Wasu ɓarayin barasar Naira miliyan 3 sun shiga hannu a Ogun

Dubun wasu ɓarayin barasa ta cika a Jihar Ogun bayan da suka tare wata babbar motar tirela maƙare da barasa a kan hanyarta daga garin Ilesha zuwa Irabgiji a Jihar Osun, inda suka karkatar da motar barasan zuwa Jihar Ogun. A cewar mai magana da yawun rundunar ’yan sanda a Jihar Ogun ASP Abimbola Oyeyemi, […]

Wasu ɓarayin barasar Naira miliyan 3 sun shiga hannu a Ogun

Dubun wasu ɓarayin barasa ta cika a Jihar Ogun bayan da suka tare wata babbar motar tirela maƙare da barasa a kan hanyarta daga garin Ilesha zuwa Irabgiji a Jihar Osun, inda suka karkatar da motar barasan zuwa Jihar Ogun.

A cewar mai magana da yawun rundunar ’yan sanda a Jihar Ogun ASP Abimbola Oyeyemi, ’yan fashin su uku ɗauke da bindigogi ne suka yi fashin  motar mai ɗauke da bararsar Naira miliyan biyu da dubu ɗari bakwai da sha huɗu, inda na’ura mai kwalkwalwa da ke jikin motar ta nuna cewa suna yankin garin Shagamu. “Nan take babban jami’in ’yan sandan yankin, ACP Ibrahim Sa’ad Muhammad ya baza jami’ai a yankin, inda suka yi nasarar kame ɗaya daga cikin ’yan fashin, yayin da ragowar biyun suka tsere.” inji shi.

Rundunar ’yan sandan ta tasa ƙeyar ɗan fashin da aka kama mai suna Saheed Omotosho, inda ya kai su wajen matar da suka kai wa barasar mai suna Khadeejat Azeez, wacce ke da shagon sayar da barasa a Ode-Remo, inda aka gano barasar, aka kuma kame matar.

Kwamishinan ’yan sanda a Jihar Ogun, Ahmad Iliyasu ya ba da umarnin mika waɗanda ake zargin zuwa sashen kula da manyan laifuka na rundunar tare da baza ƙaimin kamo ragiwar ’yan fashin da suka gudu.