Wasikar Obasanjo: SERAP ta nemi Majalisar dinkin Duniya ta matsa wa Jonathan ya dakatar da horar da makasa
kungiyar Kare Hakkin Rayuwa da na Tattalin Arziki da Tabbatar da Rikon Amana (SERAP) ta aika da kuka ga wakilin Majalisar dinkin Duniya kan yaki da kisan gilla da kashe mutane gabannin shari’a, Farfesa Christof HEYNS tana neman ya “nemi gwamnatin Najeriya ta dakatar da duk wani horar da makasa domin dalilin siyasa da ake […]
kungiyar Kare Hakkin Rayuwa da na Tattalin Arziki da Tabbatar da Rikon Amana (SERAP) ta aika da kuka ga wakilin Majalisar dinkin Duniya kan yaki da kisan gilla da kashe mutane gabannin shari’a, Farfesa Christof HEYNS tana neman ya “nemi gwamnatin Najeriya ta dakatar da duk wani horar da makasa domin dalilin siyasa da ake zarginta.”
Wasikar ta SERAP ta biyo bayan zargin da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi ne a makon jiya inda ya zargi Shugaba Jonathan da “horar da makasa da sauran masu dauke da makamai a boye tare da sayo makamai domin cimma burin a siyasa irin na Abacha, tare da horar da su a inda Abacha ya horar da nasa makasan.”
kungiyar ta bukaci a gudanar da bincike kan zargin kuma duk wanda aka samu da hannu a gurfanar da shi a gaban shari’a.
Takardar dauke da sanya hannun Babban Daraktan SERAP, Adetokunbo Mumuni ta ce, “Mun yi matukar damuwa kan zargin, idan gaskiya ne wannan babban keta dokokin duniya ne, kuma kai-tsaye sakaci ne da nauyin da ke gwamnati na kare rayuka da dukiyar jama’ar kasa. Kuma hakan cin fuska ne ga bin doka da oda tare da kauce wa tsarin dimokuradiyya da Najeriya ke kokarin bi.”
kungiyar ta ce, wajibi ne a kan gwamnati ta kare daukacin ’yan kasarta da sauran mazauna kasar nan daga duk wani ke hakkin dan Adam. Ta kare ’yancin rayuwa kamar yadda duniya ta amince a matsayin babban ’yanci. Domin haka horar da makasa zai iya jawo guguwar rashin tsaro tare da haifar da kin bin doka da oda.
kungiyar ta ce Najeriya ta sanya hannu kan yarjejeniya da dokokin kasa da kasa kan ’yancin jama’a da na siyasa, “don haka bai halatta a kashe wani rai haka siddan ba,” domin wajibi ne a kare wannan rai koda a karkashin dokar ta-baci ne inji kungiyar.
Domin haka sai kungiyar ta bukaci wakilin na musamman ya gudanar da binciken kwakwaf kan zargin tare da neman gwamnatin Najeriya ta dakatar da horar da makasan da sauran masu dauke da makamai, domin ci gaba da hakan zai iya illa ga tsaron ’yanci da rayuwar jama’a da sauran hakkokin dan Adam.