WASSCE: Dalibi mai COVID-19 zai rubuta jarabawa a makaranta
Wani dalibi daga cikin mutanen da aka killace saboda kamuwa da cutar COVID-19 zai rubuta jarabawar kammala sakandare (WASSCE) a farfajiyar makarantarsu. Zuwa yanzu babu cikakken bayani kan yadda zai rubuta jarabawar; na ko zai rubuta a ware ne, ko kuma tare da sauran dalibai. A shafin Twitter na Hukumar Kula da Lafiyar Al’umma da […]
Wani dalibi daga cikin mutanen da aka killace saboda kamuwa da cutar COVID-19 zai rubuta jarabawar kammala sakandare (WASSCE) a farfajiyar makarantarsu.
Zuwa yanzu babu cikakken bayani kan yadda zai rubuta jarabawar; na ko zai rubuta a ware ne, ko kuma tare da sauran dalibai.
A shafin Twitter na Hukumar Kula da Lafiyar Al’umma da Bayar da Taimakon Gaggawa ta Gombe, @GombePHEOC, an dauko dalibin ne daga inda aka ware wa masu fama da cutar cikin mortar daukar marasa lafiya.
Zai rubuta jarabawarsa ne ta biyu ta gwajin sinadarai (Chemistry practical) a makarantar sakandare ta kimiya da ke garin Gombe, (GSSS, Gombe).
An ce kuma za a kai shi ne dakin gwajin sinadarai na makarantar.