Wasikar Obasanjo: Gaskiya ya fada ko cin fuska ga Jonathan? 2
Wasikar nan da tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya rubuta wa Shugaba Goodluck Jonathan ta tada kura a kasar nan. Kalaman da wasikar ke dauke da su sun ja hankalin al’ummar kasa. Abin tambaya a nan shi ne, shin kalaman na Obasanjo gaskiya ne ko kuwa ya yi su ne da nufin cin fuska ga Jonathan? […]
Wasikar nan da tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya rubuta wa Shugaba Goodluck Jonathan ta tada kura a kasar nan. Kalaman da wasikar ke dauke da su sun ja hankalin al’ummar kasa. Abin tambaya a nan shi ne, shin kalaman na Obasanjo gaskiya ne ko kuwa ya yi su ne da nufin cin fuska ga Jonathan? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu kamar haka:
Wata dabarar siyasa ce – Muhammadu Sani
Muhammadu Sani: “Ni abin da na fahimta a ciki, akwai dabaru irin na siyasa kuma da shi Olusegun Obasanjo da yaron gidansa Goodlock Jonathan din, alhakin mutane ne ya fara kama su. Dalilina kuwa shi ne, idan aka duba wane ne ya yi kutu-kutun dora shi Jonathan a kan wannan mukamin bayan rasuwar Umaru Musa ’Yar’adua? Don haka a nan ba wani abu ne da za a fassara shi da wai musgunawaba, a’a; sun san abin da suka shirya kuma suka kulla da dadewa, sai dai kawai da yake yana ganin kamar shi Jonathan din ya yi watsi da shi.