Wasu abubuwa da gayya ake yi don a tsokani ’yan Arewa – Aliyu Gebi

dan Majalisar Tarayya daga Mazabar Bauchi Alhaji Aliyu Ibrahim Gebi ya kira taron manema labarai a Bauchi inda ya nemi ’yan arewa su yi karatun ta natsu don fito da Arewa daga matsalolin da ta shiga: Daga Mu’azu Hardawa, Bauchi Aminiya: Wane abu ya tsaya maka a rai game da Najeriya, har ka kira taron […]

Wasu abubuwa da gayya ake yi don a tsokani ’yan Arewa – Aliyu Gebi

dan Majalisar Tarayya daga Mazabar Bauchi Alhaji Aliyu Ibrahim Gebi ya kira taron manema labarai a Bauchi inda ya nemi ’yan arewa su yi karatun ta natsu don fito da Arewa daga matsalolin da ta shiga:

Daga Mu’azu Hardawa, Bauchi

Aminiya: Wane abu ya tsaya maka a rai game da Najeriya, har ka kira taron manema labarai?
Gebi: Ina son jan hankalin masu mulki da masu hali ne kan su ji tausayin wadanda suke mulka su kwatanta adalci, kafin Allah Ya haramta mana zalunci sai da Ya haramta wa kanSa. Manzo Allah (SAW) ya hana mu zalunci kuma ya hana mu bari a zalunce mu, don haka kowa ya sani bayan harkar siyasa da ta rayuwa za mu koma ga Allah mu amsa tambayoyinSa. Idan hakkin mutane ya zamo kamar alfarma, to yaya za mu samu zaman lafiya? Tun daga farko ake magance komai, idan abu ya lalace aka nemi gyara ba zai gyaru ba. Kowa ya san kasar nan akwai matsala kuma mu ’yan Arewa dole mu tashi mu nemi mafita game da abin da ke damun Arewa. Kwanaki idan ka ga makudan kudin da aka yi kasafi aka turo mana don tura wa Kudu, yankin Shugaban kasa dole ka ce abin ana yi ne kurum don idan muna da abin yi mu yi, yau su ne da mulki. Duk da mun saba ganin kudi mai yawa a rubuce a takarda amma ba mu taba ganin irin na wannan karo ba, kai ka ce da gayya ake yi don a tsokani ’yan Arewa mu tanka a yi mana abin da ake so. Amma idan za su tura kudi yankin su to ina namu na Arewa ko mu ba Najeriya ba ne?
Aminiya:  To me kuka yi kan wannan kasafi da kuka ga an cuci Arewa?
Gebi: Mun ki amincewa. Mun kuma bukaci yadda aka kirkiro Ma’aikatar Raya Yankin Neja-Delta mu ma a kirkiro Ma’aikatar Bunkasa Arewa, saboda a halin yanzu mu Arewa mun fi zama abin tausayi a kan can. Idan da adalci ma’aikatar ci gaban shiyyar Arewa maso Gabas ya kamata a kirkiro saboda bala’in da wannan yanki ke ciki. Haka mun ce yadda ake kai ’yan ta’addan Neja-Delta kasashen waje don horon sana’a da karatun zamani, mu ma mutanenmu suna bukata, don haka muke nema idan mu ’yan adawa mun takalo rigimar sauran ’yan Arewa su goya mana baya su daina nuna tsoro, ba zai kai mu ko’ina ba.
Aminiya: Ana gani kamar ku ’yan adawa ne kuka fi himma kan wannan, ’yan PDP masu rinjaye ke taka muku birki ina gaskiyar lamarin?
Gebi: Yanzu muna samun karfin gwiwar magana saboda lamura sun fara sauyawa saboda zuwan APC da kuma ’yan sabuwar PDP da suka farke lemarta suke neman biyo mu, don haka muke samun karfin gwiwa. Kuma koda ba yawa idan mutane za su tsaya neman hakkin Arewa tsakani da Allah ba tsoro ba munafunci ba gudu, ba ja da baya dole abin da ke aukuwa ya sauya. Idan mutum ya yi haka ya fita hakkin mutanen da yake wakilta koda ba a yi abin da mutum ya nema dari bisa dari ba.
Aminiya:  Me za ka ce game da batun dokar ta bacin da aka tsawaita a jihohi uku na Arewa?
Gebi: Wannan wata dabara ce don a yi ta rudar mutane ana jan lokaci har lokacin zabe ya zo, inda ba wanda ya isa ya fita zuwa kamfe na neman goyon bayan jama’a ko ya fita don yin zabe. Ko idan lokacin zabe ya yi aka ce an ji labarin Boko Haram za su kawo hari ka ga sai komai ya lalace idan aka baza soja kamar yadda aka yi mana a shekarar 2011. Kuma an kawo takardar kammala wannan dokar ta-baci amma mun nemi wannan wata shida da aka yi a zo a nuna mana irin nasarorin da aka samu babu. Saboda cikin watanni shida watakila a wani kaulin kuma ana ganin an yi barnar da ta fi sauran dukkan shekarun da aka yi ana cikin wannan matsala a yankin. Kada a mance a nan Abuja aka kashe mutane tara namu, amma har yanzu muna ta jira rahoton ya fito shiru kake ji. Mun san idan ’yan ta’adda sun bulla a Kudanci ba a kiransu da wannan suna sai a ce matsafa, ’yan Neja-Delta su ma ba ’yan ta’adda ba ne masu neman hakki ne, namu ne ’yan ta’adda. Mun gani a Kudu sun fito sun kashe jami’an tsaro da sojoji amma ba abin da aka yi musu, ba a sa musu dokar ta-baci ba alhali sun kashe kusan mutum 100. Don haka kada mu yaudari juna, ko wannan taron kasa da aka kirkiro a matsayina na dan Najeriya duk ina daukarsa yaudara ce kurum.
Aminiya: Me za ka ce game da ’yan sabuwar PDP kana gani za su shigo cikinku?
Gebi: Ina ganin yaudara ce, in da za su shiga APC da sun shigo, saboda duk cikin manufofinsu ba su taba cewa suna yi don an zalunci talakawa ba ne ko don PDP ko Shugaban kasa sun zalunci Arewa ba. Wannan magana ce ta kowa ya kare kujerarsa, idan da an yi musu abin da suke so, talakawa ko oho. A tunanina kamata ya yi mu APC mu ja aji su yi begen shigowa cikinmu da kansu zai fi alheri.
Kuma taron kasa ba wani da mai ido da zai haifar illa barna kurum, kuma a sake gwara kawunanmu a hargitsamu mu yamutse saboda zabe ya yi kusa. Amma yanzu an ce su ne za su yi sannan a kawo mana mu kuma mu tattauna mu yi muhawara, wannan ya zama aikin banza. Ba wani abin da ya fi illa mu ’yan Arewa mu san ciwon kanmu mu yafi juna mu hada kai mu ceci kanmu, ba wani mai ceto mu sai mu da kanmu, saboda mun dauki kanmu mun ba wasu idan ana neman kuri’u sai a watsa mana ’yan kudi mu ci zarafin juna mu yi musu abin da suke so mu kasance cikin takaici. Saboda muna nuna mu ne ’yan akida mun dage wando mun tsaida gemu ba tare da duba irin tarkon da ake zuba mana ba.
Aminiya:  Ina matsayinka a siyasar 2015 zaka sake tsayawa takara?
Gebi: Ina ciki kamar yadda Namadi Sambo ke cewa daram damdam, ina cikin siyasa har sai ranar da mutanen Bauchi suka ce ba su sona. Na rantse da wanda raina ke hannunSa idan mutanen Bauchi suka fito suka ce ba sa sona shi ke nan wallahi ba zan nemi komai ba. Saboda Manzo (SAW) ya ce idan mutane suka ce ba sa son shugaba ya ki bari, to yana cikin halaka. Kuma ya ce idan aka dauki wanda mutane ba sa so aka tilasta shi kan mutane to a jira tashin hankali da wahala. Kafin na hau wannan kujera hankalina ya fi kwanciya saboda ban taba ganin matsala da wahala ba da munafunci sai da na hau wannan kujera. To na haune don cire kitse a wuta kamar yadda muke fada a CPC don mu bauta wa jama’a, don haka da kyar muna ja talakawa na ja muka tumbuke masu neman sake dawowa, mu ba ’ya’yan kowa ba Allah Ya kawo mu kujerar, kuma alfarmar mutane ta kawo mu. Don haka majalisa zan ci gaba da nema amma akwai wata kujerar da na ke hange idan mai ita ya fito ya nemi wata to ranar zan lika takardar neman waccan kujera.
Don haka don Allah mutane su zo mu hada hannu duk wanda ya yi min laifi na yafe, su ma su yafe min mu tashi mu nemo ’yancin Arewa a shekarar 2015. Idan ba mu tashi mun yi haka ba wallahi Arewa sai mun dawo muna gudun hijira zuwa Nijar ko Chadi, Allah Ya tsare, Ya sa mu hankalta mu nemi mafita.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50