Wasu ginshikai shida da ke karfafa tarbiyya a rayuwa (2)

Assalamu alaikum, ya ku ma’abuta karanta wannan fili na Sinadarin Rayuwa. Kamar yadda muka faro muku bayani bisa wannan maudu’i a makon da ya gabata, watau inda muka zakulo wasu muhimman turaku guda shida da muka ce suna karfafa tarbiyya a rayuwa, a wannan makon za mu karkare bayani. A makon na jiya, mun nazarci […]

Wasu ginshikai shida da ke karfafa tarbiyya a rayuwa (2)
Wasu ginshikai shida da ke karfafa tarbiyya a rayuwa (2)

Assalamu alaikum, ya ku ma’abuta karanta wannan fili na Sinadarin Rayuwa. Kamar yadda muka faro muku bayani bisa wannan maudu’i a makon da ya gabata, watau inda muka zakulo wasu muhimman turaku guda shida da muka ce suna karfafa tarbiyya a rayuwa, a wannan makon za mu karkare bayani. A makon na jiya, mun nazarci turaku uku ne kadai a cikin shidan, don haka bari mu ci gaba da turke na hudu.
Abu na hudu da za ka yi domin karfafa tarbiyya shi ne, duk abin da za ka aikata ko za ka tunkari aikatawa, to ka yi kokarin mayar da shi abu mai sauki. Tun farko, komai wahalarsa, ka yi kokarin kintsa zuciyarka, ka yi magana da kanka cewa, wannan abin mai sauki ne, kuma za ka iya aikata shi. Idan ka sanya wa zuciyarka tunanin haka, babu shakka za ka jajirce, ka tunkare shi gaba-gadi, da nufin cewa akwai sauki tare da shi. Har kullum abin da za mu lura da shi shi ne, muddin dai mutum ya taba aikata irin wannan aiki, to kuwa kai ma za ka iya yin irinsa, ko ma ka wuce da na baya. Ba tunanin sauki kadai za ka yi wa al’amari ba, sai kuma ka dauki hanyar da za ka kara samun sauki wajen fuskantar al’amarin. Misali, ka fara atisaye, ko in ce gwaji na dan takaitaccen lokaci, kafin ka shiga aikin gadan-gadan. Misali, kamar a ce za ka yi wanka da ruwan sanyi kuma a lokacin hunturu, me ya kamata ka yi don ka samu amincin wankan nan? Sai ka tarbiyantar da jikinka domin shirin amsar ruwan sanyi a wannan lokaci. Watau sai ka fara shafa ruwan kadan a kanka, sannu a hankali har yanayin jikinka ya aminta da shi. Bisa haka sai ka ga ka kammala wankanka lami lafiya, ba tare da kana kakkarwar sanyi ba. To, ga dukkan al’amuran rayuwa, ka kirkiri tarbiyyar da ta dace da shi, domin samun saukin aiwatarwa.
Mataki na biyar da zai taimaka maka wajen karfafa tarbiyya a rayuwa shi ne, ka fuskanci neman farin ciki wajen aiwatar da abin da ka tunkara. Babu shakka duk wani abu mai wahalar aiwatarwa, yana da cika rai, yana da isa da gimsa. Don haka, idan kana son nasara, dole ne ka samu tarbiyyar da ta kamata. Misali, a duk lokacin da za ka aiwatar da wani aikin karfi, sai ka nemi wani abu da zai sanyaya maka rai domin samar maka da farin cikin tunkarar aikin cikin fa’ida. kila a ce za ka samu wani abokin aiki mai barkwanci, wanda zai sanya ku rika tattaunawa a lokacin da kuke aikin, wanda kafin wani lokaci sai ka ga kun kammala aikin ba tare da gajiyawa ba. Ko kuma a ce ka tanadi rediyo ko rikoda da kaset wanda zai nishadantar da kai a lokacin da kake aikin nan.
Idan ma abin ba ya bukatar surutu ko sauti mai daukar hankali, misali idan kamar karatu ne za ka yi na bincike ko nazarin wata mas’ala mai tsauri, sai ka samu wuri mai yalwar ni’ima, wurin da zai ba ka natsuwa da farin cikin tunkarar nazarin nan. Misali, kamar ka samu wuri mai yalwar inuwa, inda haka zai ba ka tarbiyyar natsuwar zuciya, domin fahimtar karatun da za ka yi. Kana kuma iya tanadar wani dan abin sha marar nauyi, wanda zai kintsa maka ruhi, kamar ruwan shayi haka ko gahawa ko kuma gyada tasoyi (amaro ko motsin gemu). Irin wadannan za su ba ka annshuwa da farin ciki, za su ba ka tarbiyyar tunkarar nazarinka cikin fa’ida.
Mataki na shida a cikin wannan maudu’i, wanda kuma zai karfafa maka tarbiyya a rayuwa shi ne, ka lizimci maimaita duk abin da ba ka yi shi daidai ba. Ta hanyar maimaita wani abu sau daya ko sau biyu har zuwa uku, zai ba ka nasara gamsassa wajen cin ma burinka a rayuwa. Misali, kamar kana karatu domin binciko wata mas’ala, sai ya zamanto ba ka gane ba, sai ka dauki tarbiyyar maimaita karatun. Babu shakka idan ka maimaita sau biyu ko sau uku, da ikon Allah za ka fahimta. Ba fahimta ma kadai ba, za ka kara gano wani abin da ba ka gano ba a karatu na farko da na biyu. Lallai kam kintsa kanka da tarbiyya babban ginshiki ne wajen samun nasarar al’amura a rayuwa.
Ba karatu kadai ne za ka yi wa haka ba, za ka iya daukar matakin maimaitawa ga dukkan wani lamari na rayuwa, domin akwai abubuwa da yawa da ba za ka iya samun nasara a kansu a karo na farko ba, sai ka sake turzawa. Ko kofa ka kwankwasa sau daya, ka ji cewa ba a bude ba, bai kamata ka juya baya ka koma ba, sake kwankwasawa sau biyu zuwa uku tukunna, idan lallai ba a bude ba, to ko dai babu kowa ciki ko kuma akwai wata matsala.
A wannan maudu’i namu, wanda muka gabatar daga makon jiya zuwa na yau, yana jan hankalinmu ne wajen kyautata tarbiyya. Tarbiyya a nan na nufin kowacce, watau samar da yanayin da ya dace da kowane al’amari. Yin haka ne zai sanya mu samu nasarar rayuwa ta kowace fuska. Allah Ya sanya mu dace, amin. Sai kuma makon gobe idan Allah Ya kai mu, inda za mu sake shiga wani maudu’in.