Wasikar Obasanjo: Gaskiya ya fada ko cin fuska ga Jonathan? 6

Wasikar nan da tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya rubuta wa Shugaba Goodluck Jonathan ta tada kura a kasar nan. Kalaman da wasikar ke dauke da su sun ja hankalin al’ummar kasa. Abin tambaya a nan shi ne, shin kalaman na Obasanjo gaskiya ne ko kuwa ya yi su ne da nufin cin fuska ga Jonathan? […]

Wasikar Obasanjo: Gaskiya ya fada ko cin fuska ga Jonathan? 6
Wasikar Obasanjo: Gaskiya ya fada ko cin fuska ga Jonathan? 6

Wasikar nan da tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya rubuta wa Shugaba Goodluck Jonathan ta tada kura a kasar nan. Kalaman da wasikar ke dauke da su sun ja hankalin al’ummar kasa. Abin tambaya a nan shi ne, shin kalaman na Obasanjo gaskiya ne ko kuwa ya yi su ne da nufin cin fuska ga Jonathan? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu kamar haka:

Gaskiya ya fada wa Jonathan – Ibrahim Abdullahi
Ibrahim Abdullahi Maigoro: “Abin da nake gani, koda akwai gaskiya da wasikar ta kunsa ko akasin hakan, to za a iya cewa gaskiyar Obasanjo a kan abubuwan da ya zana wa yaron gidansa, din domin abubuwa ne da suke ci gaba da faruwa a cikin gwamnatinsa amma shi Jonathan din sai yana kauda fuska tare da nuna ba wannan ce damuwarsa ba kuma ba shi ne yake a gabansa ba. Dalili kuwa, idan aka duba shi fa Jonathan abin da ya sa a gaba shi ne tara abin duniya da shi da mukarrabansa da daure wa cin hanci da rashawa gindin zama da neman jefa kasa cikin halin ni-’ya-su ko raba kasar zuwa bangare biyu.