Wasu birai sun nuna kwarewa wajen salon daukar hoton ‘selfie’
Wasu birai biyu sun nuna abin al’ajabi a yayin da aka zo daukarsu hoto sai suka yi irin abin nan da matasa ke yi na karkacewa gefe guda domin burgewa. Wannan ya faru ne lokacin da mai kula da su ya dauki hoto tare da su, saboda sabo da suka yi da mutane ya sa […]
Wasu birai biyu sun nuna abin al’ajabi a yayin da aka zo daukarsu hoto sai suka yi irin abin nan da matasa ke yi na karkacewa gefe guda domin burgewa.
Wannan ya faru ne lokacin da mai kula da su ya dauki hoto tare da su, saboda sabo da suka yi da mutane ya sa suke kwaikwayon halyayar mutanen. Biran an tsince su tun suna kanana wannan ya sa suka saba da mai kula da su har suke kwaikwayarsu.
Hoton an dauke shi ne a gidan gandun daji na Birunga da ke Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Kango ya jawo hankalin mutanen da ke amfani da shafin sada zumunta na Facebook.
Biran mutane na yi musu lakabi da Ndakazi da Ndeze kuma idan za a dauki hoton sai su tsaya a kan kafafunsu sannan su matso kusa da kyamarar daukar hoto su karkace ta yadda za su kayatar.
Mai kula da gandun dajin, ya rubuta a shafinsa na Instagram “Cewar wadannan ’yan mata ne guda biyu da suke nuna irin bajintarsu a gandun dajin shakatawa na Birunga.’’
Gandun dajin wanda yake Arewa maso Gabashin kasar Kongo ya kunshi sama da nau’o’i 20 na birai, cikinsu har da goggon biri. An yi kiyasin cewa akwai goggon biri sama da dubu daya. Sama da ma’aikata 600 ne suke aiki wajen kare gandun dajin wanda yake da murabba’in mil dubu 3.