewa da Kudu ko Musulmi da Kirista. Na bakwai, kada a yarda a aikata wani abu da zai gurgunta tattalin arzikin kasar nan. Na takwas, wadansu daga cikin kasashen ketare da masu kaunar bunkasar kasar nan sun nuna matukar damuwarsu game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya. Na tara,ya kamata Najeriya ta yi amfani da damar da ta samu yanzu inda masu zuba jari suke sha’awar zuba jarinsu a nahiyar Afirka, wadda dama ce ta dan kankanin lokaci. Na goma, na damu da abubuwan da za ka bari a bayanka.
Ya shugaban kasa, a lokuta da dama ka sha bayyana yadda Allah Ya yi amfani da ni ya kai ka matsayin da kake kai a halin yanzu, inda har ka sanya ni a matsayin na uku a jerin wadanda suka yi tasiri a rayuwarka, baya ga Allah da iyayenka.Ni kuma na kan ce Allah ne Ya kai ka inda kake, duk wanda ake ganin ya taimaka, Allah ne Ya yi amfani da shi a matsayin sanadi. A ganina, ina ganin a siyasance alheri ne ga Najeriya a ce an samu wani daga cikin kananan kabilun kudancin kasar nan ya zama shugaban kasa. Idan Obasanjo ya kai ga wannan matsayin, ‘Yar’aduwa shi ma ya kai, haka shi ma Jonathan ya kai, kowane dan Najeriya ma yana iya kaiwa. Domin haka babu maganar cewa yanzu lokacin wani bangare ba ne, a’a, domin amfanin kasar nan da kuma daukacin ‘yan Najeriya ne. Domin an tabbatar da cewa babu wata kabila ko wani addini ko yankin kasar nan da zai iya darewa shugabamcin kasar nan shi kadai ba tare da taimakon wadansu ba. Wannan abu ne mai kyau ga Najeriya.. Na sha fada maka cewa Allah Ya yi mini komi a rayuwata, har ma Ya ba ni fiye da abin da nake zato, saboda haka ba na bukatar komi daga wurinka, abin da kawai nake so shi ne ka gudanar da mulkin Najeriya ta yadda ba kawai za ta yi kyau ba, har ma za ta kara bunkasa, na sha godo da kai a kan haka, kuma zan ci gaba da yin haka, domin har yanzu mafi yawan ‘yan Najeriya ba su gani a kasa ba.
Akwai mukamai manya guda biyar wadanda daga Allah sai kai kuke rike da su, da suka dora maka nauyin shugabancin kasar nan, su ne: Jagorancin jam’iyya mai mulki, shugabancin kasa, babban kwamandan rundanar sojar kasar nan, babban jami’in tsaron kasar nan da  kuma shugaban siyasar kasar nan. Wadannan mukamai suna tare da shugaban kasarmu ne, kuma ko kai ne ka yi wani aiki ko kuma sanyawa ka yi a yi, kai ne dai za a ce ka yi.
Ga muhimman shawarwarin da wasikar ta kunsa a takaice;
‘’Ba na fatan a sake zubar da jini saboda rikicin siyasa a Najeriya’’
-Fitina ta yi wa kasar nan kwanto.
-Halin da kasar nan ta fada ta yi kama da na zamanin mulkin Abacha.
-Wajibi ne ka kare tare da kiyaye mulkin demokaradiyya, tare kuma da kiyaye zubar da jini.
-Ka kiyayi abubuwan da za su raba kasar nan biyu, yankin Kudu da Arewa ko musulunci da kiristanci.
-Kada ka bari harkokin tattalin arzikin kasar nan su tsaya cik ko su raunana.
-Ka yi amfani da damar da ake da ita inda masu zuba jari ke son zuba jarinsu a nahiyar Afirka, wacce dama ce ta dan kankanin lokaci.
Lokacin na tafiya
-Ka yi baki biyu game da gudanar da mulki karo daya kawai, haka kuma dangane da batun sake takara a zaben 2015.
-An gurgunta wadansu ‘yan takaran PDP a wadansu zabubbuka domin biya wa Jonathan bukatun siyasa.
-Ka yi nazarin damuwoyi guda biyar na  gwamnonin da suka balle, watau, damuwa da fusata da rashin yarda da tsoro da zargin juna.
-Za a iya kauce wa musifun da za a iya fadawa saboda gazawar gwamnati.
-Ka yi kokarin jawo kowa a jika, lokaci yana kurewa.
Matsalolin rashawa da Boko Haram
-A bayyana sunan duk mai cin rashawa, a tozarta shi, a hukunta shi, kuma a tsaya tsayin-daka wajen yaki da rashawa.
-Nuna karfi kawai ba zai magance matsalar Boko Haram ba.
-Zalunci da rashawa ne tushen ta’addanci da fitintinun siyasa.
-Najeriya ta yi habo kuma dole ne a tsayar da jinin da ke take zubarwa.
Kai daukin gaggawa ga bangaren mai da iskar Gas
-Ka nuna halin ba-sani, ba-sabo a harkar mai da iskar Gas domin kada a bar Najeriya a baya.
-Kada ka gurgunta aikin samar da tagulla na LNG.
-Ka dakatar da satar mai, ka karfafa wa masu zuba jari gwiwa.
Ka binciki badakalar cuwa-cuwar  dala biliyan bakwai da aka yi a kamfanin mai na kasa (NNPC).
Abubuwan da za su karfafa mutuncin gwamnatinka
-Kada ka dauki masu sukar gwamnatinka a matsayin makiya.
-Ka rika bambancewa tsakanin sukar kwarai da sukar hassada.
-Ka rika yin hattara da irin shawarwarin da masu taimaka maka suke ba ka, domin wadansu suna kara maka makiya ne.
Abubuwan ban tsoro
-Ana zargin ka zana sunayen wadansu ‘yan siyasa dubu da za a sanya ido a kansu.
-Ana zargin kana horar da wadansu ‘yan ina-da-kisa a wani wuri da marigayi Abacha ya horar da irin wadannan mutanen.
-Masu zuba jari sun ja da baya daga Najeriya, sun zura ido suna sauraron abin da zai faru.

Ra’ayoyin jama’a kan wasikar Obasanjo ga Jonathan

Aminiya ta tuntubi wadansu mutane domin jin ta bakinsu game da badaddiyar wasika mai shafi 18 da Obasanjo ya aika wa Shugaba Jonathan, inda suka bayyana ra’ayoyinsu kamar haka:

Abubuwan da na sha fada ne Obasanjo ya tabbatar – Sheikh Jingir

Shugaban majalisar malamai na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, ya tattauna da wakilinmu Husaini Isah.  Kan wasikar da tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya rubuta wa shugaban kasa Goodluck Jonathan. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Aminiya: Mene ne malam zai ce dangane da wasikar da tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo  ya rubuta wa  shugaban kasa Goodluck Jonathan kan cewa yana kokarin wargaza Nijeriya a makon da ya gabata?
Sheikh Jingir: Wato abin da zan ce kan wannan magana shi ne, ita gaskiya ko da ka fade ta ka sha wuya, yau da gobe za ta fito fili kowa ya ji, kowa ya sani. Ni din nan idan ka lura da wa’azozina tun kafin a yi zabe na yi ta kira kan a yi hankali da shugaban kasa mai bakwala domin ya kulla mugunta iri-iri. Da yake da hausa nake fada masu jin harshen sun san wanda da nake nufi.
Ana nan, ana nan, sai aka ce mai bakwalar ya yi dashe ya sanya wa yaronsa bodilan. Ka san an ce fike kafi kaya tsini, wanda aka fike sai ya soki mai kafa shi, da ya ji zafi sai ya zo yana bayanin cewa wannan dan banza ne, macuci ne, yana yuukurin rushe kasa. Yana aza wutar kabilancin Arewa
da Kudu da kabilancin addini tsakanin musulmi da kiristoci.
To ka ga a nan sai mu ce gaskiya ta yi halinta, ni na ji dadi da wannan abu da ya faru, domin maganar da na yi shekaru 10 da suka gabata, yau gashi ta bayyana. Saboda haka na ji dadi da wannan gaskiya ta bayyana.
Aminiya: To, yanzu ina kake ganin kasar nan ta dosa ke nan?
Sheikh Jingir: To, abin da nake gani shi ne, kasar na ta doshi kwazazabon hallaka. Don haka ina kira  ga wadanda suka kitsa wannan abu, idan mutum da shi shugaban kasa ne, ko mutum da gwamna ne, duk a dawo a tuba. Kamar yadda wannan ya fito ya yi wannan Magana, a fito baki daya a taru a magance wannan matsala.
Aminiya:  Misali idan PDP ta sake tsayar da shugaban kasa Goodluck Jonathan takarar shugaban kasa a zaben shekara ta 2015 ko kungiyar izala za ta goyi bayansa?
Sheikh Jingir: To, ai  mu kungiyar Izala babu ruwanmu da sunan jam’iyya, mu abin da ya dame mu shi ne ina mutumin kirki  nagari yake mu zaba? Don haka mu babu ruwanmu da sunan jam’iyya, mu damuwarmu it ace mu samu mutumin kirki.
Aminiya:  Saboda haka kun yi hanun riga da  Goodluck Jonathan  ke nan?
Sheikh Jingir:  Ni dai cewa na yi ina mutumin kirki yake.  Don haka ni ba ni da wani  mutum da nake fada da shi da sunansa, ina fada ne da mai laifi. Idan mutum ya fito a layin masu laifi to abokin fada ne, idan mutum ya fito a layin mutanen kirki to abokin shiri na ne.
Aminiya: Ina aka kwana kan shirin da wannan kungiya take yi na bude jami’a?
Sheikh Jingir: Wallahi muna nan muna samun cigaba kan wannan shiri na bude jami’a. Tuni mun riga mun samu fili mun  fara gina ofishin gudanarwa na wannan jami’a. Kuma mun tura takadar neman bude manyan makarantun kwalejojin ilmi, su ma an ba mu izinin budewa. Don haka a taya mu addu’a.
Aminiya: Mene ne gaskiyar maganar da ake yi cewa wannan kungiya tana kokarin bude gidan rediyo?
Sheikh Jingir:  Wannan magana gaskiya ce, wannan kungiya tana kokarin bude gidan rediyo. Har ma mun sanya wa gidan rediyon suna Al-irshad. Mun rubuta takarda neman izinin bude wannan gidan rediyo mun aika Corporate affairs kuma an ba mu izini. Don haka in Allah Ya yarda nan ba da dadewa ba za mu bude wannan gidan rediyo.

Obasanjo ya wanke kansa  -Ahmad Gumi

Daga Muhammad Yaba, Kaduna
Shaikh Ahmad Abubakar Gumi kuwa cewa ya yi Obasanjo ya wanke hannunsa daga jinin bayin Allah da ake zubarwa a kasar nan. Ya kuma yaba wa tsohon shugaban a kan dauriyar da ya nuna har ya aika wa Jonthan da wannan wasika.
Shaikh Gumi ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da kafar yada labarai ta Sahara reporters a karshen makon nan.
“ Obasanjo ya wanke hannunsa daga jinin bayin Allah saboda tashi tsaye da ya yi wajen bayyana kurakuran wannan gwamnati mai ci,” inji shi.
Gumi ya ce,  “ Na so dukkan tsofaffin janarorin da ke boye a manyan gidanjensu su fito su yi magana a kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya, amma ba su yi ba. Domin haka ina yaba wa wannan mutum, kuma a shirye nake da in yafe masa abin da ya yi wa Najeriya,” inji Ahmad Gumi.
Da tunatar das hi cewa a lokacin mulkin Obasanjo ma akwai cin hanci da rashawa, sai ya ce,  “ Akwai rashawa kwarai, amma Obasanjo ba ya yi haka domin raba Najeriya ba. Ya yi ne domin taimakon kansa da kuma abokansa.”
Dangane kuma da dora wa marigayi Umaru Yar’adua da Obasanjo ya yi ga ‘yan Najeriya kuwa, sai  Ahmad Gumi ya ce,”Abin da Obasanjo ya yi shi ne ya nuwa cewa duk wani mutum daga ko wace kabila na iya zama shugaban kasa. Obasanjo wanda ya yi yakin basasa a kasar nan, manufarsa ba ta raba Najeriya ba ce,” inji shi.
Gumi ya kuma zargi Shugaba Jonathan da rashin yin kokari wajen yakar cin hanci da rashawa da kuma nuna halin ko-in-kula wajen magance matsalar rashin tsaro a arewacin kasar nan.
 “ Ta ya ya za’a ce majalisa ta bincike minista a kan rashawa kuma ta samu ministan da laifi amma kuma a ce wai Shugaban kasa ya kasa daukar wani mataki?”
Haka kuma ya kuma zargi shugaba Jonathan da fakewa da rikicin Boko Haram domin azabtar da ‘yan Najeriya. Domin a cewarsa, mafi yawan bama-baman da ke tashi a arewacin kasar nan da ake zargin ‘yan Boko Haram da yi, jami’an tsaro ne suke saka su.
 “Yan Boko Haram mutane ne ‘yan yankin Arewa maso gabas, idan suna son fada da Shugaban kasa saboda shi dan kudu ne ko kirista ai jahohin kudu za su je suna fada da shi. Babu yadda za a yi su rika tada bama- bamai a jaharsu,” inji shi.
A ganinsa, shugaba Jonathan ya fito ne daga wani bangare na kasar nan da ke da burin ballewa daga Najeriya. Ya ce, ‘’kamata a cikin abubuwa uku Jonathan ya zabi daya, ko dai ya sauka cikin mutunci ko a tsige shi ko kuma ya kwashi kunya idan ya tsaya takara a zaben 2015. Zabi na farko ya kamata ya dauka.’’

‘’Obasanjo ya fadi gaskiya’’

Sani Gazas Chinade  Daga Damaturu
An bayyana  cewa duk maganganun da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya fada wa shugaba Jonathan da gwamnatinsa a wasikar da ya aika masa gaskiya ne, kasancewar shi ubangida ne a gare shi, da ya yi uwa, ya yi makarbiya dangane da zamansa shugaban kasa.  
Shugaban hukumar wasanni na jahar Yobe kuma jigo a jam’iyyar APC  Alhaji Muhammad Sani Fema ne ya bayyana haka a tattaunawarsa da Aminiya a garin Damaturu.    
Ya kara da cewa, duk ma’abucin gaskiya in dai Allah ya ke nufi ya san cewa duk abubuwan da tsohon shugaba Obasanjo ya fada a kan shugaban kasa Jonathan babu karya ko kazafi a ciki, kasancewar babu abin da ya fada wadda ba ya faruwa dangane da mulkin na Jonathan.  
Alhaji Sani Fema ya ci gaba da cewa, duk wani dan kasar nan ya san cewa shugaba jonathan ya fi maida da hankalinsa ta fuskar gudanar da ayyukan raya kasa da abin da nada mafi yawan manyan masu rike da madafun gwamnati ga sashen da ya fito, watau yankin Naija Delta, wanda hakan ba daidai ba ne a ce shugaba ya dauki wannan matsayi.  
A cewarsa, idan an duba zargin da Obasanjo ya yi na cewa shugaba Jonathan na rura wutar rikicin addini, inda har ya mayar da shugaban kungiyar kiristoci ta kasa (CAN) a matsayin babban mashawarcinsa a boye, abin ban takaici ne a samu shugaba da ke  yin haka a hamshakiyar kasa irin Najeriya mai dauke da mabiya addinai daban-dabam.
Ya kuma zargi gwamnatin Jonathan dangane da yadda ta mayar da yankin arewacin kasar nan, musamman jahohin Yobe da Borno, tamkar ‘ya’yan bora, inda aka maida jahohin a baya dangane da harkokin ci gaba, da kuma barin jahohin suna fuskantar barazanar tabarbarewar harkokin tsaro, wanda al’ummomin jahohin ba za su taba yafe wa wannan gwamnati ba, kasancewar an zubar da jinin al’ummominsu da yawan gaske da kuma barnata dukan tattalin arzikin yankin.

‘Ayoyin shedan ne Obasanjo ya rubuta’
Daga Abbas Jimoh da Balarabe Ladan a Abuja
Shugabannin wadansu kungiyoyi masu zaman kansu, watau PDP Reload da Arise Nigeria, Cif Richard Laman da Jasper Johnson kira suka yi ga jami’an tsaro su kama Obasanjo su tuhume shi, saboda irin wannan wasikar da ya rubuta a zamanin Shagari ne ta jawo juyin mulki a shekarar 1984.
Bakin shugabannin biyu ya zo daya, inda suka bayyana wasikar da Obasanjo ya rubuta da cewa, ‘ayoyin shedan ne.’
A cewarsu,‘’Zarge-zargen da Obasanjo ya yi za su tayar da hankali ne kawai tare da gurgunta mulkin demokaradiyya, domin muna tune da yadda irin wadannan ayoyin shedan din da Obasanjo ya rubuta wa Shugaba Shagari suka jawo juyin mulki, kuma ya yi sa-in-sa da Babangida, ya saba da Abacha, har gwamnatin Abacha ta zarge shi da laifin yunkurin kifar da gwamnati.’’
A ganinsu, gwamnatin Jonathan ta yi kokari wajen sayar da bangaren wutar lantarki domin bunkasa harkar tattalin arzikin kasar nan, kuma ta yi haka ne ta hanyar amfani da kasa da daya bisa uku na dala biliyan 16 da gwamnatin Obasanjo ta kashe a kan wannan harkar amma babu wani abun a-zo-a-gani da ta yi.
Haka kuma sun bukaci jami’an tsaro su tuhumi Obasanjo ya bayyana sansanin da ake horar da ‘yan ina-da-kisan da ya ce ana y,i da kuma inda ya ga sunayen mutanen da aka rubuta domin a halaka su.