Bata-gari sun kona motoci a tashar Oyinbo

Wasu gungun bata-gari sun cinna wa motoci kusan 30 wuta a tashar mota ta Oyinbo a Jihar Legas.  Bata-garin sun fito zanga-zanga ne don nuna fushinsu a kan kashe musu mutane biyu da jami’an ‘yan sanda suka yi. ENDSARS: An kona bankuna uku a Legas Babu wanda aka kashe a harbin Lekki —Gwamnan Legas Babu […]

Bata-gari sun kona motoci a tashar Oyinbo

Wasu gungun bata-gari sun cinna wa motoci kusan 30 wuta a tashar mota ta Oyinbo a Jihar Legas. 

Bata-garin sun fito zanga-zanga ne don nuna fushinsu a kan kashe musu mutane biyu da jami’an ‘yan sanda suka yi.

Hakan ya sa suka shiga barnata kayan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Rahotannin sun bayyana cewa fusatattun mutanen sun huce haushinsu ne a kan dukkan wanda suka ci karo da shi, matukar baya cikinsu.

Hakan ce ta jawo suka afka wa tashar motoci ta Oyinbo, inda suka kona motoci tare da farfasa gilasan wasu daga ciki.

Zanga-zangar #EndSARS ta sauya salo a Jihar Legas, inda mutanen da babu ruwansu suka rasa rayukansu, aka kuma jikkata wasu bayan da hargitsi ya ritsa da su.