Wasu daga cikin zawarawan da aka daura wa aure a Kaduna

kungiyar Al-Shabbab ta mayakan sa-kai a kasar Somaliya ta dauki alhakin kashe wakilan Majalisar Dokokin kasar biyu a kasa da kwana da daya.Al-Shabbab ta ce ta harbe Abdilaziz Isak Mursal, wanda ya cika ranar Talata, bayan wani kwanton bauna da ’yan bindigarta suka yi masa a gundumar Dharkaynley da ke birnin Mugadishu.Hukumomin kasar sun ce […]

Wasu daga cikin zawarawan da aka daura wa aure a Kaduna
Wasu daga cikin zawarawan da aka daura wa aure a Kaduna

kungiyar Al-Shabbab ta mayakan sa-kai a kasar Somaliya ta dauki alhakin kashe wakilan Majalisar Dokokin kasar biyu a kasa da kwana da daya.
Al-Shabbab ta ce ta harbe Abdilaziz Isak Mursal, wanda ya cika ranar Talata, bayan wani kwanton bauna da ’yan bindigarta suka yi masa a gundumar Dharkaynley da ke birnin Mugadishu.
Hukumomin kasar sun ce an yi ta harbin dan majalisar inda nan take ya mutu.
A ranar Litinin wani bam da aka boye a cikin wata mota, ya kashe wani dan majalisar dokokin kasar mai suna Isak Mohammed Ibrahim a birnin Mogadishu.
An kashe Isak Mohammed Ibrahim ne, lokacin da bam din da aka boye cikin motarsa ya tashi da shi, kuma bam din ya raunata wan dan majalisar mai suna Mohammed Abdi.
Ofishin Firayi Ministan kasar ya tabbatar da wannan labari.
A ’yan shekarun nan kungiyar Al-Shabbab ta yi asarar yawancin yankunan da ta mamaye, a Somaliya bayan da sojojin kasashen Afirka da na gwamnatin Somaliya suka kwace su. To amma duk da haka mayakan sa-kan, sun ci gaba da kai hare-hare jefi-jefi.
A watan Fabrairu ma, mutum 17 mahara suka kashe, lokacin da mayakan Al-Shabbab suka kutsa fadar Shugaban kasar Somaliya, Shugaba Hassan Sheikh Mohammed, sai dai Shugaban ya tsallake harin ba tare da jin rauni ba.
Jakadan Majalisar dinkin Duniya na musamman a Soma-liya, Nicholas Kay, ya ce hare- haren suna nuna cewa, duk da kungiyar ta yi asarar yankunan da ta mamaye cikin ’yan shekarun da suka wuce, har yanzu tana ci gaba da zama barazana ga kasar.