Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji (4)
Na Khalid Bin SalamahFassarar Imam DSP Ahmad Adam Kutubi Tambaya: Saboda me duga-dugan Manzo (SAW) masu alfarma ba su taba kasar Arafa ba a Hajjin Ban-Kwana?Yana daga abin da aka sani yanke cewa Manzon Allah (SAW) abin so ne a wajen kowane mumini, haka nan gurabansa (abubuwan da ya bari kamar tufafi da abubuwan da […]
Na Khalid Bin Salamah
Fassarar Imam DSP Ahmad Adam Kutubi
Tambaya: Saboda me duga-dugan Manzo (SAW) masu alfarma ba su taba kasar Arafa ba a Hajjin Ban-
Kwana?
Yana daga abin da aka sani yanke cewa Manzon Allah (SAW) abin so ne a wajen kowane mumini, haka nan gurabansa (abubuwan da ya bari kamar tufafi da abubuwan da ya yi amfani da su) su ma ababen so ne, kuma ma da yawa mutane na nemansu, kuma hakika Allah Ya yi nufin kada wani gurbin wani abin so ya kasance a Arafa ban da Shi Maddaukakin Sarki, koda kuwa guraben Manzon Allah (SAW) ne. Watakila hikamar haka- Allah Shi ne Mafi sani – ita ce da a ce Manzon Allah (SAW) yana da wani gurbi a Arafa da wadansu mutane sun rataya da ita su shagala da ita ga barin soyayyar Allah Ta’ala a wannan wuni mai girma, kuma da zukata sun karkata zuwa ga soyayyar bawa ga barin soyayyar Ubangiji Mai tsarki. Yaya haka kuwa ba zai auku ba, alhali mu mun sani cewa mafi yawan dalilin da mutane suka bata ta hanyarsa
shi ne wuce gona da iri cikin soyayyar salihan bayi da gurabensu.
Ashe shirka ta farko a bayan kasa a zamanin Annabi Nuhu (AS) ba ta kasance ta dalilin zurfafawa ba ne-cikin soyayyar salihai da gurabensu? Shin Nasara (Kiristoci) ba sun bata ba ne da shisshigi cikin soyayyar Annabi Isa (AS)? Hakan Rafidawa ba sun bata ba ne ta hanyar wuce gona da iri cikin soyayyar Aliyu da Husain (Allah Ya yarda da su)? Kuma wadansu daga cikin Sufaye sun bata ne saboda zurfafawarsu cikin soyayyar Jilani da waninsa. Sun so su irin son da ya yi kafada-da-kafada da sonsu ga Allah Mabuwayi, Madaukaki, sai suka halaka a cikin haka.
Ta haka ne aka nufi alhazai a filin Arafa kada kowane tasiri na wani abin so ya kasance a gabansu da zukata za su shagala da shi face Allah Shi kadai Mai tsarki da daukaka. Kuma an ma iya jarrabar mutum cikin soyayyarsa ga Ubangijinsa, ta hanyar bijiro masa da wani abin son wanda bukatuwarsa zuwa gare shi take tsananta, sai dai Allah zai hana shi wannan abin kuma ya haramta masa shi don Ya jarraba shi kuma Ya gwada shi, -Shin Allah ka fi so ko wannan abin son- kamar yadda ya faru ga sahabbai (Allah Ya kara yarda a gare su), yayin da suka yi harama da aikin Hajji a lokacin yunwa da talauci, suna kuwa shiga cikin Ihrami sai Allah Ya aiko da abin farauta abi kauna ya kusanto su ba yadda ya saba ba, (wato ya gudu in ya ga mutane), sai ya zama ga shi dab da su kamar sa kama da hannu ko su soke da masunsu, don dai Allah Ya jarraba su Ya gwada su, kamar yadda Allah Ta’ala Ya ce: “Ya ku wadanda suka yi imani! Lallai Allah zai jarrabe ku da wani abu daga abin farauta, hannuwanku da masunku suna samunsa, domin Allah Ya bayyana wanda yake tsoronSa a fake, wanda kuwa ya ketare iyaka bayan wannan, to azaba mai radadi tz tabbata a gare shi.” (AI-Ma’idah:94).
Lallai tabbatarwar sahabbai (Allah Ya yarda da su) ga kadaita soyayya ya girmama, yayin da suka bar wannan farautar saboda bauta ga Allah Mai tsarki, duk da tsananin bukatuwarsu zuwa gare shi, ba tare kuwa da wani mai sa musu ido ba, ko mai bibiyarsu ba face Allah Mai buwaya da daukaka.
Jarrabawar kan tsananta cikin soyayyar a lokacin dawafi da jifar jamrori, bayan da Alhaji ya jingine ababen so wadanda su halalne gare shi tun asali, kamar mata da turare da farauta, sai jarrabawa ta zo cikin abubuwan da dama an haramta su tun asaii, wato shi ne jarrabar maza da mata da jarrabar mata da maza wadanda ba muharraman juna ba ne.
To duk da cewa zai yiwu jamrorin su kasance wasunsu na mata ne, wasu kuma na maza ne, ko dawafi da jifar jamrorin su zama wuni daya ga maza, wani wunin kuma na mata; ko a yafe wa mata dawafin da jifar saboda matsatsi da maza, ko jifar ta zama ga wani dutse ne babba, maimakon karama, don kada mutane su matsu, sai dai shari’a – Allah kuwa Shi ne Mafi sani- ta zo da hukunce-hukuncen dawafi da jifa a bisa yanayinsu da aka sani, watakila ma wannan matsatsi ya jawo kusantar mata daga maza a wani wuri mai kunci, don jarrabawa da gwadawa… shin Allah Shi ne Mafi soyuwa zuwa gare ku ko mata?
Don haka za ka samu mumini na gaskiya wanda son Allah Ya shagattar da zuciyarsa, duk da wannan matsatsi mai tsanani, da rashin mai sa ido daga mutane, yana tsantseni yana kaffa-kaffa yana kaucewa iya iyawarsa, ba don komai ba sai don cewa Allah Shi ne Mafi soyuwa zuwa gare shi daga waninsa, musamman ma yayin da yake tuna cewa Annabi Ibrahim (AS) ba a ba shi darajar Badadintaka ba sai da aka jarrabe shi a wurin jamrorin cikin dansa Annabi Isma’ila (AS), bayan kuma an jarrabe shi darashin haihuwa na tsawon shekaru masu yawa, sannan aka jarrabe shi bayan ya samu dan, aka sanya shi ya bar sni tare da mahaifiyarsa a wani kwari mara shuka, kuma ya tafi Sham, sannan aka umarce shi ya komo zuwa gare su. Sannan bayan farin cikinsa da gamuwa da dansa tilo aka umarce shi ya yanka shi, sai ya zo wurin wadannan jamrorin don zartar da umarnin, sai Shaidan ya zo masa har sau uku yana sanya masa wasi-wasi domin ya hana shi zartar da umarnin Ubangijinsa. A lokacin Shaidan bai samu komai
daga Annabi Ibrahim ba face martani yankakke wato jifa da dutse da maimaita cewa Allah Shi ne Mafi girma daga kowane mai girma. Allah ne Mafi girma! Allah ne Mafi girma!!
Tambaya: Saboda me Makka ta kasance a wani kwari wanda ba ma’abocin shuka ba?
Da dai a ce Hajji ya kasance ana zuwa wuri ma’abocin shuka da korran ganye da koramu domin yin sa ne, to da watakila niyyoyi sun cudanya a wajen wasu alhazai kuma -Allah ne Mafi sani- shin sun nufi ibada ce tsarkakakkiya da aikin Hajjin? Ko sun nufi koramu ne da korayen ganyayyki da kyawun ababen halitta (na itatuwa da duwatsu)?
Kuma akwai wata hikima daban -Allah ne Mafi sani… da a ce Makka ta tara falaloli biyu:
Ta farko: Cewa zukata suna daukuwa zuwa gare ta.
Ta biyu: Ta kasance ma’abociyar koraye da koramu, watakila da mutane sun taru a cikinta sun yi yawa, kuma da ba su bar wa wadansu mutane damar zuwa gare ta ba. Sai dai yana daga rahamar Allah kasancewarta zukata ne kawai suke daukuwa zuwa gare ta, sannan su zo su samu wani kwari ne ba ma’abocin shuka ba, wanda bai tsaraita daga wahala ba, su aiwatar da ibadunsu, sannan su tafi su ba da sarari ga wadansunsu.
A karshen zance game da tabbatar da tauhidin soyayya muna cewa: “Hakika Allah Mai tsarki da daukaka ba Ya lamunta soyayyarsa a cikin zuciyar bawa da son wani abin so kwata-kwata, ballantana soyayyar abin halitta ta zarta sonsaSa Mai tsarki. Wannan kuwa shi ne tauhidin soyayya. Don haka idan ka riski wannan manufa mai girma, to addu’arka ta yawaita cikin Hajji a kan cewa wannan manufa ta tabbata gare ka, tare da abubuwan da suke damfare da ita, da gusar da abubuwan da ka iya kawo mata tarnaki. To idan an amsa maka wannan addu’a, to barkanka.
Imam DSP Ahmad Adam Kutubi, 08036095723