Wasikar Wada Nas ga Shugaba Muhammadu Buhari
Amincin Allah ya tabbata a gare ka, Allah seni! Muhammadu, Allah reni! Lekki(Gamji) kamar yadda mahaifiyarka take maka kirari da wannan suna na jarumta da karfin hali. Halinka sabulun wankan ka! Gaskiya jarin nagari na kowa. Alhamdullahi! Gaskiya da nagarta sun yi rana. Allah ya kara lafiya da taimako. Ya zama wajibi na fara da […]
Amincin Allah ya tabbata a gare ka, Allah seni! Muhammadu, Allah reni! Lekki(Gamji) kamar yadda mahaifiyarka take maka kirari da wannan suna na jarumta da karfin hali. Halinka sabulun wankan ka! Gaskiya jarin nagari na kowa. Alhamdullahi! Gaskiya da nagarta sun yi rana. Allah ya kara lafiya da taimako. Ya zama wajibi na fara da yi wa Allah godiya da ya kawo wa wannan al’umma dauki daga halin da kuka samu kanku a ciki. Bayan tsawon lokacin da aka yi ana bautar da al’umma da sunan ’yanci ko walwala. Yau ka zama Shugaban kasar Najeriya cikin yardar Allah da rahamarsa, ba don kana da dumbin dukiya ba, ko tarin gidaje, a’a sai don kokkrinka na kwatanta gaskiya da adalci. Tabbas wannan ya isa izna ga masu hankali da imani.
Kamar yadda Injiniya Ghali Sule Shugaba Rogo kan shaida min bayan barinku da na yi, yadda makiya talaka, mazambata, ‘yan wawa, ‘yan idan ba mu ba kowa ya rasa suka yi duk mai yiwu wa amma Allah ya kunya ta su. Janar wannan lamari babu abin da zance sai Alhamdullahi. Na hango halin da kannena suka dosa don saka yankin namu da ma kasar baki daya cikin bauta da kaskanci.
Na sani kana sane da lokacin da na same ka a Daura da Kaduna na roke ka ka shigo fagen siyasa don ganin ba a shiga halin da kuke ciki ba a yau na rashin tabbas,.Bakin talauci da rashin aikin yi, ga rashin tsaro da lalacewar al’amura. Kai daga labaran da nake samu suna nuna cewar komai ya lalace, ya tabarbare kai wani ma cewa ya yi da ni ana yin duk abin ba zai yiwu ba a ko’ina a duniya na karya doka ko cin amanar talaka da masu mulki ke yi. Wannan lamari ne mai ta da hankali. Da wannan ne nake ganin ya zame min dole na ja hankalinka a kan wasu abubuwa da suka zama wajibi ka sa ido a kansu.
Kamar yadda kowa ya sani ne an yi mana nisa ta fanon da dama a kasar nan.
Janar zan fara da bayyana maka irin alfarmar da Allah ya yi maka da daukaka wadda ba kowa ke samu ba, Allah ya daukaka ta hanyar saka soyayya a zukatan mutanen kirki ba don kana ba su komai ba, sai don kyawawan halayenka na rashin zarmiyya da babakere, haka da tarbiyya ta mutunta duk dan Adam. Sannan kai kadai Allah ya yi wa alfarmar da ‘yan siyasa suke cin zabe da kai ba don karfin mulki ba sai don wadannan halayen da na lissafa a baya cikin ‘yan siyasar wannan zamani. Kuma kai kadai ka yi takara a wannan lokacin da talakawa ke daukar nauyinka don gudanar da harkokinka na siyasa da rayuwa, sabanin yadda wadancan ke yi inda suke bin mutane gidajensu suna kai musu kudin da suka sace don wai suce mutanen kirki ne. Ai ka ga bambancin a bayyane yake. Wannan nagartar taka ita ce take firgita maciya amana da ‘yan barandansu .Ai ka ga yadda suka yi ta yi maka abubuwan da suna ganin suna bata ka amma sun kasa gane cewar kara maka tagomashi suke yi. Wannan ne ya sa duk takarar da ka yi talakawa suke tare da kai. Dubi yadda suka yi maka ruwan kuru’u har na 15,424,921 don kawai sun yarda da amanarka da fatan kowa ya smau daidaito da karamci. Duk da na san akwai wadanda sun aminta a sace kudin al’umma shi ne siyasa ko ma wayewa suma suna nan sun kada wa kungiyar ‘yan ta ragargaje kuru’unsu.
Hmm! Kar na manta, Malam Aminu Kano ya ce ka shaida wa mutanen Kano cewar yana yi musu fatan alhairi don ya samu labarin irin halin wayewar da suka nuna ta cewa da makiyya talaka sun ki wayon! Sun gaji inda suka ba ka kuria’a kusan milliyan biyu 1,903,999. Kuma ya kara da cewa burinsa ya cika na ganin jihar Kano ta fada hannun ’yan NEPU na gaskiya masu karrama talaka. Haka ya ce ka shaida wa mai martaba Sarkin Kano Muhammad Sunusi 11 cewar Malam Aminu yana taya shi murna da fatan Allah ya taya riko kuma ya ce a shaida wa Gwamna Rabiu Musa cewar lallai haka ya yi fatan ganin Kano kafin ya rasu. Sannan ya ce ka shaida musu duk inda suke su rika tuna cewar Nageria daya ce, amma kowa ya san gidan ubansa. Na san masu hikima za su gane abin da Malam Aminu yake nufi a nan, ba ma kawai mai martaba da mai girma gwamna Rabiu Musa Kwakwanso ba.
Dr. Chuba Okadibo da Cif Harry Mashal sun ce na shaida maka suna murna burinsu ya cika, sai dai sun ce na shaida maka dole ka yi amfani da ingantaccen tsari na nada makarranban gwamnati da za ka yi aiki da su. Dole ka nemi mutane masu amana, tsantseni, kamilallu da aiki tukuru don cimma burinka da manufofinka na saukakawa taalkan kasar nan halin da ya samu kansa a ciki. kanenka =Umaru Musa Yar’adua ya ce na shaida maka cewar karka manta da aikin yashe kogin Kwara da ginin matatar man fetur a Kogi da Zamfarad a baban titin mota daga Kano zuwa Sakkwato . Nemo da hako man fetur a Arewa, kare kwararowar Hamada a Arewacin Najeriya. Kau da masu tayar da kayar baya a Najeriya baki daya. Samar da kamfanin taki a Arewa, ka tabbatar da daidaito wajen daukar ma’aikata.
Janar dole na gaya maka wasu dabaru guda uku da nake son ka yi amfani da su wajen sake kafa harsashin sabuwar Najeriya. Ka na da tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya jagoranci kwato kudaden da mahandama suka kwashe a ko ina suke,ka ga abin mamaki. Biyu, ka nemo mai sharia Salami da ya jagoranci alkalan da za su rika yin shari’ar maha’inta. Uku ka jawo mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi da Shugabanci gyaran tattalin arzikin kasar nan.
Muhammadu ya zama wajibi ka sa dokar ta baci a hukomomi kamar haka, kamfanin wuta na kasa(NEPA), hukumar ’yansanda, ’yan sandan ciki.Kostom,hukumar kamfanonin mai ta kasa(NNPC), Kamfanin jiragen sama na kasa, Nitel, babban Bankin Najeriya, tashar jiragen ruwa ta kasa da kuma dukkan hukomin samar da kudin shiga na kasa.
Zan dakata a nan sai ka ji ni a sati mai zuwa in sha Allahu, inda zan zayyano maka wasu lamuran da za su taimake ka wajen gina sabuwar Najeriya. Haka ka nemi taimakon kamfani aikawa da sakonnin na Aminiyya don ka roke su da su kara fadakar da al’umma wajen yi maka addu’o’in neman taimakon Ubangiji a kan wannna nauyi da ke wuyanka.
Allah ya taimake ka a kan wannan Shugabanci, Allah ya zama mai taimakonka a dukkan matsaya da za ka dauka don taimakon jama’arka. Ya kara maka tsoronsa.
Nine naka
Ghali Sule Shugaba Rogo
29,Ajeboriogbon Street,
Papa-Uku, Agege, Lagos
Tel: 08023702045
Email: [email protected]