Wasu abubuwan tunawa a rayuwar marigayi Sheikh Abubakar Gumi

Auwal G. danbarno (08064595353) ya yi nazari da tariyar rayuwar fitaccen malamin Musulunci, marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, inda ya ja hankalin al’umma game da wasu kyawawan halaye da dabi’u abin koyi daga rayuwar malamin. Ga abin da yake cewa: Duk lokacin da na karanta littafin tarihin Rayuwar Sheikh Abubakar Gumi, mai suna Where I […]

Wasu abubuwan tunawa a rayuwar marigayi Sheikh Abubakar Gumi
Wasu abubuwan tunawa a rayuwar marigayi Sheikh Abubakar Gumi

Auwal G. danbarno (08064595353) ya yi nazari da tariyar rayuwar fitaccen malamin Musulunci, marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, inda ya ja hankalin al’umma game da wasu kyawawan halaye da dabi’u abin koyi daga rayuwar malamin. Ga abin da yake cewa:

Duk lokacin da na karanta littafin tarihin Rayuwar Sheikh Abubakar Gumi, mai suna Where I Stand ko na Hausar shi mai suna Manufata, wanda Malam Isma’ila Tsiga ya rubuta; nakan tausaya wa Malam irin kwaramniyar da ya sha, musamman da yake shi ya bayar da labarin da kansa.
Malam Gumi ya yi rayuwa cikin tsantsani da gudun duniya. A tasowa ta, a zamanina, a iya sani na ban ga wani Malami da ya kai kololuwar daraja ta samun matsayi, wanda matsayin bai sa shi fankama da takama kamar Sheikh Abubakar Gumi ba. Wannan fahimtata ce, ta yiwu wani ya san wani Malamin da ya fi Gumi gudun duniya.
Da farko Malam ya zama mai ba da shawara bangaren addini ga Firimiyan Arewa. Malam ya taka matsayi na alkalanci har zuwa Alkalin-Alkalai na kasa, amma bai yi amfani da matsayinsa ya yi danniya ko bankiya ko tara abin duniya ba.
Malam Gumi ne Malamin da na sani duk abin da ya shigo hannunsa na kyauta daga masu kudi, zai rabar ba tare da ya shigar da ko kwaya gidansa ba.
Shi ne har ya bar duniya bai tara suturar da ta kai kala goma ba. Idan na ga yadda wasu malamai ke daukar hotuna su ba masu kalanda a buga a yada, nakan tuna da Sheikh Gumi.
Abin da ya faru kwanan nan, wanda aka yanke wa tsinannu, wadanda suka yi batanci ga fiyayyen halitta, Manzon Allah (saw) hukuncin kisa, idan ban manta ba Malam Gumi ya taba gargadin cewa hakan za ta iya faruwa. A littafin ya yi magana kan akidu, illolinsu da kuma abin da zai je ya zo da abubuwan da za su haifar; ya yi magana kan fa’idojin wasu akidun.
Wani abin dubawa da lura ga rayuwar marigayin shi ne, yadda ya tafiyar da rayuwarsa ga tsantsan hakuri da gudun duniya. Misali, an sha Malam na karatu a zo a kafirta shi. Abin da kawai zai yi shi ne ya yi sabuwar Kalmar Shahada a gaban wanda ya kafirta shin. Kawai kuma sai a ci gaba da karatu. Yana karatu an sha a zo kai tsaye a zage shi, shi da almajiransa na lokacin babu mai tankawa. Ka kwatanta Malamanmu na yanzu, ka je gabansu ka yi musu irin yadda aka yi wa Gumi, wallahi wasu daliban sai sun yi wa mutum dukan kawo-wuka a gaban malamin kuma ba zai tanka ba.
Wani abu da na san Malamai suna yi na fifita ’ya’yansu da jikokinsu ya zama kamar ana yi musu bauta. Ka ji ana kiran ’ya’yansu Sayyid wane ko Sayyada wance. Sheikh Abubuakar Gumi bai tarbiyyantar da dalibansa da ’ya’yansa su zamo irin wannan ba. Abin da kawai ya yi, ya ba ’ya’yansa ilmi kamar yadda ya ba almajiransa – sabanin yadda muka ga wasu na ba yaransu wani matsayi na musamman, almajiransu kuma su zamo kamar bayinsu. A zamanin rayuwar Gumi, duk na kusa da shi babu wanda bai kudance ya fi shi ba, domin duk abin da ya shigo hannunsa na game da sadaka ko zakka ko taimako, su yake ba. Sabanin yadda yau malamai ke karbe duk wata zakka da sadaka ko da sun fi karfinta, idan kuma za su bayar to fa sai dai su ba ’ya’yansu da jikokinsu.
Sheikh Gumi bai tara manya-manyan motoci ba, kamar yadda muke gani yanzu ga wasu malamai. Motocinsa ba su wuce biyu zuwa uku ba. Akwai motarsa ta ofis, wadda a ka’ida duk Alkali ana ba shi ita, akwai kuma mota ta zirga-zirgar gida da kai yara makaranta, wadda ita ma duk alkali na da ita, wadda gwamnati ke ba shi.
Da wuya ka ji Malam Gumi ya yi cin fuska ga wani, sai wanda karatu ya biyo ta kansa, da wuya ka ji yana mayar da martanin nan irin na Malamai, sai wanda karatu ya biyo ta kansa.
Wata tarbiyya da ya bari ga almajiransa ita ce, duk abin da ya fadi ba daidai ba suna da damar gyarawa. Tun yana raye haka yake, ba laifi ga duk wani almajirinsa da ya tayar da shi ko ya gyara masa wata fatwah da ya yi ba daidai ba.
Ya Allah muna tawassuli da kyawawan ayyukanmu, Allah Ka kai Rahama kabarin Sheikh Abubakar Gumi. Ya Allah ka yafe masa zunubbansa da ya yi bisa kure ko da gangan a matsayinsa na dan Adam mai laifi mai kuskure.