Wasiyyar Maitama Sule gare ni (I)

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!!!  Allah Ya jikan Alh Yusuf Maitama Sule, Ya gafarta masa. Ni, Abdulkarim dayyabu, Kani ne na Yusuf Maitama Sule (Danmasanin Kano), Mahaifiyarsa da mahaifiyata uwarsu daya, ubansu daya (wato First Cousins muke). Ba  kowane yasan hakan ba saboda shi (Maitama Sule) Mahaifinsa – mutumin Yola ne (Unguwar Madakin Kano), […]

Wasiyyar Maitama Sule gare ni (I)

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!!! 

Allah Ya jikan Alh Yusuf Maitama Sule, Ya gafarta masa. Ni, Abdulkarim dayyabu, Kani ne na Yusuf Maitama Sule (Danmasanin Kano), Mahaifiyarsa da mahaifiyata uwarsu daya, ubansu daya (wato First Cousins muke). Ba  kowane yasan hakan ba saboda shi (Maitama Sule) Mahaifinsa – mutumin Yola ne (Unguwar Madakin Kano), ni kuwa mahaifina mutumin Sharifai ne (Unguwar Dukawa) duk a birnin Kano. Dawakin Tofa ita ce tushen mutanen Yola, kamar yadda mahaifin  Marigayi Yusuf Maitama Sule shi ma dan asalin Dawakin Tofa ne, haka ita ma Halima (Aniya), wacce ta haifi mahaifiyar Maitama Sule da tawa mahaifiyar – ita ma ’yar asalin DawakinTofa ce, amma Mijinta Isyaku (Baban Doki), wanda ya haifi nMahaifiyar Maitama Sule da Mahaifiyata – haifaffen Garin kunchi ne. Mahaifin Yusuf Maitama Sule shi ne kusancinsa da Sarauta har Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na farko (Sunusi  Bayero) ya nada shi danmasanin Kano. Sunan mahaifiyar Maitama Sule Hauwa, shi ne dalilin da ya sanya wa babbar ’yarsa Hauwa (Kulu).

A cewarsa, ya saba da wan mahaifina “Alhaji Yakubi Dukawa” kafin ya san cewa Alhaji Yakubi Dukawa wan mahaifina ne (watakila tun kafin a haife ni). danmasanin Kano – Alhaji Yusuf Maitama Sule shi ne ya sanar da ni cewa dalilin abotar mahaifina (Alhaji dayyabu Ahmad) da Sarki Tsalha (dan Madaki Mamudu – wan Madaki Chigari), ya auri mahaifiyata (Rakiya Isyaku Yola). Lokacin da Sarki Tsalha ya rasu, Marigayi danmasanin Kano ya gaya wa ’ya’yan  Sarki Tsalha ko su ba za su ji zafin mutuwar mahaifinsu  kamar ni ba, Abdulkarim daiyabu. Tun ina yaro karami nake ganin Alhaji Sarki Tsalha kusan kullum a gidanmu, na yi tsammanin dan uwan mahaifina ne, ashe makaranta ce ta hada su da mahaifina – Daiyabu Ahmad ajinsu daya da Turaki Maje (wan Marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero). Shi Sarki Tsalha mahaifiyarsa ’Yar Sarki ce, Madaki ne mahaifinsa. Tun ina karami idan aka kawo ni Yola wurin kakannina na uwa na yi ’yan kwanaki, a kan ba ni akuya da agwagi da tattabaru idan za a mai da ni gidanmu. Daga baya na rika zuwa wajen kakannina da kaina, ana raka ni gidajen dangi na kusa da su.

Kasancewar mahaifiyar maitama Sule (Hauwa) tun yana karami kasa da shekara biyar ta  rasu, ba cin kanen Maitama da ta haifa ya rasu  tun yana jariri. Shi mahaifin Yusuf Maitama Sule ba ya bambanta ni da ’ya’yansa da ya haifa da uar mahaifiyar tawa da ta rasu da  sauran ’ya’yan kishiyoyinta. Su ma kishiyoyin mahaifiyar  Maitama Sule ba su taba nuna min bambanci da ’ya’yan da suka haifa ba. Har na yi abokai da muka zama tamkar ’yan uwa, irin su Mansur Baffa da Mahmud Baffa da Sayyadi Yola da Sani Inuwa Chedi, muka tare a gidan Malam Baffa Wakilin Biya, har muka  kai munzalin yin aure.

Lokacin da nake Makarantar Primary  (Kuka Primary), Maitama Sule ne ya je ya sanar da ni rasuwar kakarmu Halima (Aniya), wacce ta haifi mahaifiyarsa da  tawa. Da ma tuni kakanmu Isiyaku (Baban Doki) ya  riga Halima mutuwa tun ina karami kafin asa ni a makaranta.

Lokacin da Yusuf Maitama Sule yake  Minista a Legas, ya taba aiko mana tikitin jirgin kasa (2nd Class) mu uku, ni da Abdulkadir Sunusi dantata da kanensa Usman Sunusi dantata (Amaka), na zuwa da dawowa, sannan muna Kwalejin Horar da Malamai, an ba mu dogon hutu, muka yi wata guda a Legas ana zagayawa da mu muhimman wurare a Mercedes-Benz baka – ta ministoci. Lokacin da Maitama Sule ya zama Chief  Commissioner of Complains, muna tare sai ya rubuta wa AbM  Mukhtar Muhammad wasika, ya gabatar da ni cewa “ga dan uwanka nan ku yi zumunci.” Da na samo Turawa daga Jamus, wadanda za su yi aikin gina Abuja a lokacin Abubakar Koko ne Edecutibe Secretary, Abdullahi Ma’aji yana  Administratibe Secretary suka gayyacemu, har muka  zauna da wakilan gwamnati, aka yi musu cikakken bayanin kasashen da suka yi irin wannan aikin a Duniya, inda suka zo na daya, sai dai  lokacin mulkin soja ne, ya rage watanni a yi zaben 1979,  aikin kuma zai kai shekaru 15 ana yi. Hakan  ya sa aka jingine maganar aikin sai an kafa gwamnatin farar  hula. Ana dage takunkumin siyasa sai Chief Obafemi Awolowo ya ce “su idan sun ci zabe, a Legas za su zauna, ba za su koma Abuja ba.” Shehu Shagari kuwa ya ce da zarar sun ci zabe za su koma Abuja. Da aka yi zabe Alhaji Shehu Aliyu Shagari ya zama Shugaban kasa, sai ya ce “babu wanda za su bai wa kwangilar ginin Abuja sai dan NPN, wanda ya wahalta musu suka ci zabe.”  Duk da kasancewa Madakin Kano Shehu Ahmad da Maitama Sule danmasanin Kano sun tsaya mana da cewa mu ne muka fi cancanta da a bai wa wannan aikin, amma ba a ba mu ba, saboda Gwamnatin PRP a Jihar Kano ta nadani dan Kwamitin Mai Shari’a Layiola na Binciken rabon Fili, sannan an nada ni Darakta a Hukumar Raya Birni ( UDB wato KNUPDA), an sake  nada ni dan  kwamiti Gidan  Gwamnati  an kuma nada ni Darakta mai Wakiltar Kano a Hukumar NNDC Subsidiary Kaduna, duk Duniya ta ji, ta gani a rediyo da talabijin da jaridu, haka na hakura. 

Da aka nada Alhaji Yusuf Maitama Sule ya zama wakilin Najeriya a Majalisar dinkin Duniya, sai ya je wajen mahaifiyata ya fashe mata da kuka, wai an yi masa kurciya zai tafi Majalisar dinkin Duniya, yana yi mata sallama, sai ta aika aka kira ni ta ce da ni “dazun nan dan marayan Allah (wato Maitama Sule) ya tashi daga nan gabana  yana kuka wai an yi masa kurciya, don haka in je in nemo Nasiru Sule mu je mu raka shi Amurka (sai ka ce wata Unguwa ce).” Allah da ikonSa dukkan mu biyun sai da muka je NewYork wajensa. Ni, da azumi ma na je bacin an yi sunan dana (Yusuf) – mai sunansa, na tafi masa da naman suna (soyayye), Allah Ya sa otel din da aka sauke shi ni ma a nan na sauka, ana shan ruwa sai na kai masa  naman ya fara ci, sai sakatarensa Lawal Mukhtar shi ma ya  ci, koda Maitama Sule ya ga Lawal Mukhtar zai ci gaba da cin naman, sai ya doke hannunsa ya ce “don iyayenka ka daina cin nama haka, zai ba ta maka ciki, nima don na saba da shi ne,” ya kunshe namansa yakai daki ya boye.

Da aka yi juyin mulki yana zaune ba ya komai sai rigima, ta yau daban, ta gobe daban. Allah Ya sa yana da kyakkyawar zuciya, wadansu da ya taimakawa har ma da wadanda bai taimakawa ba, suka rika taimaka masa.

Da aka nada Muhammadu Buhari Shugaban Hukumar PTF, danmasanin Kano Alhaji Yusuf Maitama Sule ya aike ni wurin Muhammadu Buhari a kan yana so a bashi kwangila ta Naira Miliyan Dubu (#1bn), koda yake ba a sona Muhammadu Buhari ya karbi aikin na PTF ba, amma matsalar Alh Baballe Ila da Akkad ta sake hadani da Buhari, har ya yimin masauki kusan na dun-dun-dun a Guest House dinsa. Da na je wajen Buhari da sakon danmasanin Kano na neman Kwangilar Naira Biliyan daya, sai Buhari ya yi murmushi ya ce “zai gaya min sako in gaya wa danmasanin,” na ce in Allah Ya  yarda duk abin da ka gaya min, ni kuma zan gaya masa. Sai Muhammadu Buhari ya ce in gaya wa danmasani tun shi Buhari yana karami, ya san lokacin da Maitama Sule yake Minista ma’adanai da makamashi(Mines & Power), akwai lokacin da British Petroleum (BP) suka ba shi Chekue na Fam Miliyan Biyar (£5m) a Landan, yana sauka a Legas bai tsaya ko’ina ba sai wajen Firayiminista  (Sa Abubakar Tafawa balewa) ya kai masa Chekue din ya ce “ranka ya dade British Petroleum ne suka ba mu taimako.”