Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji (5)
Na Khalid Bin SalamahFassarar Imam DSP Ahmad Adam Kutubi Manufa ta Biyu: Tabbatar da girman Allah Madukaki:Allah Ta’ala Ya ce: “Wancan ke nan. Kuma wanda ya girmama ibadojin Allah, to lallai ne (ita girmamawar) tana daga ayyukan zukata na ibada.” (AI-Hajji). Su kuwa kalmomin sha’a’ir da mash’ar; su ne duk wani abu da ya sanya […]
Na Khalid Bin Salamah
Fassarar Imam DSP Ahmad Adam Kutubi
Manufa ta Biyu: Tabbatar da girman Allah Madukaki:
Allah Ta’ala Ya ce: “Wancan ke nan. Kuma wanda ya girmama ibadojin Allah, to lallai ne (ita girmamawar) tana daga ayyukan zukata na ibada.” (AI-Hajji). Su kuwa kalmomin sha’a’ir da mash’ar; su ne duk wani abu da ya sanya jin girman Allah da wadatuwarSa a cikin zuciya, da kaskancin abin halitta da bukatuwarsa, wannan kuwa yana bayyana karara a kasar Muzdalifa. To tsarkin ya tabbata ga Wanda wuyaye suka risina ga girmanSa. Hakika duk wanda ya kwatanta tsakanin yanayin alhazai a Mina da Arfa ta wani bangaren da kuma- yanayinsu a Muzdalifa a daya gefen, zai lura da bambancin mai zurfi a tsakanjn yanaye-yanayen guda biyu, wadanda su ne cewa alhazai a kasar Mina da Arfa bambancin matsayinsu yana bayyana karara ta bangaren wadata da talauci, cikin irin hemominsu da abincinsu da abin hawansu.
A dai Mina da Arfa za ka samu talakan da yakan zauna da yunwa a gefen hanya, kuma za ka samu mawadacin da yakan ja hankali da hemarsa da yanayin tufarsa da kuma kayansa.
Kai ta kai wani lokacin ma alhazai na iya shagaltuwa a nan da yanayin shiga ta ababen halitta ga barin wadatar Mahalicci Mai tsarki, kuma su shagala da girman ababen haiitta ga barin girman Mahalicci wanda tsarki ya tabbata gare Shi, har ma wadansu gafalallun zukata kan kusa su manta wane ne Mai girman ma a lokacin!
To, a nan -Allah ne Masani- sai aka shar’anta hukunce-hukuncen Muzdalifa, don su gusar da duk wasu bambancen-bambancen wadata da girma tsakanin alhazai, don kada wata manuniya ta girma da wadata ta yi saura a Muzdalifa, sai fa girman Allah Wanda tsarki ya tabbata a gare Shi da wadatarSa Shi kadai.
Allah Ta’ala Ya ce: “Ya ku mutane! Ku ne mabukata zuwa Allah, kuma Allah Shi ne Mawadaci Abin godewa.” (Fatir).
Hakika da za ka yi duba ta natsuwa game da hukunce-hukuncen Muzdalifa, da ka same su an shar’anta su ne ta hanyar da za su kange tsakanin alhazai da abubuwan da suke nuna wadatarsu da girmansu. Don haka tsayuwa a cikinta da dare ne kawai, saboda haka ma ba sa bukatuwa zuwa hemomin da suke fifita juna a cikin kamanninta, kuma tsawon lokacin tsayuwar wasu awanni ne da suke tsaraita a cikinsu daga tufafin ado, don haka ba sa bukatuwa zuwa kayansu da jakunkunansu wadanda suke bayyana wadatar wasunsu da girmansu, wannan kuwa shi ya janyo suke barci dukkansu a Muzdalifa irin barcin talakawa, a kan dandalin kasa, watakila ma su ci abinci irin na talakawa.
Kai za ma ka gan su sun yi sahu-sahu a cikin (ayyuka zagaye a gaban ban-daki, talaka da mawadaci da baki da fari, suna masu cakuduwa da kamanni na bukatuwa da rauni, nesa da alama ta wadata, saboda kowa ya fahimta a yayin da suke kallon wadannan abubuwan gani a Muzdalifa…cewa babu wani mai girma sakakke mara iyaka sai Allan Shi kadai Mai tsarki!
Manufa ta uku: Tabbatar da kwadayi zua ga Allah Madaukak:
Allah Ta’ala Ya ce: “Wadancan wadanda suke kira suna neman tafarki ne zuwa Ubangijinsu wane ne mafi kusanci, kuma suna kwadayin rahamarSa kuma suna tsoron azabarSa, hakika azabar Ubangijinka ta kasance abar ki ce.” (lsra’i).
Hakika hanyar da aka shar’anta ayyukan Hajji sun janyo cakuduwa, ko kusanta a cikin masaukai musamman ma a hemomi, tsakanin nau’in mutane na masu kwadayi da wadanda ake yin kwadayi a wajensu daga halitta da tsakanin mawadata da talakawa da tsakanin masu alfarma da masu rauni, da tsakanin mai umarni da wanda ake umarta, ta hanyar da zai yi wuya a samu kwatan-kwacinta a rayuwar yau da kullum, wannan kuwa yana bayyana fiye da kowane lokaci a Arfa da Muzdalifa.
Sai dai mai duban tsanaki cikin halin alhazai a wadannan wuraren ibada guda biyu zai samu cewa kowa da kowa ya shagala ga barin yin kwadayi wajen ababen haiitta, kuma dukkansu sun fuskanci Wanda taskokinSa ba sa karewa, kuma ni’imominSa ba sa kirguwa, kuma wani abu ba ya gagararSa a cikin kasa ko sama. Suna masu daga tafuka da kaskantar da kai cikin kamanni iri daya da hali iri daya, mawadatansu da talakawansu, likita da mara iafiya. Suna masu bayyana kaskantar da kai gare Shi, da bukatuwa da nuna karaya a gaba gare Shi, don kowa da kowa ya san cewa babu wani abin yin fata zuwa gare shi face Allah Shi kadai, Mai tsarki, wannan kuwa yana daga tsarkake tauhidin fata ga Ubangijin talikai.
Manufa ta hudu: Tabbatar da tsoron daga Allah Mai tsarki:
Allah Ta’ala Ya ce: “Da wadanda suke ba da abin da saka bayar, alhali zukatansu suna tsorace, saboda kasancewarsu masu komawa ne ga Ubangijinsu. Wadancan suna yin gaggawa zuwa ga ayyukan alheri, alhali su masu rigaye ne zuwa gare su (su ayyukan alherin)” (Al-Muminuna).
Hakika duk wanda ya yi tsokaci game da nassoshin, kuma ya yi dubi duk abin da ke faruwa a zahiri, ya kuma bi diddigin tarihi, zai samu cewa akwai alaka mai karfi a tsakanin ibadar Hajji da kuma siffar tsoron (Allah), alakar da ta kusa ta kai matsayin damfarewa. Wannan kuwa na bayyana ne ta hanyar la’akari da: 1- Ayoyin Alkur’ani. 2. Sunnah. 3- Abin da ke aukuwa yau da kullum.
Da Farko: Alkur’ani: Ya dan uwana Alhaji! Ka karanta Suratul Hajji, sannan- ka yi la’akari, za ka samu cewa ita sura ce da aka bude ta da wani hoto na abin tsoro mai razanarwa, kai mafi tsananin nau’o’in tsoro da dan Adam zai taba ratsawa, kamar yadda Allah Madaukakin Sarki Ya ce: “Ya ku mutane! Ku ji tsoron Ubangijinku, hakika girgizar kasa ta tsayuwar Alkiyama aba ce mai girma. A ranar da kuke ganinta kowace mai shayarwa tana shagala daga barin abin da ta shayar, kuma dukan mai ciki za ta haife cikin nata, kuma kana ganin mutane suna masu maye, alhali kuwa su ba masu maye ba ne, sai dai azabar Allah ce mai tsanani.” (Al-Hajj). To wannan fa ita ce mabudin surar da za ta yi magana a kan aikin Hajji.
To ya jama’a ko dai akwai wata alaka ce tsakanin Hajji da tsoro?
Sannan ka yi la’akari a cikin Sunnar Annabi (SAW): Za ka samu cewa Annabi (SAW) ya ambaci Hajji da jihadi, cikin fadinsa (SAW) ga mata: “An wajabta muku wani jihadi da babu fada a cikinsa, Hajji da Umara.” Ahmad da Ibn Majah ne suka ruwaito shi kuma isnadinsa ingantacce ne.
Shin shi jihadi ba abin tsoro ba ne?
Sannan ka yi la’akari da yadda tsoro ya damfara da kokarin Manzon Allah (SAW) da sahabbansa masu girma wajen isa kasar harami a Shekarar Hudaibiyya. Domin hakika kuraishawa sun tare Musulmi, sun hana su yin Umara, kuma mutane suka yi kira da a yi yaki, kuma muminai suka yi mubaya’a a kan yaki a karkashin bishiya, sannan sulhu ya auku a kan cewa za su dawo su yi Umara shekara mai zuwa, kuma Musulmi suka shardanta yin Umarar tare da takubbansu don tsoron yaudarar kuraishawa, sai Umarar ta kasance damfare da tsoro.
Imam DSP Ahmad Adam Kutubi
08036095723