Wasu abubuwa game da Sarki Sanusi II da suka tayar da kura

A safiyar yau, Litinin 9 ga Maris ce Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya amince Ce-ce-ku-ce kan Shari’ar Musulunci da tsige Sarkin Kano, Sarki Muhammadu Sanusi II. A takardar sanarwar tsigewar, gwamnatin ta ce ta tsige sarkin bisa kin bin dokokin gwamnatin jihar, wadanda suka hada kin halartar taruka ba tare da hujjoji ba. […]

Wasu abubuwa game da Sarki Sanusi II da suka tayar da kura

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II

A safiyar yau, Litinin 9 ga Maris ce Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya amince

Ce-ce-ku-ce kan Shari’ar Musulunci da tsige Sarkin Kano, Sarki Muhammadu Sanusi II.

A takardar sanarwar tsigewar, gwamnatin ta ce ta tsige sarkin bisa kin bin dokokin gwamnatin jihar, wadanda suka hada kin halartar taruka ba tare da hujjoji ba.

Sanarwar ta kara da cewa an tsige sarkin bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki, sannan da yin la’akari da bangare na 3 na sashe na 13 na Dokokin Masarautar Kano na shekarar 2019.

Sannan a karshe, takardar wadda Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji ya sanya wa hannu, ta ce an cire sarkin ne domin a kare mutunci da kimar Masarautar Kano.

Shi dai Sarki Muhammadu Sanusi II, an dade ana zarginsa da yin kalamai da suke tayar da kura.

Don haka ne Aminiya ta rairayo wasu daga cikin kamalan sarkin da suka tayar da kura a lokutan da suka gabata.

Zargin gwamnatin Jonathan da batar da Biliyoyin Naira

A zamanin mulkin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ne, Sarki Muhammadu Sanusi II, Lokacin yana Gwamnan Babban Bankin Najeriya, ya zargi Kamfanin NNPC da yin sama da fadi da Dala biliyan 20 na man fetur.

A cewarsa, Dala biliyan 20 din yana cikin Dala biliyan 67 da NNPC din ta samu tsakanin Jnairun 2012 zuwa Yunin 2013.

Sarki Sanusi ya bayyana hakan ne a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin Majalisar Tarayya.

Sannan ya ce idan ba a dauki mataki ba, tattalin arzikin Najeriya zai durkushe.

Kamfanin na NNPC ya musanta zargin a wancan lokacin.

A wancan lokacin, batun na Sanusi ya tayar da kura matuka, inda jim kadan bayan wannan lamarin, a ranar 20 ga watan Fabrairun 2014, tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya sauke shi daga Gwamnan Bankin.

A lokacin ya kalubalanci lamarin a kotu, inda daga baya ya samu nasara.

Batun aure da rashin tarbiyyar yara

A shekarar 2017, Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi yunkurin bijiro da dokar auratayya da tarbiyyar yara.

Ya ce dokar za ta taimaka wajen inganta zamnatakewr al’umma.

Ita ma wannan maganar ta tayar da kura matuka, inda wasu suke zargin sarkin cewa ’ya’ya ne ba ya so ana haifa.

A dokar akwai batun hana auran yara kanana da kuma batun haihuwar yaran da za a iya kula da tarbiyansu ba.

Zaben 2019

A zaben Gwamnan Jihar Kano na shekarar 2019, wasu musamman ’yan Jam’iyyar APC da bangaren gwamnatin jihar, sun zargi sarkin ne da cewa yana son abokan hamayyarsu ta PDP.

An dai ta yin tataburza daga zaben zuwa yau din nan da aka cire sarkin.

Idan ba a manta ba, a ranar 9 ga watan Maris ne aka yi zaben Gwamna, sannan kuma a ranar 9 ga watan ne aka cire sarkin.