Wasu gwamnonin PDP ba sa son Ribadu

Rahotanni sun ce wasu daga cikin gwamnonin Jam’iyyar PDP mai mulkin kasar nan sun soma yunkurin hana tsohon shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC), Malam Nuhu Ribadu zama dan takarar Gwamnan Jihar Adamawa a karkashin jam’iyyar PDP a zaben Oktoba mai zuwa.Gidan rediyon BBC Landan ya ce wasu jaridun kasar nansun […]

Wasu gwamnonin PDP ba sa son Ribadu
Wasu gwamnonin PDP ba sa son Ribadu

Rahotanni sun ce wasu daga cikin gwamnonin Jam’iyyar PDP mai mulkin kasar nan sun soma yunkurin hana tsohon shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC), Malam Nuhu Ribadu zama dan takarar Gwamnan Jihar Adamawa a karkashin jam’iyyar PDP a zaben Oktoba mai zuwa.
Gidan rediyon BBC Landan ya ce wasu jaridun kasar nansun ruwaito cewa gwamnonin PDP sun soma takun-saka a tsakaninsu da wasu mukarraban Shugaba Goodluck Jonathan wadanda ake zargin su ne ke kokarin bai wa Malam Nuhu Ribadu tikitin zama dan takarar Jam’iyyar PDP a zaben Gwamnan Jihar Adamawa mai zuwa.
Bayanai sun nuna cewa wasu daga cikin gwamnoni suna zargin cewa Malam Nuhu Ribadu na iya kasancewa sojan gona na Jam’iyyar APC, yayin da wasu daga cikinsu kuma ke kallonsa a matsayin wanda ba za a iya juya shi ba.
A makon jiya ne Malam Nuhu Ribadu ya fice daga Jami’yyar APC ya koma PDP, inda ake zargin cewa ya sauya shekar ce saboda alkawarin da aka ce PDP ta yi masa na za tsayar da shi takarar Gwamna a zaben da za a yi ranar 12 ga watan Oktoban bana.
Sai dai kuma take Malam Nuhu Ribadu ya musanta cewa ya shiga PDP ne don an yi masa alkawarin tikitin takarar Gwamnan Jihar Adamawa.
Wasu daga cikin wadanda suke kokarin samun tikitin takarar Gwamnan a karkashin Jam’iyyar PDP a zaben mai zuwa sun hada da Mukaddashin Gwamnan Jihar, Alhaji Umaru Fintiri da Janar Buba Marwa mai ritaya da Mista Markus Gundiri da kuma tsohon mashawarcin Shugaban kasa kan harkokin siyasa Alhaji Ahmed Ali Gulak.