Wasu ginshikai shida da ke karfafa tarbiyya a rayuwa
Tare da sallama, Assalamu alaikum gare ku ma’abuta shafin Sinadarin Rayuwa. Kafin mu fara nazartar wadannan abubuwa guda shida, bari mu sake nazarin cewa, mafi yawa daga matsalolin da muke fuskanta a rayuwa, suna faruwa ne a sanadiyyar rashin tarbiyya ko halayya mai kyau, domin kuwa za ka ga muna da tsare-tsaren al’amura masu muhimmanci […]
Tare da sallama, Assalamu alaikum gare ku ma’abuta shafin Sinadarin Rayuwa. Kafin mu fara nazartar wadannan abubuwa guda shida, bari mu sake nazarin cewa, mafi yawa daga matsalolin da muke fuskanta a rayuwa, suna faruwa ne a sanadiyyar rashin tarbiyya ko halayya mai kyau, domin kuwa za ka ga muna da tsare-tsaren al’amura masu muhimmanci da muke son cin mawa amma rashin tarbiyya mai kyau kan zama haddasau wajen dakile mana samuwarsu.
Mu duba duk wani al’amari mai muhimmanci a rayuwarmu, za mu ga cewa ana bukatar tarbiyya mai kyau kafin a ci nasara a kansa. Mu duba zaman aure, watau tarayya tsakanin ma’aurata, da abin da ya shafi rainon ’ya’ya da sauran iyali, lallai kam ana bukatar kyakkyawar tarbiyya kafin a cin ma nasara. Idan kuma muka duba harkokin da suka shafi sana’a, aiki ko kuma siyasa da sha’anin mulki, babu yadda za a yi a samu nasararsu ba tare da kyakkyawar tarbiyya ba. Lallai kam tarbiyya wata ginshiki ce ta karfafa da inganta rayuwa.
Abu na farko da ya kamata ka fuskanta domin samun tarbiyya mai kyau, wacce za ka yi amfani da ita wajen cin ma burikanka na rayuwa, shi ne ka yafe wa kanka. Bayan ka yafe wa kanka, sai kuma ka fuskanci al’amuranka gaba gadi.
Watakila mutum ya ce me ake nufi da yafe wa kai? Shin kana yi wa kanka laifi ne, da har za a ce ka yafe wa kanka? kwarai kuwa, mutum kan yi wa kansa laifi, watau ya aikata wani abu da zai dame shi, ya gallabi rayuwarsa. Idan haka ta faru, sai ka dauki kwakkwaran matakin yafe wa kanka, watau ka mance da wannan al’amari gaba daya, sannan ka saita tunaninka ya daidaita da tarbiyyar abin da kake nema. Idan ka samu wannan tarbiyya, da ita za ka nemi biyan bukatar nan da ke gabanka. Idan ka yi haka, ka ga ka samu nasara ke nan.
Abu na biyu da za ka tunkara domin karfafa tarbiyyarka shi ne, ka sanya wa ranka cewa, ita tarbiyyar nan fa ba kaya ba ne da za ka dauka ko ka ajiye, domin kuwa tarbiyya wani abu ne da za ka sanya a zuciyarka, ka daidaita shi tare da tunaninka, yadda zuciyarka za ta iya daukar jure duk wani radadi da rashin sukunin bin ra’ayin. Ita tarbiyya, wata abu ce da ke sanya wa mutum kaimi da ingiza shi domin yin wani abu. Misali, kana son ka samu ilimi, domin amsa wannan bukata, sai ka gina tarbiyyar samun haka da tunaninka da zuciyarka. Wannan tarbiyya ce za ta ingiza ka domin kama hanyar zuwa makaranta, sannan ka kintsa tunaninka yadda za ka bi ka’idoji da hanyoyin da aka shimfida a makarantar, wanda haka zai sanya ka samu ilimi. Haka al’amarin yake ga sauran dukkan al’amuranka na yau da kullum, musamman abin da ya shafi neman dukiya ta hanyar aikin yi ko sana’a da sauransu. Ta hanyar tarbiyyantar da kanka bisa bin ka’idoji da hanyoyin da suka dace ne zai sanya ka samu nasarar rayuwa.
Abu na uku da ya kamata ka yi domin cin nasarar samun tarbiyyar da ta dace da inganta rayuwarka shi ne, har kullum ka kasance mai tsara akidojinka da bukatunka. Idan ma ka ga kamar za ka iya barin hanyar wannan tunani naka, sai ka samu takarda, ka rubuta bukatar taka, sannan ka rubuta dalilinka na neman bukatar. Idan ka yi haka, sai ka tanadar da tarbiyyar bin kadin wannan bukata, ta hanyar jure wa kalubalen da ke fuskantar hanyoyin cin ma wannan bukata taka. Idan ma har ka kauce wa hanya, sai ka dawo daga baya, ka tunano dalilinka na son wannan biyan bukata.
Ta hanyar haka ne za ka zama mai jure wa duk wata wahala da kan fuskanci hanyar cin ma burin naka, domin dai har kullum za ka gane cewa, akwai dalilin da ya sanya za ka aikata kaza, ko kuma dalilin neman kaza, da sauransu. Ke nan, tarbiyyar juriya da jajircewa, abar bukata ce ga dan Adam a kowane lokaci. Mafi yawan duk wani ci gaba da aka samu a duniya, ya samu ne a sakamakon tarbiyyar juriya da hakuri da aiki tukuru.
A nan za mu tsaya, sai mako mai zuwa idan Allah Ya kai mu za mu ci gaba da nazarin sauran abubuwa uku da za mu duba domin bunkasa da karfafa tarbiyyarmu. Har kullum dai ya kamata mu gane cewa, kowane al’amari na da sanadi kuma yana da ka’idoji da hanyoyin da ake bi domin samunsa. Idan kuwa haka ne, to komai na da turba da tarbiyyar da ya kamata a tanada domin cin ma burin nan.
Za mu ci gaba