Wasu iyaye sun garkame ’yarsu wata 30 a keji
Wata cibiyar kula da hakkin ’yan biyu (tagwaye) ta yi nasarar kubutar da wata matashiyar yarinya daga kejin da mahaifanta sukan kulle ta ciki har na tsawon wata talatin (30) saboda zargin tana da maita.Yarinyar, wadda dayar ’yan biyu ce, mai suna Blessing Olokumo da ke unguwar Ayibatari, a garin Opokuma, na karamar Hukumar Kolokuma-Opokuma […]
Wata cibiyar kula da hakkin ’yan biyu (tagwaye) ta yi nasarar kubutar da wata matashiyar yarinya daga kejin da mahaifanta sukan kulle ta ciki har na tsawon wata talatin (30) saboda zargin tana da maita.
Yarinyar, wadda dayar ’yan biyu ce, mai suna Blessing Olokumo da ke unguwar Ayibatari, a garin Opokuma, na karamar Hukumar Kolokuma-Opokuma ta Jihar Bayelsa, kamar yadda binciken cibiyar ya nuna, an samu tana da wata irin bakuwar cuta ce.
Kamar yadda mai rikon shugabancin cibiyar, Komared Tonyon Ebitei Robert, ta bayyana, wannan bakuwar cutar ce ta ja iyayen suka killace yarinyar, musamman dayake takan barke da kashi duk lokacin da ya tashi, lamarin da ke sa take bata gidan nasu.
Mahaifin yarinyar, wanda shi ma dayan ’yan biyu ne, shi ne aka ce ya hada kejin, inda aka garkame ta don a nesantar da ita daga cikin gidan. “An garkame ta kamar wata dabba, ana ba ta abinci, in ya samu, kuma ana barin ta kwanta cikin kazantarta ta amai da kashi da fitsari, lamarin da ya sa ta rame, ta susuce tana gab da mutuwa,” inji Mis Robert.
Ta ce wasu wadanda lamarin ya dame su a unguwar ta Okolobiri sun tuntubi cibiyar, wadda ta shahara wajen gangamin yaki da wulakanta tagwaye a jihar, dangane da batun yarinyar.
Yunkurin farko da cibiyar ta yi wajen ceto yarinyar ya ci tura domin mahaifinta ya gwasale su, amma yayin da suka sake komawa, sai ya yarda ya ba su ita. Daga nan aka kai ta asibiti don a kula da lafiyarta yadda ya kamata.
Yayin da wakilinmu ya nemi jin ta bakin mahaifin yarinyar, bai yi nasarar samunsa a gida ba domin an ce ya buya, amma makwaftansa sun yi tir da lamarin wanda suka bayyana shi da zalunci.