Wasu daga cikin Mu’ujizojin Alkur’ani (2)

Halittar Duniya: Akwai bayanai a kan yanayin duniya da dangantakar sammai da kasa da dukkan abin da ya shafi halittar duniya.“Kuma shin wadanda suka kafirta ba sa ganin cewa lallai sammai da kasa sun kasance dunkule (dinke) sai Muka bude su, kuma Muka sanya dukan komai mai rai daga ruwa? Shin ba za su yi […]

Wasu daga cikin Mu’ujizojin Alkur’ani (2)
Wasu daga cikin Mu’ujizojin Alkur’ani (2)

Halittar Duniya: Akwai bayanai a kan yanayin duniya da dangantakar sammai da kasa da dukkan abin da ya shafi halittar duniya.
“Kuma shin wadanda suka kafirta ba sa ganin cewa lallai sammai da kasa sun kasance dunkule (dinke) sai Muka bude su, kuma Muka sanya dukan komai mai rai daga ruwa? Shin ba za su yi imani ba? Kuma Mun sanya tabbatattun duwatsu a cikin kasa domin kada ta karkata da su, kuma Mun sanya ranguna, hanyoyi a cikinsu (duwatsun) domin su shiryu (yayin tafiye-tafiye). Kuma Mun sanya sama rufi tsararre, alhali kuwa su daga ayoyinta masu bijirewa ne. Kuma Shi ne (Allah) Wanda Ya halitta dare da yini da rana da wata, dukkansu a cikin wani sarari (falaki) suke iyo.” (Suratul Anbiya: 30 -33).
A wata ayar Allah Ya ce: “Lallai ne Ubangijinku Allah ne Wanda Ya halitta sammai da kasa a cikin yini shida, sannan Ya daidaita a kan Al’arshi, Yana sanya dare ya rufe yini, yana bin sa da gaggawa, kuma rana da wata da taurari suna gudana da umarnin Allah. To Shi ne da halitta kuma da umarni …” (Suratul A’araf: 54).
Bayani a kan doron kasa:
Duwatsu, koguna, tekuna da rabe-raben duniyoyi. Allah (SWT) Yana cewa:
“Ashe ba Mu sanya kasa shimfida ba. Kuma duwatsu turaku (domin rike kasa). Kuma Muka sanya barcinku hutawa, kuma Muka sanya dare (ya zama) sutura. Kuma Muka sanya yini (ya zama) lokacin neman abinci. Kuma Muka gina a samanku sammai bakwai masu karfi. Kuma Muka sanya fitila mai tsananin haske (rana). Kuma Muka saukar daga cikin giza-gizai, ruwa mai yawan zuba.”
6. Akwai bayanai a kan kadawar iska. Haduwar gajimare, zubowar ruwan sama, tsawa da walkiya: A cikin Suratur Ra’ad, Allah (SWT) Ya yi bayani a kan walkiya da tsawa kamar haka:
“Shi ne wanda Yake nuna muku walkiya domin tsoro da tsammani, kuma Ya kaga halittar giza-gizai masu nauyi. Kuma tsawa tana tasbihi game da gode Masa, haka ma mala’iku domin tsoronSa, kuma Yana aiko tsawarwaki, Ya samu wanda Yake so da su, alhali kuwa su suna jayayya (a cikin al’amarin), Allah Shi ne Mai tsananin karfi.” (13:12-13).
“Kuma akwai daga ayoyinSa Ya nuna muku walkiya a kan tsoro da tsammani, kuma Ya saukar da ruwa daga sama sannan Ya rayar da kasa a bayan mutuwarta. Lallai a cikin wannan akwai ayoyi ga mutane masu hankaltuwa.”
7. Cikinsa akwai bayani a kan tsarin ma’adinai da fahimtar abubuwan da ke karkashin kasa:
8.  Allah Ya yi bayani cikin Alkur’ani a kan fannin ’ya’yan halitta da abubuwan da suke kewaye da su da kuma halayen halittu.
9. Ilimin hade-haden magunguna duk akwai a cikin kur’ani.
10. Allah a cikin Alkur’ani Ya yi bayani a kan ilimin shari’a, wanda ya kunshi:
(i)  Umarni da bin dokokin Allah da kiyaye hakkokin ’ya’ya (masu ’yanci) da bayi.
(ii)  Warware matsalolin da ke faruwa a tsakanin al’umma, irin su mutuwar aure, hakkokin iyaye da ’ya’yansu, gado, kasuwanci, aikin kwadago, bashi, makwabtaka, da warware rikice-rikicen aure.
Misali: A kan dangantakar auratayya, ya zo kamar haka:
“Kuma wadanda suke mutuwa daga cikinku, suna barin matan aure, matan sai su yi jinkiri da kansu har wata hudu da kwana goma. To idan sun isa ajalin takabarsu, to babu laifi a gare ku game da abin da suka aikata da kawunansu bisa kyautatawa (wato wajen sake wani auren). Kuma Allah game da abin da kuke aikatawa Masani ne.” (Suratul Bakara 234).
Haka Allah (SWT) Ya ce:  “Kuma mata wadanda aka saki aurensu, suna jinkiri ga kansu tsarki uku. Kuma ba ya halatta a gare su su boye abin da Allah Ya halitta a cikin mahaifarsu idan sun kasance suna yin imani da Allah da Ranar Lahira. Kuma mazan aurensu su ne mafiya hakki ga mayar da su idan sun yi nufin gyarawa…” (2:228).
(iii) Hukuncin haramta neman kudi daga abubuwan da aka hana kamar su riba, kwace, algush, zamba, rashawa, cin amana, karuwanci da sauransu, duk akwai a cikin Alkur’ani.
(ib) Hukuncin abinci da abin sha wadanda aka halatta da wadanda aka haramta.
11. Adana kayan tarihi domin su zama darasi ga al’ummar Musulmi. Misali:
(a) dakin Ka’aba: Allah Mai girma Wanda Ya ba da labarin Ka’aba a wurare da dama a cikin Alkur’ani kamar haka:
“Kuma a lokacin da muka sanya dakin (Ka’aba) ya zama mafuskanta ga mutane, da aminci kuma ku riki wurin Sallah daga Makama Ibrahim, kuma muka yi alkawari zuwa ga Ibrahim da Isma’ila da cewa: Ku tsarkake dakiNa domin masu dawafi da masu lazimta da masu ruku’i da masu sujada.” (Suratul Bakara:125).
(b)  Katangar Zulkarnaini: Bayanin wannan bawan Allah tare da katangar da ya gina a cikin mulkinsa ya zo ne a cikin Suratul Kahfi inda aya ke cewa:
 “Kuma suna tambayarka game Zulkarnaini, ka ce zan karanta muku ambato game da shi, lallai ne Mun ba shi mulki a cikin kasa, kuma Muka ba shi daga kowane abu hanya (zuwa ga muradinsa). Sai ya bi hanya har zuwa lokacin da ya isa ga mafadar rana. Kuma ya same ta tana bacewa a wani ruwa mai bakar laka, kuma ya samu wadansu mutane a wurinta, har a lokacin da ya isa a tsakanin duwatsu biyu, ya samu wadansu mutane daga gabaninsu, ba su yi kusa su fahimci magana ba, suka ce, ‘Ya Zulkarnaini! Lallai Yajuju da Majuju suna barna a bayan kasa, to, ko za mu biya ka haraji saboda ka sanya wata katanga a tsakaninmu da su?’” (Suratul Khaf aya ta 83-86, 93-94).
(c) As’habul Kahfi: Bayanin wadannan matasa muminai Ma’abuta Kogo ya zo ne a cikin Suratul Kahfi:
“Ko kuwa ka yi zaton cewa Ma’abuta Kogo da rakimi (allon da aka rubuta sunayensu) sun kasance abin mamaki daga ayoyinMu (Allah). A lokacin da samarin suka tattaka zuwa ga kogon, sai suka ce, ‘Ya Ubangijinmu, Ka ba mu wata rahama daga gare Ka, kuma Ka saukake mana shiriya daga al’amarinmu.” (18:9-10).
10. Cikin Alkur’ani akwai bayani a kan zamantakewar al’umma cikin sha’anin mulki da tsaron kasa da duk sauran al’amuran rayuwa.
11. Alkur’ani ya bayyana sirrin wadansu abubuwa da ke nuna cikar hikimar Allah da makamantansu. Alal misali, Alkur’ni ya ba da labarin “kudan Zuma” a cikin Suratun Nahli kamar haka:
Mu tsakuro wannan rubutu ne daga littafin BAYANI A KAN ILIMIN ALkUR’ANI na

Malam Aliyu Muhammad Sa’idu Gamawa
karamar Hukumar Gamawa, Jihar Bauchi
08035829071