Wasikar Obasanjo kiyayya ce zalla

Ina so in yi amfani da  wannan dama in bayyana ra’ayina game da ire-iren budaddun wasiku da tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo ke rubuta wa Shugaban Kasa na Muhammadu Buhari a-kai-a-kai. Da farko ina so in bayyana wa duniya cewa wadannan wasiku nasa ba komai ba ne fa ce kiyayya ce karara da yake […]

Wasikar Obasanjo kiyayya ce zalla

Olusegun Obasanjo, Tsohon shugaban Kasar Najeriya

Ina so in yi amfani da  wannan dama in bayyana ra’ayina game da ire-iren budaddun wasiku da tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo ke rubuta wa Shugaban Kasa na Muhammadu Buhari a-kai-a-kai.

Da farko ina so in bayyana wa duniya cewa wadannan wasiku nasa ba komai ba ne fa ce kiyayya ce karara da yake nuna wa Shugaba Muhammadu Buhari da yankin Arewa da al’ummarta baki daya. Kamar yadda kowa ya sani ne kowace kasa tana da nata ire-iren kalubalen tsaro da take fuskanta. Haka ma ita Najeriya tana da nata kuma tarihi ya nuna ba an fara fuskantar wadannan kalubalen tsaro a lokacin mulkin Shugaba Buhari ba ne. Za a iya cewa dukkan gwamnatocin da suka shude sun fuskanci kalubalen tsaro daban-daban. Amma sai ya kasance Obasanjo yana ci gaba da sukar gwamnatin Buhari ta wannan fanni ba gaira ba dalili.

Batun Fulani makiyaya kuma da Obasanjo ke nuna musu kiyayya, kada ya manta cewa su ma ’yan Najeriya ne da ke da damar zama a duk inda suka ga dama kuma kada ya manta cewa har yanzu daga nan Arewa ake kwaso shanu da sauran dabbobi zuwa can Kudu da kewayenta. Kuma ina so in yi amfani da damar nan in ja hankalin shugabanninmu na Arewa cewa lokaci ya yi da ya kamata a ce mun gano kura-kuranmu mu fara neman mafita musamman na watsi da muka yi a kan ilimin ’ya’yanmu da sauransu.

Sanin kowa ne cewa Allah Ya albarkace mu da ma’adinai da sauran abubuwan raya kasa da dama a nan Arewa. Misali a fannin noma kasancewa ni babban manomi ne kuma shugaban manoma na san irin albarkar da Allah Ya ba mu a Arewa a fannin noma. Yau kusan duk abin da muka shuka a gonakinmu yana yin albarka. Ba kamar yadda lamarin yake a Kudancin kasar nan da sauransu ba inda ba komai ake iya shukawa ya yi albarka ba. Amma abin bakin ciki sai ya kasance saboda sakaci da shugabanninmu na Arewa ke nuna wa wannan fanni na noma ya sa wadannan ’yan Kudu da sauran sassan kasar nan ke yi mana kallon raini har suke ganin ba za mu iya dogara da kanmu ba sai da gudumawarsu.

Kuma har ila yau wani abin farin ciki shi ne yadda ake ci gaba da gano wasu rijiyoyin mai a Arewacin kasar nan. Amma abin tambaya shi ne ana mai da fifiko wajen habaka irin wadannan albarkatun kasa da ake ganowa a sashinmu? Saboda haka ina so in yi amfani da damar nan in nanata kirana ga shugabanninmu da masu hannu da shuni da sauran al’ummar Arewacin kasar nan baki daya cewa lokaci ya yi da dole mu yi watsi da bambance-bambancen siyasa da na addini da na kabilanci da sauransu, mu zo mu hada kai mu nemi mafita daga wadannan matsaloli da suke tare da mu da kuma irin sharrin da ’yan Kudu da wadansu shugabannin kasar nan na da da na yanzu ke yi mana.

Kuma kada mu manta cewa tun suna yi boye yanzu a fili wadannan ’yan Kudu da Obasanjo suke nuna mana kiyayyar. Na bayyana haka ne saboda idan aka yi la’akari da yadda suka fito fili suka nuna adawarsu da wannan shiri na gina Ruga na zamani da Gwamnatin Tarayya ta Buhari ta shirya don tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a tsakanin al’ummar kasar nan musamman tsakanin manoma da makiyaya. Na tabbata Gwamnatin Tarayya ta fito da shirin ne ba don nuna bangaranci ko wani abu makamancin haka ba. Amma saboda adawa da ’yan Kudu ke nuna wa gwamnatinsa da Arewacin kasar nan sai suka rika sukar shirin cewa wani shiri ne na musamman don fifita Fulani a kan sauran kabilun kasar nan. Kuma Allah na tuba idan aka ci gaba da samun wadannan tashin-tashina a tsakanin Fulani makiyaya da manoma a kasar nan sakamakon kin amincewa da shirin su ’yan Kudun ne za su fara fitowa suna sukar gwamnatin Buhari a kan matsalar. Saboda haka kamar yadda na bayyana a baya yanzu ya zame wa mu ’yan Arewacin kasar nan dole mu hadu mu hada kai mu tunkari wannan lamari.

Dole mu magance matsalolinmu na cikin gida musamman a bangaren samar wa ’ya’yanmu ingantaccen ilimi sannan mu farfado da fannin nomanmu wanda Allah Ya albarkace mu da shi da sauran bangarori da muke fuskantar matsalolin da ke barazana ga ci gaban yankinmu. Idan muka yi  haka ba shakka na tabbata su ’yan Kudu da sauran masu yi mana adawa irin su Obasanjo za su fahimci cewa lallai zai yi musu wuya su raba mu ko ta wane fanni don cimma mummunar manufarsu.

Alhaji Usman Adamu da aka fi sani da Doya Hamsin ya rubuto daga Agyaragu Hedkwatar Jankwe da ke Karamar Hukumar Obi a Jihar Nasarawa.

08065224270